Wednesday 4 April 2018

Karanta Kaji: Kuskure 10 da akayi a fim din Korarriya cigaban Ankon biki tare da Sharhin fim din

Tura Wannan Zuwa

Suna: Korarriya
Tsara labari: Auwal M
Sarki
Furodusa: Muhammadu
Mia
Bada umarni: Ali Gumzak
Kamfani: Mia Enterprises
Jarumai: Aminu Sharif
Momo, Fati Shu’uma,
Sadiya Kabala, Hadiza
Muh’d, Malam Inuwa,
Nasir Naba, Malam
Haruna, Baba Saugiji,
Sayyid Ali Muh’d da
Rahma MK .
SharhiN: Saddika Habib
Abba

A farkon fim din an nuna
Yahaya(Al’amin Buhari)
yana korar ‘yarsa Fa’iza
(Sadiya Kabala) daga
gidansa sakamakon dakko
masa abin kunya da ta yi a
ranar daurin aurenta aka
zo da hoton bidiyo na
lalata da ta yi hakan tasa
ya yi fushin zuciya yaki
saurarar duk wasu masu
bashi hakuri hatta
mahaifiyar Fa’izar Talatu
(Hadiza Muh’d)

A lokacin Fa’iza ta saka
kafa ta shiga duniya
sakamon korarta da
mahaifinta ya yi, ta fara
da shiga garin Zariya gurin
wata shaharrariyar
karuwa Zee Ta Kowa(Fati
Shu’uma) domin ta kara
bunkasa kwarewarta a
bariki zaman su da Zee Ta
Kowa yaki da di
sakamakon ita Fa’iza
tsayyayiyar yarinya ce
kuma mara kunya tana ji
da kanta domin babu
wanda ya isa ya lankwasa
ta kuma ta yi masa
biyyaya saboda ita asali ba
karuwa bace kaddarace ta
fito da ita. ita kuma Zee Ta
Kowa tunda shugaba ce a
wajen dole kowa ya yi
mata biyyaya sakamakon
kin wannan biyyaya da
Fa’iza ta yi mata ta sanya
suka rabu baran baran
Fa’iza ta kama gabanta
daga nan ta tafi ta hadu da
wani shaharran dan
duniya mai suna Dan
Agulla(Aminu Sharif
Momo) suka ta fi suka bar
Zariya suka wuce Kaduna
suka fara sheka ayarsu,
Dan Agulla direban mota
ne yana da uban gida
wanda suke gudanarda
harkokinsu tare mai suna
Alh. Maina wanda shi
wannan Alhajin shine ya
fara lalata rayuwar Fa’iza
a baya sakamakon sunje
gurinsa ita da kawarta
domin ya basu hayar hall
din bikin Fa’izar da za’ayi
domin sun gayyaci
kawayensu basa son suji
kunya shi wannan Alhaji
Maina ya yanka musu kudi
mai tsada wanda za su
kasa biya, ta hanyar daya
samu dama ya bullowa da
Fa’iza bukatarsa kenan ta
fasinkanci da sharadin
cewar idan ta amince zai
bata hall din kyauta Fa’iza
ta ki Amincewa a lokacin
wata kwararriyar karuwa
kawar Fa’iza mai suna
Bintu (Hafsat Idris) ta
tursa sa Fa’iza ta ribace ta
har ta amincewa
Alh.Maina domin gudun
kada suji kunya shine
hotan bidiyon da aka kawo
gidansu ranar daurin
auren amma kafin haka
Fa’iza kamilalliyar yarinya
ce, bayan Fa’iza sun hadu
da Dan Agulla ranar da ta
fara ganin Alh. Maina a
matsayin shine uban gidan
Dan Agulla abinda ya faru
a baya ta fara tunawa irin
ta’asar da ya yi mata a
baya.

A bangaren gidansu Fa’iza
kuma mahaifinta ya yi
nadamar korar Fa’iza daga
gida da ya yi kuma
mahaifiyarta ta dame shi
da kuka da damuwa
sannan ga mahaifinsa ya
yi fushi da shi kuma ya
kafa masa sharadin cewar
lallai duk in da jikarsa ta
ke yaje ya nemo ta hakan
tasa mahaifin Fa’iza ya
bazama yawon nemanta
gari gari duk inda yaje
baya samunta sakamakon
tana can Kaduna tare da
Dan Agulla suna sheka
ayarsu domin Fa’iza ta sha
alwashin tunda mahaifinta
bai ga kaddarar data
fadamata ba ya kore ta to
ita kuma sai ta dakko
masa abun kunyar da ya fi
na da wato dan shege.

A bangaren kawar Fa’iza
Bintu kuma sun kulle da
Alh.Maina domin dama
tun tuni ita karuwace
bakin cikinta ma shine ya
yi sanadin rasuwar
mahaifiyarta a karshe har
suka sakawa juna cutar
kanjamau kowannensu ya
gane kuskurensa, ita kuma
Fa’iza burinta ya cika ta yi
ciki ta haihu a lokacin ta
koma gida ta kaiwa
mahaifinta dan shege
hankalinsa ya yi matukar
ta shi kuma ya yi nadamar
korar Fa’iza da ya yi a
baya itama Fa’izar ta yi
nadamar abinda ta aikata.

Abubuwan Birgewa:

1- Jaruman sun yi kokari
sosai gurin isar da sakon
musamman Fa’iza da Dan
Agulla.

2- An yi amfani da kayan
aiki masu kyau kamar
camera ta daukar hoto da
kuma Abin daukar sauti da
gida je da suka dace da
labarin.

3- Anyi amfani da salo na
harshe masu kayatarwa
sannan da kwarewa gurin
furtasu wato (dialogue).

Kurakurai:

1- Yakamata a nunawa
mai kallo mijin da Fa’iza
zata aura aka fasa.

2- Yakamata a nuna
makomar Dan Agulla mara
kyau saboda irin barnar
da ya tata saboda darasi.

3- An nuna Fa’iza
kamillaliyar yarinyace a
farkon fim din mai kuma
ya hada su kawance da
Bintu karuwa? kuma har a
gidansu aka bari duk da
sun san ‘yarsu mai
tarbiyyace?

4- Farkon haduwar Fa’iza
da Dan Agulla lokacin da
ya dauketa suka tafi tare
lokacin dare ne daga nan
suka sauka a garin da za
su je da safe maikallo bai
ga Fa’iza da jakar kaya ba
kuma a wannan karamin
lokacin ba’aga sun tsaya
sun siya ba amma sai ga
shi da suka sauka a garin
da za su je da safe an ga
Fa’iza ta canja kaya shin a
ina ta samu?

5- Duk rashin mutuncin
mutum mahaifiya ba wasa
bace babu yanda za’ayi
mutum ya shigo gida ya
tarar mahaifiyarsa ana
kurma ihun ta mutu amma
ya nuna halin ko in kula
kuma yana cikin
hayyacinsa kamar yanda
Bintu ta yi a fim din sam
hakan a gaske abune
wanda bazai faru ba.

6- Shin babban Mutum
kamar Alh.Maina ba shida
iyali ne? yakamata ace an
rarrabewa mai kallo ko da
a baki ne.

7- A lokacin da mahaifin
Fa’iza yana nemanta har
suka hadu a wani waje shi
da ita ta saka nikaf ta rufe
fuskarta kallon da ya yi
mata ido cikin ido babu
yanda za’ayi ace bai gane
ta ba.

8- A gurinda Fa’iza taje ta
sami Bintu a yashe tana
jinya domin ta mayar
mata da martani sai aka ji
Bintu ta nunawa Fa’iza
cewar tasan jiya ta dawo
shin ta yaya Bintu ta san
cewar Fa’iza ta dawo jiya?
ita da take a kango a yashe
tana jinya?

9- Acikin fim din
yakamata idan an dauki
tsahon wani lokaci wani
abun ya faru a rubuta mai
kallo ya gani bayan kazaa
saboda tabbacin cewar
abun zai faru a wannan
tsahon lokacin misali
kamar daukar cikin Fa’iza
da haihuwarta an nuna su
a lokaci kan kani.

10- Yakamata anunawa
mai kallo sanadin daya sa
asirin su Fa’iza ya tonu
har aka kawo hoton bidiyo
dinta ranar daurin
aurenta sannan a nuna
wanene ya kawo.

Karkarewa :

Fim din ya yi kyau sannan
akwai darasi amma wasu
kalamai da akayi amfani
da su sun yi tsauri dayawa
ya kamata a sakaya yanda
kowa zai iya kalla hatta
kananan yara saboda an
bude abubuwa ko don
saboda tarbiyyar kananan
yara.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Muryarhausa24.com don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum

An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com
Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Muryarhausa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki
daya Amin Summa Amin.

Source by ©Fim Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: