Thursday 25 January 2018

Kalli Yadda Saurayi ya Mutu a Wajen Zance da Budurwarsa

Tura Wannan Zuwa
'Yan sandan jihar Katsina a arewacin Najeriya, na tsare da wata budurwa da mahaifinta kan zargin kisan saurayinta.

'Yan sandan sun ce saurayin ya gamu da ajalinsa ne sakamakon wata takaddama da ta kaure kan batun aure tsakaninsu da iyayen budurwar tasa.

Kazalika ana kuma tsare da wani makusancin saurayin budurwar.

Saurayin dai ya yanke jiki ne ya fadi a gidan su budurwar a garin Funtua bayan da mahaifin budurwar ya ce ba zai yadda ya aura ma sa 'yarsa ba.

Saurayin mai suna Ma'aruf Yakubu dan kimanin shekara 22, haifaffen garin shinkafi a jihar Zamfara ne.

Ana dai zargin budurwar tasa Aisha, 'yar shekara 19 da zama sanadin mutuwarsa bayan ita da mahaifinta sun ce ba zai aure ta ba.

Yayin da shi kuma ya shaida wa mahaifin cewa budurwar na dauke da cikinsa.

A zantawar da BBC ta yi da Kanwar mahaifiyar Aisha ta wayar tarho, wadda ta nemi a sakaya sunanta ta ce cutar farfadiya ce ta kama Mu'aruf, a lokacin da ya ke ganawa da mahaifin budurwar tasa.

Kanwar mahaifiyar budurwar ta ce "Shi yaron dama yana da ciwo, kuma ya nemi yarinyar amma ta ki yarda saboda yana da ciwon farfadiya".

Ta ce daga baya ya sami mahaifin yarinyar, inda ya yi ikirarin tona musu asiri, domin yarinyar na dauke da juna biyunsa.

Kanwar yarinya ta kara da cewa uban yarinyar ya yi alkwarin kai 'yarsa asibiti a auna ta ko da gaske ta na da ciki.

Ya kuma ce zai dauki mataki a kan yaron idan har ba ta da cikin.

"Da jin wannan maganar, sai yaron ya yanke jiki ya fadi, har kyaure ya yanke shi", inji kanwar yarinyar.

Ta kuma bayyana cewa daga baya an kai shi asibiti, inda aka yi masa maganin raunin da ya samu. "Daga baya an sallame shi ya koma gidansu, amma da daddare kuma sai Allah ya yi mai rasuwa".

Rundunar 'yan sandan jihar Katsina, ta ce tana gudanar da bincike kan wadanda ake zargi ne don gano ko duka ne ya yi sanadin mutuwar Mu'aruf Yakubu.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Katsina Isah Gambo, ya fada wa BBC cewa: "Wadannan mutane na hannunmu muna kuma yin bincike a kan dalilan da suka janyo mutuwar saurayin."

A bincikenta dai rundunar 'yan sandan katsina ta ce ta hada hannu da hukumomin lafiya da suka yi gwaji a kan ma'aruf kafin a binne gawarsa domin tattabatar da gaskiyar al'amarin.

Source By ©Bbc Hausa
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: