Sunday 29 April 2018

Kalli Hoton Musulma ta farko me saka Hijabi zata zama sarauniyar kyau a kasar Ingila

Tura Wannan Zuwa

Musulma 'yar kaaar Ingila me suna Maria Mahmood na kan
hanyar zama sarauniyar kyau ta kasar Ingilar ta farko dake
sanya hijabi, Maria dai ta wuce mataki na biyu na
tantancewa a gasar kamar yansa jaridar Mirror ta kasar
Ingilar ta ruwaito kuma itace musulma ta farko me sanya
hijabi da ta taba shiga gasar.

A shekarun baya akwai musulmar da ta taba zama sarauniyar
kyau ta kasar Ingilar amma bata sanya Hijabi, Maria ta
bayyana cewa iyayenta da abokanta da kungiyoyin addinin
musuluncine suka dauki nauyinta kuma tana kokarin zama
sarauniyar kyan kasar ta Ingilane dan ta kawar da irin kallon
da akewa musulmai na cewa sunfi kwarewa a harkar
ta'addanci da kuma ta kara karfafawa 'yan mata Musulami
gwiwa akan cimma burinsu na rayuwa.

Tace duk da yake akwai masu ra'ayin 'yan mazan jiya dake
sukar wannan abu da takeyi amma masu yabonta sunfi yawa
dan haka zata cigaba.

A yanzu dai za'a ci gaba da wannan gasa ta sarauniyar kyau
ta kasar Ingilar wadda mataki na gaba shine sanya rigar
mama da pant kawai da 'yan mayan zasuyi dan aci gaba da
tantancesu, amma Maria, 'yar shekaru ashirin tace ita ba
zata saka irin wadancan kaya ba dan sun sabawa koyarwar
addininta, zata ci gaba da saka hijabi da kayan mutunci.

Idan dai Maria taci gasar ta sarauniyar kyau ta kasar Ingilar
itace zata wakilci kasar a gasar sarauniyar kyau ta Duniya,
muna mata fatan Alheri.

Source by ©Hutu Dole

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: