Friday 20 April 2018

HOTUNA DA CIKAKKEN TARIHIN JARUMA MARYAM YAHAYA: ABUBUWAN DA BAKU SANI BA GAME DA JARUMA MARYAM YAHAYA

Tura Wannan Zuwa

Ga duk mai bibiyar harkokin masana’antar shirya finafinan
Hausa watau Kannywood, ya kwana da sanin bullar sabuwar
jaruma Maryam Yahaya (Mansoor), wadda za a iya cewa ta
shigo farfajiyar fim da kafar dama, kasancewar ta zamo cikin
jerin taurarun da ake sa ran za su haska nan da shekaru
masu zuwa.

Akwai mamaki matuka yadda cikin lokaci kankani jarumar ta
yi wa takwarorinta fintikau wajen yawan fitowa a finafinai
masu kyawun gaske, ko da yake ba abin mamaki ba ne idan
aka yi la’akari da kamfanin FKD Production da ya tsaya
tsayin daka wajen yi mata babban fim watau MANSOOR,
wanda za a saki a satin karamar Sallah a sinimun da ke fadin
kasar nan, ranar 30 ga watan Yuni 2017.
Maryam, ‘yar asalin Jihar Kano, ta shimfida kwarewarta a
farfajiyar, gwana ce ta gwanaye, wadda take yin kyau da
zarar an dora mata kyamara. Wani karin armashi game da ita
shi ne, yadda ba ta wasa da aikinta a matsayin jaruma.


Bajintar da ta nuna a fim din, MANSOOR, duk da cewa ba shi
fim na farko da ta fara fitowa ba, amma an ga yadda
tauraruwarta ta haska (wanda aka gani tun kafin fim din ya
fita) shi ne ya janyo mata farin jinin tun kafin ya fita. Tallansa
kawai jama’a suka gani, amma suka tabbatar da cewar
Maryam Yahaya za ta yi abun kirki a masana’antar fim.
Tun daga nan manyan furodusoshi suka fara nuna ra’ayinsu
na sanya ta a finafinansu, kafin ka ce kwabo jarumar ta kai
matsayin da take a yau, na zamowa cikin jerin manyan
jaruman da Kannywood ke alfahari da su.
Cikin shekara daya kacal da fara yin fim, jarumar ta zamo
tauraruwar da kowane lungu da sako ake labarinta.

Gwana
ce wajen iya aktin, musamman da ta kasance tana iya taka
kowace irin rawa da aka dora ta matukar ba za a wuce gona
da iri ba.
Masana’antar Kannywood ta dade ba ta samu jaruma da
cikin lokacin kankani ta shige sahun takwarorinta ba, domin
an saba ganin yadda wasu jaruman ke daukar shekaru kafin
‘yan kallo su gamsu cewar kwararru ne, balle har manyan
furodusoshi su rika aiki da su a kai a kai.
Sai dai masana na ganin tagomashin da ta samu na horo
daga wurin maigidanta jarumi Ali Nuhu, shi ne
ummul’aba’isin kasancewarta kwararriya a masana’antar
Kannywood.

Babban abin da yake kara mata farin jinni tsakanin abokan
sana’arta shi ne girmama na gaba, karamci, mutunci da
sanin girma mutane.
Har ila yau, jarumar ta dan yi tsokaci kadan game da
abubuwan da ta fuskanta daga gida kafin a amince mata ta
fara harkar fim.
“Dole ne duk wanda ya samu kansa a wannan hali zai iya
samun matsala, musamman a gidansu za a ji irin ba dadi din
nan. Amma daga karshe ina nuna masu harkar fim sana’a ce
tamkar kowane irin aiki, lokacin da kake bakin aiki magana a
waya ma jarumi ba shi da damar yi balle ya samu damar
zuwa yawo.


“Kuma ina son mutane su sani, fim sana’a ce kuma ko wace
masana’anta akwai nagari akwai kuma na banza. Idan ka
tsare kanka Allah Zai taimake ka, saboda kai dai ka san me
ka je yi, idan ka je iskanci ne kai ka sani, idan ma ka je a
wulakance ne kai ka sani idan kuma ka je da mutuncinka
Allah zai kare maka mutuncinka.” A cewar Maryam.

Jaruma Maryam Yahaya ta ciri tuta, ta kafa tarihi a
masana’antar Kannywood, ta zamo gwana da ta ta yi
bajintar a zo a gani cikin kankanin lokaci, alamu sun nuna
matukar jarumar ta dage kan kadamin da ta taho a kai, babu
shakka nan da wani lokaci za ta shiga sahun manyan jarumai
mata da duniyar fim ke labari.
Cikar jaruma shi ne yin abin da darakta yake so, a lokacin da
yake so. Haka zalika rawar da jaruma kan taka fim kan zamo
wani siradi na sirrin nasararta. Batun kyau da cikar zati kuwa
na karawa jaruma kwarjini a idanun ‘yan kallo, ta yadda idan
ba jarumar da suke so suka gani a fim ba, bai cika birge su
ba.

Finafinan da ta fito ciki sun hada da: Tabo, Mijin Yarinya,
‘Yar Mai Ganye, Duhun So, da Arashi.
Ta samu magoya baya da yawa a shafukan sada zumunta,
musamman Instagram, inda take amfani da @MaryamYahya.

Source by ©Leadership A Yau and Muryarhausa24.com

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user