Saturday 23 December 2017

Mace Mai Kamar Maza: Na gina gida da sana’ar kafinta – Binta Kafinta

Tura Wannan Zuwa Ga

Malama Binta Muhamamd, wacce aka fi sani
da Binta Maicarbi kafinta
Malama Binta Muhamamd wacce aka fi sani da
Binta Maicarbi kafinta ce da ke gudanar da
sana’ar kafinta a unguwar Kabuga cikin Jihar
Kano.

A tattaunawarta da Aminiya ta bayyana
cewa ta fara sana’arta ne da Naira dubu daya
wacce a yanzu ta kai ga gina gidan kanta da
ribar da take samu. Ga yadda tattaunawar ta
kasance:

Me ya ja ra’ayinki kika shiga sana’ar kafinta duba
da cewa ana ganin sana’a ce da maza?

Zan iya cewa sha’awa ce kawai da kuma rabo.

Da na fara kuma sai na ji ina son abin don haka
na kara jajircewa don na nuna wa duniya cewa
mata ma jarumai ne wajen neman na kansu.

Duk
da cewa ba komai ne mace za ta iya yi ba,
amma akwai abubuwa da dama da mata za mu
yi kamar maza. Ga shi yanzu na dauki kimanin
shekara 17 ina wannan sana’a.

Ina yin aikin gado
da kujeru da sauransu. Babu abin da ba na yi na
aikin sarrafa katako tun daga kan fila da feshi da
sanya yadin kujeru.

Nakan je titin France rod na
sayo katakona da sauran kayan aikin sai na zo
na yi aikin goge shi. Daga nan sai na yanka na
fitar da kowane abu da nake son kerawa sawa’un
gado ne ko kuma kujeru.

Idan na gama sai na zo
na sa pila in goge. Sannan idan suka bushe sai in
kunna inji na goge su wato na yi musu feshin
fenti.

Duk da cewa mun fi yin sababbin kaya,
amma muna sayen tsofaffin kaya don sayarwa
kodayake a lokuta da dama sai na sake gyara su
sannan nake sayar da su.

Shin kin fuskanci kyama daga wurin ‘yan uwanki
mata ko kuma abokan sana’arki maza wadanda
za su ga sana’arsu ce kika yi wa shisshigi?

A gaskiya da farko na fuskanci wannan matsala,
amma a yanzu da rayuwa ta sauya kowa ya fito
neman na kansa mun zama abin sha’awa a
tsakanin ‘yan uwana mata, domin a yanzu da
kansu suke zuwa sayen kayana, kuma su kawo
min masu saye har ma na ba su wani abu.

Haka
kuma su kansu maza kafintocin sun nuna min
kyama domin za ki ga yadda suke kushe wa
mutum aiki a maimakon su karfafe shi.

A wasu
lokuta ma zan so shago na tarar an kone min
kaya, amma da na yi hakuri ga shi komai ya
wuce.

A matsayinki na mace yaya kike yi wajen hada
aikin gida da kuma sana”arki?

A baya dai na sha wahala ta zirga-zirga, amma
cikin ikon Allah da yake na kuduri aniyar cewa
zan iya yi sannan kuma maigidana ya bani goyon
baya, hakan na rika hada wadanan abubuwa biyu.

Cikin ikon Allah ga shi har yanzu muna ci gaba
da yi.

Yanzu kuwa abin ya yi sauki domin ina da
budurwar yarinya a gida wacce take taimaka min
da ayyukan gida.

Yawanci ina zuwa shago da
misalin karfe 11 na safe sannan aduk lokacin da
karfe hudu ta yi to na koma gida. Sai dai idan da
wani abu muhimmi da zai tsayar da ni.

Wacce nasara kike jin kin samu daga wannan
sana’a?

Babu shakka ina takama da wannan sana’a tawa,
domin da ita nake rike da iyayena da ‘yan uwana.

Baya ga filaye da na mallaka da wannan sana’a
na gina gida. Haka kuma na mallaki shaguna da
nake zuba kayana a ciki.

Alhamdulillahi babu abin
da zan ce sai godiya. Idan an duba na fara
wannan sana’a ne da Naira dubu daya kacal.

A
wancan lokaci nakan je na sayi ‘yan kayan
katako na hannu na kai wa masu saye su saya.

Yau da gobe ina yin haka har na sami jari na fara
wannan sana’a.

Wane irin matsaloli kike fuskanta a wannan
sana’ar?

A gaskiya akwai kalubale musamman wasu
lokutan mutane za su sanya a yi musu aiki a
dauka akai musu wasu garuruwa kamar Zariya da
Zamfara da Fatuskum, bayan mutum ya sa
kudinsa ya yi aikin ga kuma kudin motar daukar
kaya da ya biya, idan aka kai musu kayan sai su
ki biyan kudin.

A wasu lokutan kuma mutane
suna sanya wa a yi musu aiki sai kuma su kasa
biyan cikon kudin kayan, haka za a bar mutum da
kaya sai dai ya saka a kasuwa.

Mutane nawa ne ke karkashinki?

Kin san da yake mutanen suna zuwa suna tafiya
ne. idan mutum ya dade a hannuna ya koyi aiki
nakan yaye shi shi ma ya je ya kafa nasa shagon
don cin gashin kansa.

A yanzu haka irin wadanan
mutane suna nan suna gudanar da sana’arsu ta
kafinta a wurare daban-daban.

A halin yanzu dai
akwai mutane takwas da ke zuwa su yi aiki a
karkashina wadanda kuma suke samin na abinci
a kullum.

A lokuta da dama ana kuka da ku kafintoci game
da rashin cika alkawari me za k ice akan hakan?

Gaskiya ne wannan, wanda kuma a tunanina
hadama ce take kawo hakan. Ban sani ba ko don
kasancewata mace ba na hada wa kaina aiki da
yawa, ma’ana idan na ga aiki ya yi min yawa
idan an kawo min aiki nakan gaya wa mutam
halin da ake ciki, inda nake kai su wasu wuraren.

Wace shawara za ki bayan uwanki kafintoci a
kan hakan?

Ina shawartarsu da su rike gaskiya da amana,
domin duk abin da mutum zai yi idan babu
wadannan abubuwa to ba zai sami nasara ba.

A
mastayinka na kafinta idan har mutum ya nemi
ka yi masa aiki har ya dauki kudinsa ya ba ka
kuka tsayar da lokaci to kamata ya yi ka yi
kokari ka yi masa. A gaskiya Allah Ya yi wa
wannan sana’a tamu albarka, akwai rufin asiri a
cikinta.

Wane kira kike da shi ga gwamnati ta yadda za a
inganta muku wannan sana’a taku?

Ina ganin ya kamata gwamnati ta dube mu
musamamn matan da ke cikin wannan sana’a ta
yi kokarin bunkasa mana wannan sana’a tamu ta
hanyar ba mu jari sosai yadda za mu rika
gudanar da wannan sana’a.

A wasu lokutan kin
san yadd mata suke babu karfin jari, sai ki ga
abubuwan ba sa yin daidai. Muna bukatar
gwamnati ta kawo mana dauki.

Muna bukatar
kayan aiki na zamani saboda har yanzu da
tsofaffin kayayyaki muke amfani.

Muna so kuma
gwamnati ta ba mu fili da za mu rika zuba
kayanmu idan mun kera.

Zan kuma yi amfani da
wannan dama wajen kira ga ‘yan uwana mata da
mu tashi mu nemi na kanmu kasancewar
zamnani ya canza dole sai mace tana neman na
kanta sanann abubuwan gida suke tafiya daidai.

Ba duk namiji ne zai iya biya wa mace bukatunta
ba.

Ina kishin na ga ‘ya mace tana kwance babu
sana’a. don haka akwai bukatar mata su tashi su
jajirce domin su dogara da kansu.

Shafin komai da ruwanka, Dadinkowa24 munayin aiki Tukuru don jin dadin ku

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin  website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin

Source By ©Aminiya

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: