Wednesday 21 February 2018

Kalli Yadda aka Ma Nura M Inuwa Barazanar kara watsa masa Acid-Bude Kagani Kasha Mamami

Tura Wannan Zuwa Ga

Kamar yanda kuka gani a hoton da yake sama Anyi ma Shaharren mawaki Nura M Inuwa barazana da karasa kashe masa kwayar idonsa ( watsa masa acid)

A shekarun da suka wuce dai anyi Nasarar watsa masa acid sai dai a wannan lokacin yace shge ka fasa kamar yanda ya rubuta a shafinsa na instagram:

" Wannan shine sakon da aka turamin tun kafin ince komai bana nufin kowa da sharri duk masoyina yasan haka bana kokarin gani bayan kowa kuma bansan me yasa suke son ganin nawa ba inada makiyan boye inada na fili wanda duniya ta sani ban kuma san abin danayi musu ba sama da shekaru shida duk wanda ya damu dani sai sunyi kokarin rabani dashi hakane ma yasani fahimtar masoyana suna nesa dani sune wadan ba a sansu bare a hure musu kunne ko ayi musu barazana sau da yawa nakan zauna nayi kukan abin da akemin musamman na nunawa mutane ban kai asoniba da akeyi ko kuma a dauki gaba da wanda yake sona batare da dalili ba duk da kokarin ku na hana mutane bani aiki da kukeyi ALLAH bai hanani ba in mutum ya yabeni ku zageshi inya dora hotona kirashi kuce ya cire duk akan me ?

toni dama ban dorawa kaina kowa za soni ba wanda kuke da iko dasu ku hana su sona ku hana wanda kuma baku da iko kuyi rayuwata da mutuwata bata hanun kowan ku in kuma kunyi nasarar kasheni ku ku gaji duniya ina tare da masoyina duk inda yake zanci gaba da fadawa duniya duk abin dana boye a zuciyata".

Source by ©Fim Hausa

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: