Monday 30 April 2018

Karanta Dalilai 13 Da Suka Sa Na Musulunta- Inji Emmanuel Adebayo Dan Kwallon Kafa

Tura Wannan Zuwa Ga
Ya Ce Yana Da Dalilai Kan Yadda Musulmai Suka Fi Yin Imani
Da Annabi Isa (A.S) Fiye Da Mabiya Addinin Kirista.


Dalilai 13 Da Suka Sa Na Musulunta- Inji Emmanuel Adebayo Dan Kwallon Kafa



Ga Dalilan Nasa;

1. Annabi (Jesus) ya bayyana cewa Allah daya ne, kuma shi
kadai ne abin bauta, kamar yadda ya zo a littafin bible (Deut
6:4, Mark 12:29). Su ma Musulmai sun yi imani da hakan a
Alkur’ani (4:171).

2. Annabi Isah A.S, ba ya cin alade, kamar yadda ya zo a bible
(Leviticus 11:7), kamar yadda su ma Musulmai ya zo musu a
Alkur’ani (sura ta 6:145).

3. Annabi Isa ya kan yi amfani da Kalmar "As-salaam alaikum"
wajen gaida mutane (John 20:21), kamar yadda su ma
Musulmai suke yi.

4. Annabi (Jesus) yana amfani da kalmar da yardar Allah
(InshAllah), kamar yadda su Musulmai suke yi a duk al’amuran
da za su yi (Alkur’ani 18:23-24).

5. Annabi Isa (Jesus) yakan yi alwala kafin ya gudanar da
ibada, kamar yadda Musulmai suke yi.

6. Annabi Isa (Jesus) da sauran Annabawa da aka ambaci
sunansu a littafin Bible suna yin sujjada ne a yayin da suke
ibada, kamar yadda ya zo a (Matthew 26:39). Kuma su ma
Musulmai haka suke yi (Qur'an sura ta 3:43.

7. Annabi Isa ya bar gemu, wadda ita ma dabi’a ce ta
Musulmai.

8. Annabi Isah ya yi imani da dukkanin Annabawa kamar yadda
ya zo a (Matthew 5:17). Su ma kuma Musulmai sun yi imani
da Annabawa kamar yadda ya zo a (Qur'an sura ta 3:84, da
2:285.

9.Mahaifiyar Annabi Isa, Nana Maryam, ta kan rufe jikinta da
wadatattun kaya tare da sanya hijabi kamar yadda ya zo a
surori daban daban a bible (Timothy 2:9, Genesis 24:64-65, da
Corinthians 11:6). Haka su ma matan Musulmai irin shigar da
suke yi kenan kamar yadda yake a Alkur’ani sura ta 33:59.

10. Annabi Isah da sauran Annabawan da aka ambanci
sunansu a Bible sun yi zumi na sama da kwanaki 40, ku duba
(Exodus 34:28, Daniel 10:2-6, 1 Kings 19:8, da Matthew 4:1.
Sai ga shi su ma Musulmai an umarce su da azumtar kwanaki
talatin na watan Ramadan. (Ku duba Qur'an 2:183), baya ga
haka kuma wasu sukan yi azumin kwanaki shidda, wato sitta
Shawwal bayan Ramadan.

11. Annabi Isa ya kan yi sallama idan zai shiga gida, kamar
yadda ya zo a bible (Luke 10:5, sannan kuma ya kan yi wa
jama’ar da ya tarar a gidan sallama. Haka su ma Musulmai
suna yin daidai yadda ya yi, kamar yadda ya zo a Kur’ani
(24;61).

Yanzu sai a fada min wanene cikakken mai bin Annabi Isa
tsakanin Musulmi Da Kirista? Yanzu na yi imani cewa ina kan
addinin gaskiya, Inji Emmanuel Adebayo, wanda ya buga wasa
a kungiyoyi irin su Real Madrid, Arsenal, Monaco, Man City da
sauransu.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: www.MuryarHausa24.com.ng


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user