Friday 20 April 2018

KARANTA KAJI: MATASAN KASAR NIGERIA MALALATA NE KUMA YAWANCIN SU JAHILAI NE- Muhammadu Buhari

Tura Wannan Zuwa Ga

Shugaba Muhammadu Buhari ya soki
matasan Najeriya, wadanda ya kira
sangartattu, saboda dabi’ar su ta jiran
tsammanin samun abu ba tare da sun tashi
sun ci gumin kan su ba.

“Sama da kashi 60 cikin 100 na yawan
al’ummar Najeriya duk matasa ne ‘yan kasa
da shekaru 30, kuma da yawan su ba su je
makaranta sun nemi ilmi ba, kawai su na
ikirarin cewa Najeriya kasa ce mai arzikin
man fetur. Saboda haka, sai su zauna a
sangarce su na jiran su samu gidajen zama,
kula da lafiya da kuma ilmi duk a kyauta.”

Haka jaridar The Cable ta ruwaito shi ya na
furtawa a lokacin da ya ke jawabi ga taron
Shugabannin Duniya a Taron Tattauna
Kasuwanci da Tattalin Arziki a Landan,
ranar Laraba.

Dama kuma cikin watan Fabrairu, 2016,
Buhari a wata tattaunawa da ya yi da
jaridar Telegraph, ya ce wasu ‘yan Najeriya
mazauna Ingila, musamman matasa, duk
sun karkata ne wajen aikata munanan
laifuka don haka bai cancanta Ingila ta rika
ba su mafaka su zauna ba.

Daga jiya zuwa yanzu dai gaba daya kasar
nan, duk jama’a sun karkata ne wajen
jinjina wannan furuci na Buhari, wanda da
dama ke cewa bai kamata ma, kuma
kasassaba ce shugaba ya fita waje ya na
aibata kasar sa.

A farkon wannan shekara ne wani bincike
da sharhi da Jami’ar Rice ta gudanar a
Amerika, ya tabbatar da cewa ‘yan Najeriya
bakin da suka fi dukkan sauran baki daga
kowace kasa ilmi.

Bidiyon furucin da Buhari ya yi a Landan ya
na ta yawo a soshiyal midiya, inda matasa a
fadin kasar nan, musamman a Arewa ake ta
yin tir da kalamin.

Buhari ya ce, 'Da damansu ba su suyi makaranta ba, sannan
suna cewa ai Najeriya kasa ce mai albarkar mai, don haka
suna zaune ba sa komai suna jira gwamnati ta samar musu
ilimi, da gida, da kula da lafiya kyauta'.

Shugaba Buhari yana magana ne a taron kasashen renon Ingila
dake gudana a birnin Landan.

Sai dai kalaman sa na ci gaba da tayar da kura a tsakanin
matasan kasar musamman a kafafen sada zumunta na
zamani.

Matasa da dama dai sun nuna damuwarsu kan kalaman da
suka ce na zubar da kima ne.

Ra'ayoyin Wasu Kenan:

This statement is causing a lot of backlash. No one
supported the President more then the youths
(educated & uneducated). He shouldn’t be making such
statements in an international conference. He should
have used the opportunity to highlight the good things
the youths are doing. https://t.co/WPdOEHcIDx

— Dr. Aminu Gamawa (@aminugamawa) 18 Afirilu, 2018

Yusuf BUHARI is very very very very lazy, yet he bought
OKADA for 112million naira and he got the best
treatment outside the country on our bills.
RT if you are a youth and not lazy.
— BOLANLE 🇳🇬 (@bolaNLee_c) 19 Afirilu, 2018
Very true....some Nigerian youths are lazy. I back
Buhari's claims. Only the courageous say the truth.
Only the strong accept it.
Deal with it ......

— Ibrahim Ijaola (@ijaola_ibrahim) 19 Afirilu, 2018

Buhari did not say Nigerian youth are lazy. But a bulk of
lazy Nigerian youth, wearing a toga of laziness that was
not necessarily ascribed to them, have failed to find out
exactly what the President said.
Guilty of a crime you confessed to, even when you were
not accused?

— Dr. Thompson Udenwa (@TomUdenwa) 19 Afirilu,
2018

Wannan batu dai na daga cikin abubuwan da suka fi daukar
hankalin matasan kasar, musamman ma da ya ke Shugaba
Buhari ya fi farin jini a wajen matasa a sama da masu shekaru
da yawa.

To sai dai duk da haka akwai wasu matasan da suke ganin
babu aibu a maganar shugaban, domin kuwa bai hada
matasan ya yi musu kudin goro ba, ya dai ce da dama daga
cikinsu ne suka da wannan matsala.

Haka kuma wasu na da ra'ayin cewa gaskiya ce zalla
shugaban ya fada, don haka babu wani abin tada jijiyar wuya.

Source by ©Premium Times Hausa and BBC HAUSA

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user