Monday 8 January 2018

BA RABO DA GWANI BA: TUNAWA DA AHMED S. NUHU DA HAWWA ALI DODO-Karanta Kaji

Tura Wannan Zuwa
Allahu Akbar! Rai bakon duniya. A duk sabuwar shekara jama'a, musamman masoyan 'yan fim, na tunawa da rasuwar manyan jaruman Kannywood guda biyu - wato Ahmed S. Nuhu da Hawwa Ali Dodo.

Dukkan su sun rasu ne a ranar 1 ga watan Janairu. To amma ba a cikin shekara daya su ka rasu ba. Ahmed ya rasu a cikin 2007 (shekara 11 kenan), ita kuma Hawwa (wadda ake yi wa lakabi da Biba Problem) ta rasu a cikin 2010 (shekara takwas).

Ban da wannan, kowannen su ya rasu a had'arin mota ne. Ahmed ya rasu tare da wasu abokan sa biyu a cikin Jihar Bauchi a kan hanyar su ta zuwa Maiduguri lokacin da motar sa da ya ke tukawa ta kwace ta yi kundunbala da su.

Ita kuma Hawwa, ta rasu ne a kan hanyar ta ta komawa Kano daga Jos, Jihar Filato, kafin su kai Saminaka a Jihar Kaduna, lokacin da mortar su ta haya kirar VW Golf ta fadi da su.

A lokacin mutuwar sa, shi Ahmed bai dade da auren fitacciyar jaruma Hafsat Shehu ba. Ita kuma Hawwa ba ta yi auren fari ba. Hasali ma dai ta ziyarci wani saurayin ta a Jos din ne wanda ya fada wa mujallar Fim cewa ta je ne domin su yanke shawara kan bikin auren su da ya karato.

Bayan mutuwar Ahmed, lokacin da babban aminin sa Ali Nuhu Mohammed ya samu haihuwar d'a namiji sai ya rada masa sunan Ahmed din. Yanzu haka yaron ya girma har ya zama jarumin fim da ya ci kyaututtukan kwarewa a rol din yara a bukukuwan gasar finafinai daban-daban.
Wadannan mace-mace su na daga cikin manyan mace-macen da su ka gigita 'yan fim da masoyan su, wanda har yau ba a fasa yi masu addu'a ba.

Allah Ya rahamshe su, amin.


Source By ©Hausaloaded
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user