Saturday 14 April 2018

Karanta Kaji: Babban Dalilin da ya sa zan je Mauludin Nyass na Abuja – Sheikh dahiru Bauchi

Tura Wannan Zuwa

Fitaccen Malamin Musuluncin nan kuma jigo a darikar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh dahiru Usman Bauchi ya ce Maulidin Sheikh Ibrahim Nyass na kasa da ake yi shekara-shekara a bana za a yi a Kaduna ne da Abuja.

Manema labarai sun tambayi Shehin kan dalilin da ya sa za a yi haka, ya amsa tambayar da wasu daban kamar haka:

Mene ne makasudin yin wannan Maulidi?

Farko dai dalilin da ya sa muke yin wannan Maulidi, Ubangiji ne Ya yi umarni cewa ku gode wa ni’imar Allah idan Ya yi muku, in ya zamo kuna kadaita Allah kuna bauta maSa. Saboda haka babbar ni’ima da halitta ta samu babu kamar samun Annabi Muhammadu (SAW), saboda haka muke taron Maulidinsa don mu gode wa Allah da samun wannan babbar rahama ta Annabi (SAW). Manzon Allah (SAW) yana da magada da suke rike da tutarsa suke kiran mutane zuwa ga addinin Musulunci, su ne manyan waliyyai saboda haka mu da muka shiga darikar Tijjaniyya idan lokacin haihuwarsu ya zo kamar yadda muke Maulidin Annabi (SAW), in 13 ga watan Safar in ya zo sai mu taru mu gode wa Allah da samun ni’imar da ya ba mu ta Shehu Tijjani (RA), Allah Ya samar mana da shi a cikin rayuwarmu samunsa cikin rayuwarmu don ya amfane mu ya amfani rayuwarmu sannan Shehu Tijjani na da Babban Khalifansa shi ne Shehu Ibrahim Nyass (RA) cikin darikar tamu shi kuma wanda aka haifa ranar 15 ga watan Rajab, in wannan lokaci ya sake dawowa sai mu tuna ni’imar da Allah Ya yi mana ta samun wannan babban bawa naSa Shehu Ibrahim, mu taru mu gode wa Allah a cikin wannan lokaci. Maulidi ma’anarsa wurin haihuwa, Maulidi ma’anarsa lokacin haihuwa, wurin haihuwa na Annabi Muhammadu saboda haka aka wajabta aikin Hajji a cikin rukunan Musulunci domin mutane su je su yi aikin Hajji wato Maulidin Annabi (SAW) na wurin, shi kuma Shehu Tijjani Aljeriya ne wurin da aka haife shi, shikuma Shehu Ibrahim Maulidinsa na Senegal.

Akwai bayanan da ke cewa bana ba a wuri daya za a yi Maulidin ba, yaya lamarin yake?

Wato Maulidin da za a yi bana ya samu wani irin salo ne. Da farko mutanen Jihar Taraba sun nuna sha’awar a yi a wurinsu. Na ce a’a bai kamata a yi Maulidi a wurinsu ba saboda irin bala’in da Allah Ya dora musu na kashe-kashen mutane da dabbobinsu, bai kamata a yi wani biki a Taraba ba, sai muka daga sai mutanen Kaduna suka ce suna so a yi musu Maulidin nan, sai muka karba to muna cikin wannan hali sai mutane suka kawo shawara da hujjoji gamsassu suka ce su sun fi so a yi wannan maulidi a hedkwatar Najeriya, Abuja. Sai muka amsa muna cikin wannan sai mutanenmu na Kaulaha shi ainihin Khalifanmu na Kaulaha, magajin Shehun, Shehu Tijjani (RA) bai tilasta a yi a Kaduna ko Abuja ba. Ana nan ana cikin wannan hali, sai abin ya zama kamar Shehun ne yake so ya nuna bunkasarsa cewa yana so a yi Maulidin fiye da na kullum, tunda na kullum akan hada kai a yi a wuri daya, na bana kuwa akwai wadansu samari da suka sa wani abu da ba a jin dadinsa, kuma lamarin ba na yara ba ne, ba na samari ba ne a’a lamari ne na Khalifofin Shehu da Khalifan Shehu, ba yadda za a yi wani almajirin Shehu ya yi jayayya da Khalifan Shehu na Kaulaha, abu ne da ba zai yiwu ba. Don mu shi abin girmamawa ne a wajenmu, dan Shehu wanda ya zama Khalifa mu abin girmamawa ne a gare mu ba abin jayayya ba ne, saboda haka har yanzu dai wadansu suna cewa za a yi a Abuja wadansu suna cewa za a yi a Kaduna. Tunda abin namu ba na jayayya ba ne, ba na gaba ba ne, kafin lokacin ya iso dai za mu san yadda za mu yi, tunda abin na bayyana soyayya ga Shehu Ibrahim ne. Shi abu duk in za a yi shi saboda Allah an huta wahala, tunda Allah Yana ganin zuciyar kowa Yana ganin niyyar kowa. Idan wani yana so ya shigar da wani abu na baci cikin wannan al’amari to Allah ba zai yarda ba, sai abin ya zama alheri a gare mu baki daya.

A yanzu a ina ke nan aka ajiye wajen Maulidin?

Kamar yadda na fada muku da farko Shehu Ibrahim namu bana yana so ya nuna kasaita kamar wuri dayan ba zai yi ba ne sai ya zamo ana ja wadansu suna cewa Abuja wadansu suna cewa Kaduna. Saboda haka mu dai in Allah Ya yarda za mu je Abuja ne. Amma da Abujan da Kadunan duk daya ne muna tare da su, insha Allahu zikiri za a yi shi ne a Abuja Babban Masallacin kasa, kuma muna sa ran ’ya’yan Shehu za su zo mana da yawa wadansu a Abuja wadansu a Kaduna.

Shehu wannan ba zai jawo rarrabuwar kai ba?

A’a babu wani rabuwar kai, ’yan uwanmu ne,da mu da su duka daya ne, suna lazimi suna wazifa suna zikirin Juma’a, mu ma muna yi, kuma wadannan su ne darikar. Kuma su mutanen Manzon Allah ne (SAW), mutanen Shehu Tijjani ne (RTA), mutanen Shehu Ibrahim ne (RTA). Don haka muna nan tare Allah Ya sa a yi taro lafiya a tashi lafiya kowa ya koma gida lafiya alfarmar Ma’aiki (SAW).

Akramakallahu yaya za a yi wannan taro ganin cewayan darika suna da yawa?

Ai kamar yadda yake a kullum haka lamarin yake, kuma haka zai kasance in Allah Ya so, an nemi izinin hukuma na wajen da za a yi taron da yadda za a samar da tsaro na rayuka da dukiyoyin jama’a a lokacin taron.

Wace gudunmawa jama’a za su iya bayarwa ganin jama’a da yawa za su zo?

Gudunmawa ta farko dai a nuna musu soyayya saboda taron na soyayyar masoyin Annabi (SAW) shi ne Shehu Ibrahim (RA), kuma jama’a su karbi bakin namu hannu bibbiyu a taimake su da duk abin da ya kamata a taimake su da shi.

Daga ina ne ake saran bakin za su zo?

Muna da manyan bakinmu daga Senegal da Moroko da Kamaru da Aljeriya da Ghana da Nijar da Chadi muna da baki daga kasashen makwabta da kasashen da suke nesa.

Wane kira za ka yi ga jama’a?

Jama’a gaba daya muna kira gare su da su ji tsoronAllah a zauna lafiya dukan alheri sai an ji tsoron Allah ake samunsa dukan sharri sai an ki jin tsoron Allah ake gamuwa da shi. Saboda haka muke kira ga jama’a a ji tsoron Allah a zauna lafiya. Dukanmu al’ummar Musulmi Allah Ya hore mu da mu rike igiyar Allah gaba daya kada mu rarraba mu karfafi juna da soyayya, sannan makwabtanmu wadanda ba Musulmi ba mu nuna musu halin kirki, wanda muka gada na Musulunci domin su gani idan aka nuna musu ya zama kamar talla muka yi musu na Musulunci, musamman wadanda suke rike da addinin Annabi Isa (AS), su ne manyan mutane wadannda ba sa cikin Musulunci kuma ake tare da su, su kuma su nuna mana halin Annabi Isa (AS) halinsa na zama lafiya tunda addininsa addinin tausayi ne mu kuma Musulunci addininmu addinin zama lafiya ne.

Saboda haka mai addini tausayi har abada ba zai yi fada da mai addinin zama lafiya ba. Mai addinin zama lafiya har abada ba zai yi fada da mai addinin tausayi ba saboda haka kowa a kiyaye masa hakkinsa a martaba masa addininsa don a samu zaman lafiya.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Muryarhausa24.com don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum

An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com
Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Muryarhausa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki
daya Amin Summa Amin.

Source by ©Aminiya

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: