Sunday 24 December 2017

Karanta Cikakken Tarihin Shehu Usman Dan Fodio : Abubuwan da Yakamata Ku sani dangane da Rayuwar Mujaddadi Shehu Usman Dan Fodio

Tura Wannan Zuwa
Takaitaccen Tarihin Shehu Usman Ɗan Fodio Abubuwan da Yakamata Ku sani dangane da Rayuwar Marigayi Shehu Usman Ɗan Fodio - Hotuna da Cikakken Tarihi







Kashi na ɗaya

Gabatarwa

Limamin yakin Jaddada addinin musulunci da
kore bidi'a gami da hana sarakuna aikata
ayyukan masha'a da zalunci a kasar Hausa dama
makwabta shine Shehu Usmanu Bn Fodio.

Hakika, tarihin wannan yaki ba zai taɓa cika ba
har sai an haɗa da wani yanki na rayuwar shehu
Usmanu ɗan fodio.

Shi Bafillatani ne, jinsin toronkawa.
Cikakken
sunansa shine Usmanu, ɗan Fodio ɗan Usmanu
ɗan Salihu ɗan Haruna ɗan Muhammadu Gurɗo,
ɗan Jabbo ɗan Abubakar ɗan Musa Jakollo
wanda akace ya auri 'yar Imamu Demba, kamar
yadda Marigayi wazirin sokoto ya ruwaito a
littafinsa Mai suna 'Tarihin Fulani'.

An haifi shehu Usmanu a ranar wata lahadi ta
karshen watan safar, shekarar 1168 hijiriyya
(wajajen 1759 miladiyya).

Yayi karatun Alkurani a gaban mahaifinsa, ya koyi
ilimin fikihu bisa mazhabar Imamuna Maliku ɗan
Anas a gaban Mallam Abdurrahman ɗan Hamadi,
ya koyi karatun littafin ishiriniya da wasu
littattafan addini a gaban malamin sa Usmanu
Bakabe.

Haka kuma ya koyi karatun littafin Muhtassar
daga kawunsa mallam Bibnoduwa, wanda yake
gwani ne a fagen tsoron Allah da ilimi, gami da
umarni da kyawawan ayyuka da kuma hani ga
aikata mumunana.

Hakika, ance ta hanyar zama dashi shehu
Usmanu ya koyi halayen kirki da gudun duniya
masu yawa.
Baya da haka, shehu Usmanu ya zauna shekara
ɗaya a hannun Sanannen Malami Mal Jibrila
(wanda ta hanyarsa alaka ta samu tsakanin
shehu Usmanu da Mallam Bakatsine) yana
ɗaukar karatu. Tare dashi ma sukaje Agadez,
sannan malamin ya mika shehu Usmanu ga
mahaifinsa yayin da shikuma ya wuce aikin Hajji,
domin a lokacin shehu usmanu bai karɓi izinin
tafiya Hajji daga mahaifin saba.
Sannan dai, shehu Usmanu ya zauna da kawunsa
Mallam Ahmadu ɗan Muhammadu yana koyon
karatu, har ma a wajensa ya koyi tafsirin
Alkur'ani maigirma. Daga nan kuma sai ya sake
zuwa gaban Mallam Hashimu Bazamfare, inda ya
zauna daram yana sauraren tafsirin Alkurani
maitsarki tun daga farko har karshe.
Wannan shine kaɗan daga tarihin karatun shehu
usmanu.
Don haka kamar yadda yake a ɗabia ta ilimi,
kafin wani lokaci sai Allah ya cika zuciyar shehu
usmanu da ilimi, saboda haka sai shima ya soma
bayarwa ga mabukata, a haka har ya zama
cikakken malami.

KIRA ZUWA GA TURBAR MUSULUNCI TA
GASKIYA DA BARIN BIDI'O'I

Ance shehu Usmanu ya fara wa'azi ne da kiran
mutane a mazauninsa dake Degel.
A lokacin, yakan tara mutane yayi musu nasiha
da faɗakarwa, sannan kuma yana rubuta musu
wakoki da Ajami.

A wancan zamanin, shehu ya tarar da cewa Mafi
yawan sarakuna kafirai ne, Shugabannin su kuma
ko dai kafirai ko kuma fasikai.
Sannan bidi'o'i sun
yawaita a gari, har ma an jirkita addini daga
yadda yake.

Sannu a hankali mutane suka soma karɓar kiran
shehu Usmanu, har ya zamo wasu na binsa gari-
gari don yin wa'azi, amma ko kaɗan baya zuwa
ga sarakuna don neman wata bukata.
Sa'ar da Shehu Usmanu ya soma zuwa ga wani
sarki shine lokacin daya lura mutane sunyi yawa
gareshi, kuma ya samu shahara, don haka yaje
ga sarkin Gobir Bawa Jan Gwarzo a fadarsa dake
Alkalawa yayi masa wa'azi, ya kirashi izuwa
addinin musulunci na hakika tare da tsayar da
adalci a mulkinsa, sannan ya koma masaukinsa.

Haka kuma ance a wannan ritsin ne Shehu
Usmanu ya tafi zamfara yana wa'azi, har sai
daya shafe shekaru biyar acan wajen faɗakarwa.

Kuma ance yasha wahala sosai a lokacin, saboda
zamfarawa sunyi nisa wurin jahilci da bidi'a.
Da shaharar shehu Usmanu ta fara yin tsamari,
sai sarakunan Hausa suka soma kishi gami da
damuwa da lamarinsa.

Ana haka sai sarkin Gobir Bawa Jan Gwarzo
rannan ya aika masa yazo, nufinsa idan yazo ya
halaka shi. Sannan kuma ya aikewa malumman
yankinsa duka suzo domin su shaida kisan shehu
Usmanu da Jama'arsa.

Sai dai, lokacin da Shehu Usmanu ya riski fadar
Sarki Bawa, sai ya tarar ya tafi Sallar Idi, don
haka shima sai yaja zugar mutanensa suka tafi.
Wani abun mamaki daya faru a zamanin shine,
Sarki Bawa da jama'arsa suna masallaci don
sallar idi sai ga zugar shehu Usmanu tana
tahowa, aikuwa nan take mutanen Sarki Bawa
suka tashi fuuu izuwa gaban shehu, ance Bawa
kaɗai aka bari a wurin.

Kuma tun daga nan ya
tsorata da lamarin shehu Usmanu.
Da aka kare sallar Idi, sarki Bawa ya zauna cikin
barorinsa da Bayinsa cikin damuwa, yayinda
shehu Usmanu ke tare da zugar Malumma sama
da dubu suna ta caffa tsakaninsu.
Shine har
akace da wani abokin sarki Bawa ya lura da da
halin dayake ciki, sai yace masa "Ya sarki, kayi
sani cewar mutum ɗaya ba zai iya aikata abinda
kayi nufi ba a zuciyarka, sai dai Allah".
Sai Bawa ya kira shehu Usmanu gareshi, ya
umarci a bashi awo na zinariya guda ɗari. Amma
sai shehu yace masa " Kayi sani ya wannan
sarki, dani da jama'ata bama bukatar dukiyarka,
sai dai ga bukatu na a gareka
Na ɗaya, kabar ni inyi kira zuwa ga addinin Allah
a garinka.
Na biyu kada a hana kowa dake son karɓar
addini.
Na uku ka sanya Alfarma ga dukkan masu hula
da rawani.
Na huɗu ka saki dukkan waɗanda ke ɗaure a
kurkukun ka.
Sannan na biyar a daina amsar haraji mai
tsauwalawa daga talakawa."
Abinda akayi kenan, sarkin Gobir yace " Na baka
dukkan abinda ka nema, na kuma sahale maka
yin duk abinda kake son yi acikin garin mu"
Daga cikin fursunonin da aka saki a lokacin, har
da Sarkin Zamfara Abarshi.
Shi kuwa Bawa Jan Gwarzo, sai nemi da shehu
Yayi masa addu'a yaci garin Maraɗi da yaki.
Saboda an samu a lokacin, adawa tayi tsanani
tsakanin masarautar Gobir data maraɗi, har kuma
cinye Maraɗin ya gagari sarki Bawa
Nan take Shehu Usmanu yayi masa addua, yace
masa " Na baka maraɗi, zaka kuwa cinyeta da
zarar ka sauka gareta, amma kada ka wuce ta"
Daga nan Bawa da Shehu usmanu sukayi
sallama, shehu ya juya da jama'arsa ya nufi
Degel, shikuwa Bawa ya tsaya jim yana kallon
Shehu yana tunani gami da mamaki. Sannan
yakira sunan mutanensa har sau uku yana mai
cewa "Jama'ar Gobir!, jamaar Gobir!!, Jamaar
Gobir!!!, kunga wancan Bafillatanin? Ina baku
labari cewa babu sauran Sarki a bayana, sai dai
Uban Unguwa"
Sai kuma ya shiga tara dakaru da kayan faɗa,
domin zuwa murkushe garin Maraɗi da yaki.
Ace ya tara gagarumar runduna wadda rakuma
arbain ne ke ɗaukar mata goran ruwansha, da
kayan faɗa masu yawa, sannan suka nufi
maraɗi.
Haka Kuma kamar yadda shehu Usmanu yayi
masa albishir, Bawa yaci Maraɗi da yaki cikin
kankanin lokaci.
To amma da yaga wannan nasarar ta samu, sai
yace "Munga adduar shehu, yanzu kuma zamuga
aikin Masun mu"
Kurum sai yaja tawagarsa suka shige maraɗi
izuwa wani gari mai suna 'Dan Kace'.
Ai kuwa da saukarsa a garin, mutanen garin suka
ce dawa Allah ya haɗamu ba dakai ba, sai suka
rufar masa da yaki, suka kuma samu gagarumar
galaba akansa, har takai sun kashe ɗansa da
yake matukar so.

Haka Sarki Bawa Jan Gwarzo ya taho da sauran
dakarun da suka rage masa cikin kunchi da ɓacin
zuciya, kafin ya iso Birninsa Alkalawa, ajali ya
riskeshi a wani gari mai suna Naya...

Kashi na biyu

Rasuwar Sarkin Gobir Bawa Jan Gwarzo keda
wuya sai ɗan uwansa mai suna Yakubu ya
gajeshi.
A lokacin kuma Shehu Usmanu ɗan fodio ya
zauna a daular zamfara, har ma yana ganin
aikinsa na wa'azi daya shafe shekaru yana yi a
yankin ya samu nasara, don haka gudun kada
duniya ta ruɗeshi sai ya koma mazauninsa Degel.
Sarkin Gobir Yakubu kuwa da hawansa mulki, sai
ya shiga shirin yaki don tafiya garin Dankace
ɗaukar fansar ɗan uwansa Bawa Jan Gwarzo.
Ance akan hanyarsa ta tafiya, Shehu Usmanu ya
aika masa da kira izuwa tafarkin tsira, tafarkin
musulunci na gaskiya.

Kuma ana ganin yayi yunkurin bin kiran shehu
Usmanu da fari, amma sai mutanensa suka hana.
Sai dai shima koda yaje Dankace da yaki acan
hanya ya mutu bai dawo Alkalawa da rai ba.
Shehu Usmanu ya shiga yankuna makwabta yana
wa'azi, shine har cikin garuruwan kasar Kabi
(Kebbi) yana kira izuwa musulunci tare da barin
shirka da bidi'a, ya tsallaka gulbin Kwara mafi
girma a wannan yanki, har ma ya isa wani gari
mai suna Ilo (Ilorin) ya kai musulunci, kamar
yadda ya faɗa a wakensa inji Wazirin Sokoto
Junaidu.
Bayan Mutuwar Yakubu, sai ɗan Uwansa Nafata
ya gajeshi.
Shikuwa a kullum cikin k'ulla sharri yake ga
Shehu Usmanu.

Watarana sai ya kira Shehu Usmanu izuwa
fadarsa. Nufin sa idan yazo ya halaka shi.
Don haka shima sai ya tara sarakuna da
malaman daularsa, ya zauna a tsakaninsu akan
kujera, sannan ya hori shehu Usmanu ya shigo
gareshi.
Akace, koda Shehu Usmanu ya shigo, sai kuwa
wani kurji dake wuyan Sarkin Gobir Nafata ya
fashe, nan take ya faɗi sumamme. Aka ɗauke
shi izuwa gida magashiyyan baya iya magana.
Shehu Ya koma Degel. Yumfa ɗan Yakubu shine
yayi masa rakiya a lokacin.

Sa'ar da zasu rabu, sai shehu ya cewa Yumfa
"Ya kai Yumfa, hakika al'amarin ubanka ya kare,
alamari gareka yake, kayi kokari" (Yana masa
maganar mulki ne)
Sai Yumfa yace, "Hakika idan na samu mulki,
bazan aikata irin aikin da iyayena suka aikata
gareka ba, don haka zanyi ɗa'a ga kowanne
alamari"
Daga nan suka rabu, Yumfa ya koma gida ya
zauna abinsa.

Kuma koda Nafata ya rasu, sai aka naɗa shi
Sarki.
Yayi hawa ya tafi ga Shehu Usmanu, kafin ya isa
da tafiyar misalin mil guda, sai ya sauka ya taka
a kafa bisa makirci. Ashe a zuciyarsa cike yake
da fushin shehu da Jama'arsa.
Koda Jama'ar shehu suka ga Sarki da kansa ya
tako a kafa zuwa ga shehu, sai suka rinka cewa
"Bamu taɓa ganin sarki kamar wannan ba"
An ruwaito Shehu Abdullahi kanin Shehu Usmanu
yana cewa "Ni kuwa banga komai daga gare
shiba sai Makirci"
Sarki Yumfa yace da Shehu " Bani aikata komai
daga binda iyayena suka aikata gareka "
Shehu Abdullahi zaiyi magana, Shehu Ummaru
Alkammu ya hana shi, har sai bayan tafiyarsa
sannan Ummarun ya faɗi ga shehu cewa "Hakika,
faɗinsa bani aikata abinda iyayena suka aikata,
ba komai ke nufi ba sai zaiga abinda iyayensa
basu gani ba"
Daga nan fa Sarki Yumfa na Gobir, ya shiga kulla
miyagun dabaru ga shehu Usmanu, burinsa kurum
ya halaka shi.
Rannan, shima sai ya kira Shehu Usmanu izuwa
fadarsa, alhali ya gina rijiya ya kafa masu
acikinta, yasa an rufe samanta da tabarma.
Shehu Usmanu ya taho tare da Kaninsa Abdullahi,
da abokinsa Ummaru Alkammu.
Abudullahi yayi nufin zama akan tabarmar da
akace shehu Usmanu akayiwa tanaji, amma sai
shehu ya hanashi, yaje ya zauna shi da kansa.
Suka gama maganganunsu suka kare da sarki
Yumfa, sannan suka koma gida ba tare da wani
abu ya auku ba.
To amma, sa'ar da shehu Usmanu yaga jama'a
tayi yawa gareshi, ga kuma makircin sarakuna na
karuwar musu, sai ya umarci jama'arsa su fara
yin tanajin makamai.

Yace musu " Tattalin makamai sunna ne"
Sannan kuma sai ya shiga adduar neman nasara
daga Allah.

Shehu ya faɗa a wata wakarsa cewa
"Allah ka gwada min rinjayar addininka ga
garuruwan nan namu na sudan domin darajar
Abdulkadiri"

Kashi na uku

HIJIRA DA DALILIN TA

Sa'ar da Sarakuna suka ga jama'ar Shehu
Usmanu na tattalin makamai, sai suka fito da
k'iyayyarsu a fili garesu.

Suka shiga hanasu yin rawani, suna hana mata
lulluɓi.
Da mutanen shehu suka ga haka, sai suka
kauracewa garuruwan sarakunan, izuwa wani
wuri mai suna Gimbana a Kasar Kabi.
Sarkin Gobir ya aike su komo, sai suka k'i.
Sai kuwa ya aikewa shehu Usmanu Sammacin
kira, nufinsa a wannan karon idan yazo ya halaka
shi kota halin k'ak'a.
Shehu Usmanu Bn Fodio da k'aninsa Abdullahi,
da abokinsa Ummaru Alkammu suka tafi ga fadar
sarkin Gobir Yumfa.
Koda Suka shiga gareshi, sai kuwa ya harbesu da
bindiga da nufin kone su da wuta, amma
maimakon haka, sai wuta ta koma gareshi har ta
kusa k'oneshi, ya ruga gida da gudu, sukuwa ko
ɗaya cikinsu bai motsa ba.
ƁBayan ɗan lokaci ya dawo garesu, ya zauna tare
dasu, sannan yace musu "Ku sani bani da wani
makiyi a fili anan duniya kamar ku"
Ya bayyana
musu kiyayya a fili.
Su kuma suka bayyana masa cewar sam-sam
basa tsoronsa. Allah zai karesu daga gareshi.
Sannan suka tashi suka tafi gida ba tare da sun
sanar da kowa wannan ba.
Shehu yace musu Ku ɓoye wannan abu, muyi
addua kada Allah ya kuma haɗa mu da wannan
kafiri. Shehu yayi addu'a suka amsa da Amin,
sannan suka shafa fatiha suka koma gida.
A lokacin, sai sarkin Gobir ya haɗa runduna ya
tafi yak'i da jama'ar Abdussalamu a Kabi, ya
kuwa samu nasara akansu, ya kashe na
kashewa, ya kama na kamawa, saura kuwa suka
warwatse neman mafaka.
Wannan sai ya k'ara masa girman kai da jiji-da-
kai, yana ɗagawa shi sarki ne mai cikakken iko
da ɗumbin nasara.
Da yake acikin mutanen da aka kama, da
yawansu mutanen shehu ne da sukayi hijira, sai
mutanen Sarkin Gobir suka taso keyarsu izuwa
Gobir, kuma suka biyo dasu ta garinsu shehu
Usmani, ta gabas da gidansa ma.
Wannan yasa mutanen shehu suka kamu da
tausayin 'yan uwansu, har suka kasa jurewa suka
rufarwa dakarun sarkin Gobir tare da kuɓutar da
'yan uwansu.
Da dakarun sarkin Gobir sukaga haka, sai suka
runtuma da gudu gaban sarkinsu, suka zaro
kibbau daga kwarinsu, sannan suka gabatarwa da
sarkin, suna masu cewa "waɗannan kibiyoyin
jama'ar shehu ne da suka harbe mu suka k'wace
duk binda muka tafi dashi".

Hakan kuwa sai ya fusata Sarkin Gobir Yumfa
kwarrai da gaske, yace "Hakika dmsun cimma
abinda suka so, amma zasu gani".
Sai kuma ya aikewa shehu Usmanu cewar ya fita
dashi da iyalinsa izuwa wani wurin daban, ya
rabu da jama'arsa anan.

Shehu Usmanu kuwa yace sam bazaiyi haka ba,
sai dai duk abinda zai samu jama'arsa ya
samesu baki ɗaya.
Shehu ya aika masa da Cewa "Ni kam bani
rabuwa da jama'a ta, amma ina iya rabuwa da
garuruwanka, kasar Allah yawa gareta".
Daga nan Sai Shehu ya shiga shirin yin Hijira.
Sarki Yumfa ya sake aiko masa da ɗan aike yana
rarrashinsa da kada ya tashi daga inda yake.

Amma sai shehu Usmanu yace "Hakika, ni bani
fita daga kasarka, amma zan sauka a gefen
garuruwanka"
Ai kuwa, sai Shehu Usmanu yayi hijira, yabi ta
hanyar Kwarin Gezo, ya shiga ta Demba, yabi ta
Kalmalo, ya shiga Farkaji, sannan ya isa Ruwa
wuri, sannan ya riski wani rafi da ake kira 'Gudu'
dake gefen kasar Gobir ya sauka da hijirarsa
anan, a ranar alhamis 12 ga watan zulk'ida, na
shekarar 1218 bayan hijirar Ma'aiki Annabi
Muhammad tsiran Allah da aminci su tabbata a
gareshi.
Koda ya isa wurin, ya tarar Aliyu Jedi tuni ya
shirya masa masauki.

Shikuwa Agali, shine ya taho da rakuma ɗauke da
littattafan shehu Usmanu...



Kashi na huɗu.

Shehu Usmanu Dan fodio yayi godiya ga Allah
bisa ni'imar da yayi masa bayan ya sauka a Gudu
wurin hijirarsa, sannan ya nemi a gabato masa da
gadon wa'azinsa.

Daga nan sai ya tara jama'arsa duka a wurin,
sannan ya hau kan gadon wa'azinsa yana musu
wa'azi.
Anan ne yace musu "Na cire sarautar dukkan
wani mai sarauta sai wanda yazo mini nan"
A lokacin kuwa, Sarki Ashiru ne kaɗai yazo
gareshi, don haka da akayi yakin jihadi aka barshi
da sarautarsa.

Haka kuma, shehu yayi addu'a ga mutanensa
cewa "Duk wanda ya fitad dani daga gidana,
Allah ya fitar dashi daga nashi."
Mutane suka
amsa da Amin. Akayi addua aka tashi.
Daga nan sai Kaninsa Abdullahi yazo gareshi yayi
masa mubaya'a (ta yin jihadi), sai kuma ɗansa
Muhammad Bello shima yazo yayi sannan sai
abokinsa Ummaru Alkammu, sai sauran jama'a
kuma duka kowa yazo yayi.

Daga wannan rana, Shehu Usmanu da Jama'arsa
suka ɗaura shirin soma yaki da sarakunan duk da
basu biyo wannan tsari nasu ba.

FARA YAKIN JIHADI

Sa'ar da Shehu Usmanu da jama'arsa suka yi
hijira, sai Sarkin Gobir Yumfa ya umarci
sarakunan garuruwansa da cewar, su kame duk
wani mai shirin zuwa ga Shehu Usmanu.
Ai kuwa sai suka shiga fitinar musulmai mabiya
Shehu Usmanu da kisa, azabtarwa gami da
kwace dukiya.
Da wannan hali ya k'azanta, sai musulman da
sukayi hijira suka soma fita yakin jihadi izuwa
garuruwa.
Ya zama suna kame kananun garuruwa a hankali
har sukazo wani gari waishi Giniga, yaki kuwa
yayi tsamari anan.

Ance duk da an halaka musulmai da dama a
yakin, wasu manya kuma daga tawagar Shehu
sunyi shahada, amma dai saida sukayi nasarar
kame garin. Suka kashe na kashewa, wasu kuma
aka kame su.

Daga nan suka fita yaki zuwa Matan Kari, nan
ma suka ci garin da yaki, suka sake nufar wani
gari mai suna Wata Alkarya, shima suka cinyeshi
da yaki, sannan suka samu nasarar cinye garin
K'wanni da yaki.

A wannan shekara ta farko dai, an gwabza yake-
yake masu tsauri, amma cikin ikon Allah duk
mutanen shehu ke samun nasara.
Akwai Yakin Kwato da akayi a shekarar, shikuwa
yaki ne mafi girma wanda sai dai a Kwatantashi
da Yakin Badar a tarihin kafuwar Musulunci, ko
kuma yakin Daukar girma a tarihin Yakin Jihadin
mutanen shehu Usmanu a Kano.
Sarkin Gobir fa sai hankalinsa ya dugunzuma, ya
shiga shirin yaki haikan.
Ya aike da takardu na neman taimako izuwa
sarakunan Katsina, Kano, Zazzau, Daura da
Azbin, duk kuwa saida suka bashi tallafin daya
nema, sannan suma suka ɗaura ɗamarar yaki da
duk wani mai alaka da Shehu Usmanu a
biranensu.
Daga nan Sarkin Gobir Yumfa ya fita daga
garinsa, ya kwana a 'Bore, sannan yahau ya riski
Gamba, yabi ta Makida, sannan ya sauka a Tsara
ya kwana. Daga nan sai gashi a Janar-Sarki ya
kwana biyu anan yana sauraren wasu k'arin
dakaru. Bayan sun isone ya fuskanto Gudu da
gagarumar runduna.
Koda Shehu da Mabiyansa suka ji Labarin yaki na
gabato su, sai suka ɗau harama suma.
Wazirin Shehu, kuma kaninsa, watau Abdullahi,
ya taso da rundunar mayaka izuwa gefen wasu
gidaje suka sauka suna jira, har yamma tayi
basuji komai ba, sai suka koma da baya.
A kwana na biyu ma suka sake yin kamar haka,
amma babu abinda ya faru.

Sai a kwana na uku ne wasu 'yan uwansu fulani
suka iso garesu a sukwane, suka shaida musu
cewar daga cikin rundunar sarki Yumfa suka sato
jiki, kuma yaki ya kusa zuwa garesu, tunda kuwa
rundunar tana garin Ayame ne, tsakaninsu da
garin kuwa tafiyar yini ɗaya ce..

Zan dakata anan sai mun hadu daku a kashi na Biyar don haka Ku cigaba da Kasancewa da Shafin Muryarhausa24.com.ng aduk inda Ku ke afadin Duniya
Rubutawa Sadiq Tukur Gwarzo Tace Rubutu da haɗawa Muhammad Kabiru Muhammad (M. Kabiru Muhammad)


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, FADAKARWA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com 

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki Mungode

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user