Monday 30 April 2018

Karanta Kaji: Nayi Alkawari Zan Binciki Shugaban Kasa Buhari Idan Na Ci Zaben Shugaban Kasa A 2019- Atiku Abubakar

Tura Wannan Zuwa

Tsohon mataimakin shugaban kasa
Alhaji Atiku Abubakar, kuma mai
neman tsayawa takaran
shugabancin kasa karkashin
jam'iyyar PDP a shekarar 2019 ya ce
zai gudanar da bincike a kan cinikin
makamai da gwamnatin shugaba
Buhari take saya.

A wata hira da ya yi da gidan
rediyon BBC Hausa a yau Asabar,
turakin Adamawan yace an dauki
lokaci mai tsawo ana ta artabu da
yan kungiyar ta Boko Haram amma
har yanzu ba'a kawo karshen
matsalar ba.

An kwashe shekaru takwas ana yaki
da yan kungiyar Boko Haram duk da
cewa basu da wani cikakken horo
na musamman," inji shi.

"Ina son zama shugaban kasar
Najeriya, saboda akwai wasu
abubuwa da nake da niyyar
aiwatarwa amma ban samu dama
ba lokacin da nake mataimakin
shugaban kasa a Najeriya, zan
kuma binciki yadda gwamnati ta
gaza kawo karshen rikicin Boko
Haram na tsawon shekaru, zan
kuma binciki batun siyan makamai
da wannan gwamnatin ta sayo."

Bugu da kari, Atiku ya ce zai
magance cin hanci da rashawa inda
ya zargi gwamnatin shugaba Buhari
da kare wasu mutane wadanda ya
kamata su fuskanci shari'a.

idan yan Najeriya basu manta ba,
gwamnatin mu ne ta kafa hukumar
yaki da rashawa (EFCC), kuma nine
na samar da kudaden da hukumae
EFCC ta fara amfani dashi bayan
kafa ta.

Source by ©Hausa Naija

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: