Monday 18 December 2017

Kannywood: An Garkame Rahma Sadau-Karanta Kaji

Tura Wannan Zuwa

Jarumar wasan Hausa, Rahama Sadau, ta sha
da kyar a hannun dalibai masoyanta

- Lamarin ya faru ne a jami'ar Umaru Musa dake
Katsina

- Jami'an tsaro sun yi nasarar tserar da ita ba
tare da samun lahani ba

Shahararriyar jarumar wasan Hausa, Rahama
Sadau, ta sha da kyar a hannun wasu daliban
jami'ar Umaru Musa dake jihar Katsina.

Tun farko shugabannin kungiyar daliban jami'ar
ne suka gayyaci jarumar domin karramata a
ranar Mata ta duniya.

Saidai lamarin ya kwacube
bayan isowar jarumar harabar taron, Students
Centre, dake cikin jami'ar.

Majiyar mu ta bayyana mana cewar jarumar ta
iso wurin taron a makare, kuma zamanta keda
wuya a teburin manyan baki sai dalibai suka
barke da sowa da murnar ganin jarumar.

Dalibai
da dama sun nufi jarumar domin samun damar
daukan hoto da ita, lamarin da ya kai an kasa
sarrafa dandazon matasa masoya ga jarumar
dake son yin hoton da ita.

Rahoton da muka samu ya tabbatar mana da
cewar wasu daga cikin daliban ba iya son daukan
hoto ya kai su ga wurin da jarumar ke zaune ba.

Majiyar mu ta shaida mana cewar wasu daliban
sun so afkawa jarumar ba don jami'an tsaro sun
yi gaggawar shiga tsakani ba.

Da kyar jami'an tsaron jami'ar suka yi nasarar
raba Rahama Sadau da janjamim masoyan dake
ta kokarin kusantar ta da manufa daban-daban.

Babu rahoton samun lahani ko yin wata illa ga
jarumar, an fitar da ita lafiya daga harabar
jami'ar.

Kokarin Majiyar mu na jin ta bakin Jarumar ko
kungiyar daliban jami'ar Umaru Musa yaci tura.

A satin da ya gabata ne jaruma, Rahama Sadau,
ta yi bikin murnar zagayowar ranar haihuwar ta a
kasar Cyprus.

Shafin komai da ruwanka, Dadinkowa24 munayin aiki Tukuru don jin dadin ku

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin  website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin

Source By ©Arewa Online

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: