Monday 2 April 2018

Karanta Kaji: Sirrika Guda 7 Da Ya kamata Kowane Musulmi Ya Sani Akan Amfanin ruwan Zam-Zam

Tura Wannan Zuwa Ga

Da sanadin shafin yanar gizo na lifeinsaudiarabia.net, NAIJ.com. da hadin giwar shafin muryarhausa24.com ta kawo muku wasu sirrika goma da ruwan Zam-Zam ya kunsa da kuma ya dace a ce kowane musulmi ya ribaci ilimin da suke tafe da shi domin yada shi ga sauran al'umma.

1. Asalin Ruwan Zam-Zam: Dan Hajara Annabi Isma'il, tsira da aminci su kara tabbata a gare su, ya tsunduma cikin yunwa da kishirwa bayan guzuri ya yanke da mahaifin sa Annabi Ibrahim ya bari.

A sakamakon tausayi da jin kai irin na uwa ga dan ta, ta shiga kai komo tare da hawa da sauka a kan duwatsun Safa da Marwa wajen neman abin da dan ta zai sanya a baka. Bayan wannan kai komo har sau bakwai sai kawai cikin mamaki ta ankare da wani ruwa dake gudana a karkashin inda sawayen dan ta, Annabi Isma'il.

2. Wasu sunaye da ake yiwa ruwan lakabi: Akan kirayi ruwan Zam-Zam da Maimoona, Shabbaa'a da kuma Murwiya.

3. Karfin jiki: Binciken wani masanin kimiyya na kasar Jamus, Dakta Knut Pfeiffer ya bayyana cewa, kwayoyin halittu na jikin dan Adam su kan zabura da zarar an kwankwadi ruwan Zam-Zam.

4. Amfani: Alfanun ruwan Zam-Zam ba su da iyaka, ya kan biya bukata duk wata niyya da aka sha ruwan domin ta.

5. Kiwon Lafiya: Ruwan Zam-Zam ya kunshi sunadaran Magnesium da Calcium dake kawar da wata cuta mai kwazaba.

6. Tarihi: Tun shekaru sama da 4000 da suka gabata, ruwan Zam-Zam yake ta gudana ba bu kakkautawa.

7. Tsafta : Bincike ya bayyana cewa ba bu wani tsaftaceccen ruwa da zai goga kafada da ruwan Zam-Zam.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Muryarhausa24.com don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum

An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com
Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Muryarhausa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki
daya Amin Summa Amin.

Source by © Hausa Naija and Hausaloaded

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: