Tuesday 13 March 2018

KARANTA TARIHIN TUNAWA DA YAKIN BASASAR JIHAR KANO A NIGERIA

Tura Wannan Zuwa
Galadima Yusufu mutane keso ba Alu ba. A garin Garko yake kuma acan ya mutu. Kafin rasuwar sa, kowa yayi amannar cewa shine zai zamo Sarki, amma sai ciwo ya kamashi har ya mutu a Garko.

Daga nan sai sarakunan bayin Sarki da 'ya'yansu sukace yanzu menene abinyi? Sai wasu sukace abu d'aya ya kamata muyi, mutum d'aya ne kurum zai iya jagorantar mu zuwa Kano. Shine Mallam Babba, Alu kenan. Daga nan suka aika masa, sannan suka dora shi a gadon Mulkin Yusufu.

Bayan sunyi haka, da dare suka binne Yusufu da hasken fitilu. Suka kawo Alu suka zaunar dashi akan karagar mulki. Sukayi masa nad'i. Sai kuma akace fadawa kowa yazo yayi mubaya'a. Kaji yadda Alu ya zamo Sarki. Kuma shine dalilin da yasa dayaji turawa na tafe ya tafi sokoto domin ziyartar hubbalen Shehu tayadda Sarkin Musulmi zai amince da zamowar sa Sarki tare da goya masa baya.

Jama'ar gari, mafarauta da maharba ne sukayi bore ga Sarki Alu a lokacin da yakin Basasa ya barke.

Basasa anan na nufin yakin da akayi don dora Alu akan karagar mulki. Anyi shine a Ramli shekarar 'Ba-Sa-Sha'. 'Sha' a ilimin Hisabi na nufin 1000, 'Sa' na nufin 300, 'a' na nufin 1, yayin da 'ba' ke nufin 2. Idan ka hada lissafi zai baka shekara ta 1303 kenan bayan Hijira. (Dai-dai da 1894 miladiyya).

Ana kiran Alu da suna 'Mallam Babba' (Ma'ana babban malami), domin a wurin mu duk wani dan Sarki Mallam ne koda bai koyi karatu ba. Amma da zarar Sarki ya bashi wata sarauta sai a daina cewa Mallam, a koma kiransa da wannan sarauta.

Alu ya shiga Kano ranar wata Laraba. A wannan lokacin mutane da yawa sun bar Kano izuwa Kamri wajen Tukur, domin shi akafi so.

An kashe Tukur ne a Gurum (Kamri da Gurum wasu kauyuka ne dake kusa da juna a kasar katsina). Naji labarin cewa anji masa raunika sannan aka kawo shi gaban Sarki Alu. Ance Sarki Alu yayi fushi sosai akan cewa don me zasu yiwa d'an uwansa na jini haka? Sarki Alu yace "kuyi maza ku kawo masa ruwa yasha". Amma sai Sarki Tukur yace "kada a kawo min ruwa, azumi nakeyi, bazan sha ruwa ba". A haka kuwa Allah ya amshi ransa. Allahu Akbar!!!

A garin Gurum aka binne Sarki Tukur, shiyasa ake Kiran sa da 'Maje-Gurum' kamar yadda ake kiran Galadima Yusufu 'Maje-Garko', ake kiran Sarki Abbas kuma 'Maje Nasarawa'.

Marigayi Alhaji Mahmud Koki tafinta ne na turawa, shine kuma ya bamu wannan labari. An rubuta labarin a cikin tarihin sa wanda aka wallafa a shekarar 1977.

ASALIN YAKIN BASASA

Sarkin Kano Abdullahi Maje-karofi shine d'a na biyu ga Sarkin Kano Ibrahim Dabo, ya rasu a wajajen shekara ta 1882 miladiyya a wani gari mai suna Kauran-Namoda. Sai k'aninsa Muhammad Bello (shima dan Marigayi Ibrahim Dabo ne) ya hau karagar mulki.

Ance Sarki Muhammad Bello ya rinka kokarin karbe muk'amai daga hannun 'ya'yan 'yanuwansa yana dasa 'ya'yansa na cikin sa. Sannan ya kara yawan jakadu masu tattara Haraji, abinda yayi sanadiyyar jefa talakawa cikin matsi kenan, tare da janyo masa bakin jini a gurinsu.

Ance tun alokacin ya fara sharewa dansa Muhammad Tukur hanyar zama Sarki bayan ya rasu. Ya rinka aikawa da Kyaututtuka izuwa Sokoto domin neman goyon bayan Sarkin Musulmi.

Shikuwa Sarkin Kano Muhammad Tukur, sarkin musulmi Abdurrahman (danyen kasko) ne ya nada shi bayan mutuwar mahaifin Tukur din, watau Sarkin Kano Muhammad Bello. Wasu sunce bai kai shekaru arba'in ba aka nad'ashi mulki, Wasu kuma sunce bashi da karsashin Rike mulki.

A wannan lokacin, sai dan uwansa Galadima Yusuf, wanda yake d'a ga marigayi Sarkin Kano Abdullahi Maje-karofi tare da jama'ar sa suka gudu izuwa garin Takai wadda ke kudu maso gabashin Kano.

Mutuwar Galadima Yusuf ce sanadin dora Sarkin kano Alu a mazauninsa. Sannan a hankali suka rinka cinye garuruwan kano da yaki.

A haka har sai da rundunar su tayi karfi, suka shigo kano a ranar wata Laraba, 19 ga watan agusta na shekarar 1894 miladiyya ana buga tambura na sarauta bayan ya samu nasara akan Sarki Tukur, wanda ya gudu ya bar Kano bayan rundunar yak'insa ta raunana.

Dafatan zamu amfanu da darussan wannan labari.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Muryarhausa24.com don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum

An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Muryarhausa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki
daya Amin Summa Amin.

Source by ©Sadik Tukur Gwarzo
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user