Friday 12 January 2018

Karanta Kasha Mamaki: Cikakken tarihin Jarumi Shahrukh Khan

Tura Wannan Zuwa Ga

A duk lokacin da aka yi magana a kan jaruman fina-finan Indiya, wadanda ake kira fina-finan Bollywood, ba za a kammala ba ba tare da ambato Shah Rukh Khan ba--idan ba a fara da ambato shi ba ke nan.

A shekaru 25 da ya yi a harkar fina-finan Bollywood, Shah Rukh Khan ya fito a fina-finai 62.

Fim din Darr na kamfanin Yash Chopra shi ne fim din da ya fara fitowa da shi a shekarar 1993, amma fim din da ya fara fitowa a cikinsa shi ne Deewana, wanda ya fito a shekarar 1992.

Wani abin mamaki da Shah Rukh Khan shi ne galibin fina-finan da suka daga tauraruwarsa asali ba shi aka shirya ya fito a cikinsu ba, jaruman da aka nemi su fito ki suka yi, ciki har da fim din na Darr.

Shekaru hamsin da biyu kenan da haihuwar jarumi Shah Rukh Khan, wanda aka haifa ranar 2 ga watan Nuwamba, shekarar 1965 a babban birnin kasar India, New Delhi.

Sunan Mahaifinsa Taj Mohammad Khan kuma tsohon dan gwagwarmayar kwato 'yanci ne a wancan lokacin.

Sunan mahaifiyarsa Lateef Fatima. Marainiya ce ita, kuma ta taso ne a hannun wani janar na soja, kasancewar iyayenta sun rasu a sakamakon wani rikici da aka yi tsakanin 'yan tawaye da gwamnati.

Shah Rukh Khan maraya ne gaba da baya, domin mahaifinsa ya rasu tun yana dan shakara 15 bayan ya yi wata doguwar jinya sakamakon kamuwa da cutar daji, wato cancer. Ita ma mahaifiyarsa ta rasu a shekarar 1990.

A iya cewa rashin mahaifi ya jefa Shah Rukh Khan cikin wahalar rayuwa, musamman ta fuskar karatu.

Ya halarci makarantar St. Columbar's School inda ya karanci wasan kwaikwayo (Drama).

Kafin fitarsa daga makarantar ya zama dalibin da babu kamarsa, inda ya karbi kyautar Sword of Honour. Bayan nan ya wuce zuwa Kwalejin Hansraj daga 1985 zuwa 1988.

Duk da dimbin kalubalen da ya rika fuskanta a rayuwarsa, ya yi nasarar kammala digirinsa na farko a fannin Nazarin Tattalin Arziki (Economics) a wannan makaranta.

Kafin shigarsa Bollywood, Shah Rukh Khan ya fito a fina-finan talibijin, irin su Fauji, da Circus, da Commando Abhimanyu, wadanda suka ja hankalin 'yan kallo. A nan ya fara yin suna.

Tun daga wancan lokacin ne kuma masana suka fara kwatanta shi da shahararren jarumi Dilip Kumar.

Hema Malini, wato mai dakin Dharmmendra, ita ce silar shigarsa harkar fim gadan-gadan, lokacin da ta sanya shi a fim dinta Dil Ashna Hai--shi ne fim da ya fara sa hannu a kan kwantiraginsa; tsaikon da fim din ya fuskanta ne ya sa ya fara fitowa a Deewana.

Babban abin lura game da Shah Rukh Khan shi ne, duk da cewa ya fado harkar a tsakiyar manyan jarumai, wadansu daga cikinsu ma iyayensu ne ke shige musu gaba wajen nema musu labarin da suke ganin zai fi kasuwa, shi kuwa ya zo ba shi da kowa, don akwai finafinan da kusan kyauta ya yi, ba a ba shi wani kudin kirki ba.

Amma da yake mutum ne mai jajircewa da naci, yanzu shi ne Jarumi na biyu a jadawalin jaruman da suka fi wadata a duniya.

Da kansa yake fadin cewa, "Akwai lokacin da sai na yi rancen kudi kafin na samu zuwa inda nake neman a sanya ni a fim."

Kadan daga cikin nasarorinsa su ne: a cikin shekaru 10 ya fi dukkan jaruman da suka zo kafinsa kudi, da suna, da masoya, da fina-finan da suka yi kasuwa da samun karbuwa, domin an yi kiyasi cewa finafinansa wadanda suka shahara sun fi na dukkan takwarorinsa yawa.

Shekarar 1995 na cikin shekarun nasarar jarumin, don ya fito a finafinai biyu da suka zama sanadin zamowarsa jarumi lamba daya, wato fim din Karan Arjun inda suka yi haduwar farko a fim guda da jarumi Salman Khan--wanda Rakesh Roshan ya ba da umarni kuma ya samu karbuwa sosai a ciki da wajen Indiya, sai Dilwaale Dulhaniya Le Jayenge, fim na biyu da Khan ya yi a karkashin kamfanin Yash Raj.

Tsakanin shekarun 1998 zuwa 2002 ya zama jarumin da duniya ta san da zamansa, wato International Icon a Turance, sakamakon rawar da ya taka a fina-finai irinsu Kuch Kuch Hota Hai, da Dil Se, da Badshaah, da Duplicate, da Mohabbatein.

Duplicate fim ne na barkwanci kuma ya fito tare da Juhi Chawla da Sonali Bendre. Duk da wannan fim bai samu kasuwa sosai ba, hakan bai hana masana harkar fim yaba masa ba saboda rawar da ya taka ta mutum biyu (double role).

A shekarar 2000 shi da abokiyar aikinsa Juhi Chawla, suka yanke shawarar bude kamfaninsu na kansu mai suna Dreamz Unlimited.
Bayan kammala yarjejeniya suka fara da fim na farko Phir Bhi Dil Hai Hindustani wanda Aziz Mirza ya ba da umarni. Daga nan ya fito a cikin Josh na Mansor Khan tare da Aishwar Rai Bachchan.

Jerin wasu daga cikin fina-finansa da suka samu gagarumar nasara a duniyar fim su ne: Anjaam, da Dil To Pagal Hai, da Badshaah, da Kabhi Haan Kabhi Naa, da Chahat, da Raju Ban Gaya Gentleman, da Kabhi Khushi Kabhi Gham, da Devdes. Sauran su ne Chalte Chalte, da Swades, da Kal Ho Naa Ho, da Main Hoon Na, da Kabhi Alvida Naa Kehna, da Chekde India, da Veer Zaara, da Om Shanti Om, da kuma Rabne Bana Di Jodi. Akwai kuma My Name Is Khan, da Ra One, da Jab Tak Hai Jaan, da Chennai Express, da Happy New Year da Dilwaale da Fan da Dear Zandagi da Raees da Jab Harry meet Sejal, Yanzu haka yana kan aiki akan wani shiri da ba'a bashi suna ba wanda Anand L Rai yake bada Umarni.

Babbar gudunmuwarsa ga harkar fina-finan Bollywood ita ce, yadda ya dauke ta daga harkar cikin gida, ya daukaka ta ta samu karbuwa a duk duniya.

Fina-finansa ne suka fara karbuwa a kasashe irin su Amerika, da Ingila, da Australia, da Jamus, da Morocco, da Faransa, da Italiya, da Indonesiya, da China, da Japan.

Shi ya sa ma a wani babban gidan ajiye kayan tarihi da ke birnin Landan aka yi mutum-mutuminsa domin tunawa da shi.

Har ila yau, kasar Faransa ta karrama shi da lambar girma mafi daraja wato Legend de France.

Sannan ya bude kamfani mai suna Red Chillies Entertainment wanda daruruwan matasa ke cin abinci a karkashinsa.

Ya fi kowanne jarumi yawan lashe kyaututtuka a kasar Indiya, domin yanzu a gidansa akawai kambi kusan 217, wanda babu jarumin da ya ke da yawan nasa.

Yana da mata daya, Gauri Khan da kuma 'ya'ya uku, Aryan Khan, Suhana Khan da Abram Khan.

Yana zaune a gidansa da ke unguwar Bandra, cikin yankin Maharashtra na birnin Mumbai.

Sannan akwai abubuwan da ya bambanta shi da sauran jaruman finafinan duniya: duk da cewa yana da milyoyin masoya, hakan bai hana shi kokarin sadar da zumunci tsakaninsa da su ba, shi ya sa ya kirkiri wani dandali na musamman da masoyansa kan hadu su tattauna, a wasu lokutan ma har da shi.

Jarumin yana yawan hawa dandalin sada zumunta na Facebook da Twitter, domin a yanzu shi ne wanda ya kere kowanne jarumi a Indiya yawan mabiya bayan Amitabh Bachchan.

Yanzu haka, a kusan kowacce kasa, yana da kungiya ta masoyansa mai tsari bisa shugabanci, kuma yana bibiyar abubuwan da suke yi, har yana aikewa da goron gayyata idan wani shagli ya taso.

An tambaye shi wacce kalma bakinsa ya fi furtawa, sai ya bayar da amsa da cewa "AlhamdulilLah" da "Masha-Allah".

Shafin komai da ruwanka, Dadinkowa24 munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address
kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa
kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin
Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://
dadinkowa24.blogspot.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Dadinkowa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Babban Shafi a Yanar Gizo da
ke gabatar da
shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla
cikin 24 Hours ba tareda kakkautawa ba

Burin shafin DADINKOWA24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin

Source By ©Bbc Hausa and Fim Hausa

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: