Monday 26 February 2018

KARANTA KAJI: Jarumar films din India Sridevi ta rasu

Tura Wannan Zuwa

Fitacciyar jarumar fina-finan Bollywood Sridevi Kapoor, ta rasu a daren ranar Asabar sakamakon bugun zuciya.

Kanin mijin jarumar, Sanjay Kapoor, shi ne ya tabbatar wa da manema labarai na India labarin mutuwar ta, inda ya ce ta mutu ne Dubai, bayan sun je biki tare da mijinta Boney Kapoor da kuma 'yar ta Khushi.

An dai haifi Sridevi ne a ranar 13 ga watan Augustan shekarar 1963 a Tamil Nadu.

Sridevi ta fara fitowa a fina-finan Tamil ne tun tana karama wato tana da shekara hudu a duniya , amma a shekarar 1975 ne ta fito a fim da girmanta wato fim din Julie, daga nan ne ta ci gaba da fitowa a fina-finai amma na Tamil.

Fim dinta na farko da ta yi wato na Hindi shi ne fim din Solva Sawan wanda aka yi shi a shekarar 1979.

Shekara hudu bayan nan kuma sai aka hadata fim da Jeetandra wato fim din Himmatwala wanda kuma ya yi matukar fice a shekarar da aka sake shi wato 1983.

Daga nan ne fa Sridevi ta koma fitowa a fina-finan Hindi.
Tayi fina-finai fiye da 150 ciki har da wadanda da suka yi fice kamar, Mawali da Sadma da Mr India da Chandni da Nagina da Chalbaaz da Janbaaz da English Vinglish da Chandra Mukhi da kuma fim din ta na karshe da ya fita bara wato Mom.

Ta rasu ta bar mijinta da 'ya'ya mata biyu wato Jhanvi da Khushi Kapoor.
Sridevi ta bayar da muhimmiyar gudunmuwa a fina-finan Bollywood.
Ta karbi lambobin yabo da dama bisa rawar da ta taka a fina-finan.
Tana daga cikin jarumai mata da suke da kyau sosai, da kuma iya rawa.

Ta fara auren jarumi Mithun Jakraborty ba su haihu ba, daga baya kuma ta auri mai shirya fim da bayar da umarni Boney Kapoor, inda suka haifi 'ya'ya biyu mata Jhanvi da Khushi Kapoor.

Tuni jarumai irinsu Priyanka Chopra da Reteish Deshmukh da Sharukh Khan da sauransu suka wallafa alhininsu bisa rasuwar jarumar a shafukan sada zumunta.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Muryarhausa24.com don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum

An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com
Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Muryarhausa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki
daya Amin Summa Amin.

Source by ©BBC HAUSA

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: