Friday 20 April 2018

Karanta Kaji: Dukkanin wani Mabiyi Na Ya Fito Ya Yanki Katin Zabe Domin Kwatar ‘Yancinsa – Shaikh Dahiru Bauchi

Tura Wannan Zuwa

Babban Malamin darikar Tijjaniyyar a Nijeriya, Sheikh Dahiru
Usman Bauchi ya yi karin haske kan kiran da yake yi wa
mabiyansa na su fito kansu da kwarkwatansu wajen yankan
katin zabe na dindindin domin takadarwa don yin amfani da
wannan katin a zaben da ke tafe don aza nagartaccen
mutumin da suka ga ya dace kuma zai yi musu aiyukan da
suka kamata.

Shehu Dahiru Bauchi, wanda ya yi wannan karin hasken a
hirarsa da manema labaru a gidansa da ke Bauchi a ranar
Talatar nan, yana mai cewa, Nijeriya kasa ce wacce kowa na
da ikon yin zaben da ya dace da shi domin kafa wanda zai
biya masa dukkanin bukatunsa ta hanyar shugabanci.

Ya bayyana cewar ta wannan hanyar ne kadai dan Nijeriya
zai iya yakar wanda bai so kuma cikin sauki domin a
cewarsa zabar shugaba na gari tamkar bayar da dama ce
wajen wanzar da shugabanci na gari, don haka ne ya umurci
mabiyansa da cewa; “Dukkanin mutanenmu su fito su yanki
katin zabe,” a ta bakinsa.

Shehi ya bayyana cewar kasar Nijeriya kasar su ce don haka
suna da hakkin fitowa domin neman wanda suke so, hade da
dabar mutumin da suka tabbatar zai yi musu aiyukan da
suka zabe sa don su.

Ta bakinsa yake cewa Nijeriya musulmi da kirista kowa na
da zarafin zabin da yake so ta fuskacin shugabanci, “Ai kasar
Nijeriya ta musulmi ne da wanda ba musulmi ba; waye zai
yadar da hakkinsa? Wani dai ba zai yada hakkinsa ba. tun da
abun ya zama yakin da ‘yar karamar takarda ake yi bada
makami ba; ai ya yi sauki, ka je ka jefa kuri’ar ka zabi wanda
zai mallakeka wanda kuma kake ganin alamar zai biya maka
bukatarka a zamanka na dan kasa,” In ji Dahiru Bauchi.

Bauchi ya daura kuma da cewa kuri’ar mutum makaminsa
ce, domin da kuri’a mutum ka iya kashe kansa ko ya yanka
kansa, don haka ne ya bukaci kowa ya yi amfani da wannan
makamin tasa wajen zabar na gari, “Wai wasu ‘yan siyasa
suna cewa kuri’arka-‘yancinka. Ni kuma ba haka nake cewa
ba. ni ba dan siyasa bane, amma abun da na ke cewa, shi ne
kuri’arka makaminka, wukarka ka bai wa wanda zai yanka ka
ko kuma wanda zai yanka maka.
“Masoyinka wanda yake sonka zai yanka maka in ka bashi
kuri’arka zai yanka maka, makiyinka ko kuma masoyinka na
suna idan ka ba shi wannan kuri’ar to soyaka zai yi kuma ya
yanka ka. Soboda haka ka san fuskokin mutune tun daga
farko, ka san masoyinka ka san makiyinka. Dukkaninmu ‘yan
Nijeriya mun san masoyanmu da kuma makiyanmu, mun san
su, sai in lokacin kada kuri’ar idan ya kammala yi sai mu
kada ma wanda muke so,” in ji Shi.

Daga bisani ya kuma nemi dukkanin wani dan Nijeriya da ya
fito fagen zabe domin zabar na gari a kowani lokaci.
Da ya juya kan shuwagabanin kuwa, Shehu Dahiru Bauchi ya
gargadi shugabanni kan wadanda suke shugabanta domin a
cewarsa kowani shugaba ya dace ne ya tabbatar da cika
alkawuran da ya yi wa jama’arsa a lokacin yakin neman zabe
“Ainuhin abun da ake nufi da gwamnati musamman
gwamnatin siyasa, jama’a ne idan suna da wasu abubuwan
da ba za su iya samu ba sai su nemi gwamnati ta hanyar
siyasa, su kuma ‘yan siyasa za su nemi yin aiyukan da za su
kare mutane daga sharri da kuma samar musu da alherin da
suke bukata. in an zabi gwamnati ba ta kawo alheri ba sai
sharri, ba ta ture sharri ba sai alheri ta ture wannan ai ba
gwamnati bace, a don haka ne muke jawo hankulan mutane
su yi karatun ta nutsu,”.

Ya bayyana cewar duk wanda ya fito gaban jama’a aka kada
masa kuri’a ya ci ya kamata ya yi dukkanin mai iyuwa domin
rage wa jama’ansa matsatsin da suke ciki “Ana wahala don
haka muna kira ga gwamnati ta yi duk mai iyuwa domin rage
wa jama’a halalhalun da suke ciki domin a samu gudunar da
shuganci yadda ya dace,” kamar yadda ya ce.

Source by ©Leadership A Yau

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user