Saturday 10 March 2018

Karanta Yanzu Kaji: A Kalla Mutane Sama Da 15,000,000 Ke Cin Gajiyar Kanikanci

Tura Wannan Zuwa Ga
Injiniya Magaji Muhammad Sani Shine shugaba na farko da aka zaba na kungiyar masu Kanikawa ta kasa da aka fi sani da “NATA’.

A wannan hira da jaridar LEADERSHIP A Yau ta yi da shi ya bayyana mana yadda aka yi har ya kai ga nasarar lashe zaben kungiyar wacce ba a taba samun wani daga shiyyar Arewa da ya taba zama shugabanta ba.

Ga yadda hirar ta kasance:

Injiniya Magaji Muhammad Sani kaine shugaban bakanikan motoci ta kasa da aka zaba. A matsayinka na shugaban wannan kungiya za mu so mu ji tun fari ma yaya ka sami kai a wannan sana’a ta gyaran motoci?

To da farko ina yi wa Allah godiya kamar yanda ka fada na sami kaina a harkar gyara ta hanyar wani maigidana da Allah yayi masa rasuwa mutumin Neja ne, ana kiransa Adamu Wakili yazo ya sameni ina dinka hula zanna, ya ga yadda nake dinkin hular. To an yi masa canjin wajen aiki ne lokacin yana aiki a kamfanin”Philips electronis”aka yi masa canji daga sakkwato ya dawo nan kano. Allah ya hadamu dashi muka saba yana aikena inyo masa kaza inyo masa kaza, sai ya sameni ya ce, Magaji inda zaka yarda dana kai ka wajen koyon gyaran mota kaje ka koya ina ganin zaifi dinkin wannan hular, amma sai in zaka iya daurewa. Na ce, in Allah ya yarda zan daure ya ce, to shikenan. Sai ya je ya sami mutuminda masa gyara a wancan lokacin ana ce masa Mista Godwin shi kuma dan Bendel ne, to da mukaje na fara koyon gyara wannan lokacin a 1976 bayan nayi koyon gyara zuwa 1981 saina bude nawa garejin anan hanyar gidan zoo, bayan na iya aikin daga nan muka ci gaba muna gyara daga 1982, 83, 84 sai Allah ya kawo Gwamnatin Soja ta Buhari sai sukace ba za a rika aiki a ko’ina a bakin titina ba, wannan tasa aka rika tashimmu muje nan, muje nan saida mukaje wajen guda Biyar bayn titin gidan zoo mun zauna a kan titin zariya da Na’ibawa can wajen gidan Fiat” har muka dawo bayan ofishin yan sanda na yar akwa wanda daga wannan lokaci ne 1983 aka bamu gareji anan Kwakwaci a lokacin tsohuwar karamar hukumar Birnin kano lokacin Baffa Usman shine Kantoma. Aka bamu wuri a tsohuwar Kwakwaci inda muke yanzu to munanan a cikin 1985 ya zamanto akwai kotu da ake cewa ta tafi da gidanka, wannan kotu sai ta zo ta same ka a gareji saboda akwai ka’idoji da aka sa a wancan lokacin.

An ce kowane bakanike zai sa Unifom dashi da yaransa da wajen zuba shara za ka yi ban daki da ofis a cikin garejinka, to idan akazo aka samu babu daya daga cikin wadannan abubuwa sai a kama ka ayi maka shari’a ko ka tafi kurkuku ko ayi maka tara ta kudi ka biya in kana dasu.

Ta yaya kuka soma kungiyar masu gyara motoci a Kano?

Da muka ga cewa tunda muna da yawa a matsayin wajen hadaka na Kanikawa da ake cewa sai mukayi shawarar cewa mu hada kungiya , sai mukayi kungiya ta kwakwaci mukasa mata suna Kwakwaci ‘Technicians Debelopment Assocition’wannan yasa muke magana da yawu daya haka muka rika tafiya har 1992 zuwa 93 sai wasu mutane wanda da taimakonsu daya ana ce masa Alhaji Tanko ya rasu a lokacin shine mataimakin shugaban kungiyar NATA a Arewa maso yamma, akwai wani ana ce masa Ahmed Bini shima ya rasu a Bauchi yake, wannan kuma namu a Kaduna yake sai suka shigo sukace me yasa kuka tafi da kungiya ta wani bangare ko karamar hukuma bata kai ba, ga kungiya ta kasa gaba daya,tunda muna da kungiya mu namu mai sauki ne abin da zamuyi kokari kawai mu koma mu amshi wannan kungiyar.
Muka ce to zamuyi shawara,to a wannan lokacin aka yi shawara kuma yawanci makanikai na kasa dana nan jahar Kano aka taru bangare-bangare aka yi shawara aka yanke hukunci aka shiga kungiya bayan an shiga kungiya aka rika tafiya a haka a wannan lokacin Alhaji Bala Isa Sharada shine shugabammu akwai wani Alhaji Mashudi Isma’ila Allah yayi masa rasuwa shine mataimakinsa ni kuma nine sakataren kudi na wannan kungiyar a lokacin daga nan da Alhaji Hamza ya tashi daga nan sai shi Alhaji Mashudi ya zama shugaban na tsohuwar Kwakwaci ni kuma na zama mataimakinsa a haka kuma nazo na zama shugaba na wannan bangaren daga nan akwai shugaban wannan kungiyar da aka shiga “NATA” Nigeria Automobile Technician Association” Hadakar kungiyar masu fasahar gyaran ababan hawa na kasa saboda haka sai aka bada ita a wajen shugaban riko. Alhaji Auwalu Maigari.

Da kungiyar ta kafu sai sukace ya kamata ayi zabe a lokacin mutane suka fito masu sha’awa ni kuma mutane da suka sanni anan sukace lallai sai in fito inyi wannan takara na ce ba zan yi ba,suka matsanta dole inje inyi,haka dai naje mukayi takara dashi wanda ya rike Alhaji Auwalu dani Allah ya bani saboda haka nine zababben shugaba na farko na NATA na jahar Kano bayan na shekara wajen Goma akai daga nan kuma sai su shugabanni abokammu da suke Arewa maso yamma Kaduna, Kano, Kebbi, Sakkwato, Zamfara da Katsina jihohi Bakwai akwai wani ana ce mishi K. Salau ka san na ce akwai mataimakin shugabammu Alhaji Tanko Allah yayi masa rasuwa to sai akaba K. Salau da lokacin zabe yazo sai shugabannin yanda yake tafi da kungiyar basu gamsu ba,suka nuna dasu yarda yayi takara ba sai dai su bani in rike mataimakin shugaba na kasa shiyyar Arewa maso yamma na ce ni bazan rike ba,tunda ina shugaban na Kano. Anan dai aka zartar in rike shugabancin guda Biyu shugaban Kano na NATA da mataimakin Shugabanta na kasa na wannan shiyyar. Bayan na gama mataimakin sai akazo za a yi zabe cikin wannan shekara da muke ciki aka yi zabe 17-1-2018 a jahar Edo a birnin Benin,sai sukace tunda lokacina ya riga ya kare na wa’adina na mataimakin shugaban kungiya ta kasa ya kare tunda nayi sau biyu.
Shekaru Hurhudu karo Biyu na shekara Takwas inayi kamar yanda tsarin mulki ya tsara, tunda bazan sakeyin takra na mataimaki ba sai su shugabannin guda 7 Na wannan shyya sai suka hada kai sukayi taro sukace in fito in nemi shugaban kungiyar ta kasa gaba daya. Bayan sun gama shawara suka sameni na ce musu a’a su bari tukuna lokaci baiyi ba,suka hada kansu sai suka fita,suka sami sauran shiyyoyi da ake dasu a kasa sukace su suna ganin ga dan takararsu,amma menene su kuma shawararsu tunda abune wanda ya shafi kasa gaba daya . Bayan shawara da tuntuba da sukayi sai suma suka goyi bayan in fito, suka zo suka sameni suka fada min na ce su sake dakatawa daga karshe dai har akazo na yarda aka je aka yi wannan takara Allah ya tabbatar dani naci shugabancin NATA na kasa. Wannan kungiya tsohuwa ce amma munan a Arewa da kanikancimma bai dade da zuwa mana ba,amma ba wani da aka taba zaba dan Arewa nine zababbe dan Arewa na farko a matsayin hausa fulani da aka zada a wannan kungiyar .
A tarihinta an kafa NATA ne tun 1919 saboda haka yanzu ana maganar zamuyi bukin cika shekara 100 da kafuwar NATA amma babu wani dan Arewa daya tada shugabancinta sai yanzu da Allah ya kawo mu.

Bayan kai ko wani ya tada kokarin tsayawa daga takara daga Arewa?
Sosai, akwai wadanda suka taba kokarin su tsaya dama wanda aka taba ba riko daga baya aka cireshi, to amma yanzu Allah cikin hikimarsa wannan ma zabe ne muka fito aka yi kuma Allah ya taimakemu, wakilaine suke tafiya suke tafiya yin wannan zabe a ciki kowace jaha tanada mutum uku wakilai sannan da wanda suka sayi fom na takara sune wadanda sukeyin zabe su zabe ka ko a zabesu saboda haka muna da kuri’a guda 225 da aka jefa guda uku ta lalace muna da guda 222 masu kyau a ciki wanda mukayi takara dashi ya sami Takwas na sami kuri’a 214 a zaben to ba abin da zamu yiwa Allah sai godiya kuma muna fata Ubangiji nauyinda ya dora mana ya bamu ikon saukewa.

A baya kayi maganar lokacin da ka shiga harkar gyaran motoci to a wane garaji ka soma. Sannan an yaye kane ka kafa garejinka ko yaya aka yi?

Eh, ka san kamar yanda na gaya maka kasan mu. muna da ka’idoji zaka zauna inka koyi aikin an yayeka zaka san cewa, inane kakeso ka tafi koka zauna wajen me gidanka ko kuma in kana ganin zaka iya bude naka garejin sai kaje ka bube in kuma zaka zauna a wajen mai gidanka saika zauna a matsayin ma’aikaci me yiwuwa kuyi yarjejeniya menene zai rika baka a sati ko sati biyu ko wata wanda a lokacin da ake nake koyon aiki garejimmu yana can Ado Bayero Skuire a cikin sabon gari”New road”.

A nan ne garejin mu yake a lokacin abin da nake biya kudin bas gidanmu yana nan kofar mazugal wajen gidan mai sikeli. Idan na fito daga nan zuwa ‘yan kura sule ne ake biyan kudin mota amma wani lokacin idan banida kudin a kasa nake tafiya kuma wani lokacin ba tare da naci abinci ba, sai dai in sha ruwa.
Haka na rika tafiya koyon aikin in dawo, akwai wani abokina mai shayi anan kofar mazugal unguwarmu in nazo wani lokacin a wajensa zan hada shayi na silai Biyu insha ranarda Allah yasa naje na sami wani kona wanke masa injin mota inya bani Naira daya ko biyu sai inzo in biya bashinda yake kaina, saboda in sake samun dama in sake ci gaba da karbar wani bashin har saida wataran wannan kuwa ya farune saboda shi wanda ya kaini wajen aikin, bai san cewa ba’a bani kudin abinci a can ba kana shi kuma mai gidammu bai san cewa ba’a bani kudi daga gida in zan taho wajen koyon aikin ba.
Ranar da Allah ya tashi yanke abin wanda ya kaini yana aiki a “Lebentis Motors”Yazo cin abincin rana yazo ya zauna yaci abinci kusada inda nake koyon aiki sai ya kirani ya ce, magaji a ina kake cin abinci ne? Na ce, abin da Allah yasa na samu anan ko idan na wanke mota a lokacin kuwa nine nake sayo kayan aikin mota kudaden suna hannuna, amma bana tabawa tunda nasan ba nawa bane, koda na dauka ba inda zasu kai ni. Saboda haka na ce abin da na samu a wankin injin mota ko ta wani abu dashi nake cin abinci inyi kudin mota in ban samu ba in tafi a kasa.
Ya ce, me yasa kai baka taba gaya min ba, na ce saboda baka taba tambayata ba, sai ya girgiza kai ya ce, daga Yau duk lokacin da nazo cin abincin rana kazo ka amshi N200 a lokacin bana iya cinye abincin sile biyar shinkafa da wake da kifi saboda haka tun daga wannan ranar har yanzu da nake maka magana ba ranarda na tashi na rasa abin da zanci.

Zuwa yanzu wane irin gudummuwa Kanikanci ke bayarwa wajen ci gaban al’umma?

A kasar nan kusan lokacin da aka ce an fito da tsarin rage talauci da hana zaman banza, ai wannan aiki namu ne tuntuni, mu muke rage talauci da hana zaman banza, shekara da shekaru illa iyaka ita Gwamnati bata san da hakan ba, saboda mu ba yan banbadanci bane, duk mutuminda yake da sana’a bai iya banbadanci ba, saboda haka ita Gwamnati kamar bata san me mukeyi ba.
Dalilinda yasa nake gaya maka haka a wancan lokacin a baya zakaga wasu mutane in sunje makaranta ko iyayensu basu da kudinda biya musu makaranta ko sun kasa karatun sai kaji ance a kaishi ko wajen makanikai ya koyi aiki. Yanzu kuma makanikanci ya koma cikin ilimi saboda yanzu in bakada ilimin kanikancin bazai yiwu ba. Saboda motocin yanzu ba irin nada bane, motocine wanda ake amfani da Kwanfuta wajen nemo motalolinsu wanda ake kiran wannan gyara “Mechatronic”wanda wannan kwanfuta zakasa a jikin mota a gano abin da ke damunta.
Kamar a nan Kano a lokacin Gwamnatin Kwankwaso ya bada horo ga mutanenmu samada 1000 a yanzu Gwamnatin Ganduje akwai mutane da aka tura kamfanin Fijo suna koyon aikin kanikanci na zamani. Gwamnati yanzu ta fuskanci cewa lallai akwai muhimmanci a nemawa mutane aikin hannu wanda yana daga cikin abin da ya kamata a dogara dashi. Mu kuma bangaremmu kaga babban wurine kaga akwai me gyaran mota wanda ake ce masa bakanike ga me tada komada “Panel bitting”ga me penti, ga mai gyaran taya ga mai gyaran iyakwandishin ga mai gyaran kujera ga mai gyaran batir da waya da walda da”Iron bender”masu lankwasa karafuna su gyarasu ayi wani bodin dashi duk wadannan suna karkashin wannan kungiya ta makanikai. Wannan fanni ba karamin wuri bane saboda yanzu muna da samada mutane masu rijista da NATA samada Miliyan Biyar a kasa gaba daya sai kuma wadanda suke cin albarkacin kungiyar basu kai gayin rijista ba tukum a takaice kana maganar mutane Miliyan 15 koda kuwa kuwa wani yara Biyarne dashi a wajensa bare kuma ba wani gareji da zaka samu ace yanada kasada mutum Biyar saidai daga biyar zuwa 10 akwai garejinda zaka samu mutum sanada 20 zuwa 30. Mu aikinda muke bayarwa a matsayimmu na Kanikawa zakaga cewa abin ba karami bane. kuma abu ne da yake bukatar ita Gwamnati ta shigo saboda a taimaka.
Ana maganar habaka noma mutane su dogara da kansu, wadannan sana’oi sunada kyau domin dogaro dakai zakaga akwa sana’oi da yawa, bama kamar munan hausa fulani da ake cewa bamaso mu shiga sana’oi.
Lokacin da na shiga makanikanci mutane wasu har dariya suke min a wancan lokacin wadanda sukeyin dariyar yanzu in sun ganni kuma dana sani suke saboda a wancan lokacin suna ganin kamar sana’ar ta kaskanci ne, ba za su yita ba ni kuma na daure na ci gaba dayi da hakuri abin da yake da farko yanada karshe. Ba abin da zamu yiwa Allah sai godiya kuma muna kira ga Gwamnati su ci gaba da taimaka wa a bamu wuri na dindindin na Kanikawa wanda zai taimaka, na farko a kauda bata gari daga sana’ar saboda duk wanda keyin abin da bai kamata ba, baya son ya ganshi cikin mutane. Na biyu zai sa ita Gwamnati ta sami kudin shiga ba tareda wahala ba, saboda wadanda zata samu a wajensu suna waje daya, dole kowa zai biya. Na uku za a samarwa yara da suke makotaka da wajen gyaran na dindindin damar zuwa su koyi gyara koda makaranta suke zuwa in sun dawo su koya.
Kamar yanzu muna magana suma”graduate”Sunaso a rika turosu suna koyon aikin kanikanci a aikace saboda sunyi karatu kawai, amma idan ka basu aikin a aika ce ba za su iya ba saboda anaso su zo bayan sun koya a karatu su iya a aikace. Ana nan ana maganar da kamfanoni da makarantu lokaci yayi da ya kamata azo a hadu a gudu tare a tsira tare maganar cewa Gwamnati ta baiwa kowa aiki bai taso ba. Sai mun hadu kowa ya bada nashi taimako don kai wa ga nasara.
Ku cigaba da Kasancewa da Muryarhausa24.com domin jin cikakken Karin Bayani a kai.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu
Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Muryarhausa24.com don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum
An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com
Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Muryarhausa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri
Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke
KARIN BAYANI
Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@gmail.com mungode
Allah ka daukaka harshen Hausa dama Kasa baki
daya Amin Summa Amin.
Source by ©Leadership Hausa
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user