Sunday 29 April 2018

Karanta Kaji: Yayi Niyyar Komawa Cikin Addinin Musulunci matar shi ta hanashi ko me ye mafita???

Tura Wannan Zuwa Ga

Wani mutum mai shekaru 37 a duniya, Idris Afegbua, ya sanar
da wata kotun customary a garin Abeokuta yanda matarshi ta
daka tsalle tace bata yarda da komawarshi zuwa addinin
Islama ba, wanda ya kawo husumar da suka kasa sasantawa
tsakanin su.

Afegbua wanda ya tunkari kotun don ta raba auren shi da
Omolola na shekara biyu, yace dukkaninsu mabiya addinin
kirista ne kafin ya koma addinin Islama.
Yace a halin da ake ciki ya rufe idon shi yaki komawa addinin
kirista, wanda yayi sanadiyyar rashin zaman lafiyarsu.

"Dukkan mu mabiya catolika ne kafin in musulunta. Mun hadu
ne a 2016 ta hadin gida. Bayan na musulunta duk kokarina na
ganin mu daura auren musulunci ya tashi a banza. Koyaushe
fada mukeyi." yace.
Omolola bata samu ta halarci zaman kotun ba a jiya, a inda
kotun tace Omolola ta kasa fuskantar kotun.

Chief Akande shugaban kotun ya ba ma Afegbua damar raba
auren a inda yasa Mista Adesina, kilakin kotun da ya ba wa
Afegbua rantsuwa.

Source by ©Hausa Naija

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: