Monday 30 April 2018

Karanta Yanzu Kaji: Zan Sake Cin Zabe A 2019 Saboda Ni Tsarkakakke Ne Ba Maciyin Rashawa Ba Ne Kamar Sauran Shugabannin Nigeria Da Suka Gabata- Cewar Shugaba Muhammadu Buhari

Tura Wannan Zuwa Ga

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa zai sake
tsayawa takara a karo na biyu a zaben 2019 kuma zai sake ci
saboda shi tsarkakakken mutum ne kuma ba maciyin rashawa
ba ne kamar sauran shugabannin Nijeriya da suka gabata.

Shugaba Buhari wanda ya bayyana hakan a ziyarar kwanaki
biyu da ya kai jihar Bauchi, ya kara da cewa da yawa daga cikin
shugabannin Nijeriya da suka gabata sun wawushe dukiyar
kasa kuma sun mallaki gidaje sama da 20 ko 30, yayin da
akasarin 'yan Nijeriya ko daki daya da za su kwana a ciki ba su
mallaka ba saboda talauci.

"Zan sake neman takarar shugaban kasa kuma zan ci saboda
ba a ta taba nema da laifin wawushe dukiyar kasa ba.

"Na rike mukamin shugaban kasa, na yi gwamna, na rike
shugabancin PTF, amma ban saci dukiyar kasa ba kamar yadda
shugabannin Nijeriya da suka gabata suka yi, wadanda suka
mallaki gidaje sama da 20 ko 30 yayin da talakawa ko daki
daya wasu ba su mallaka ba saboda tsananin talauci", inji
shugaba Buhari.

Source by ©Rariya

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: