Thursday 10 May 2018

Karanta Kaji: Takaitaccen Tarihin Jihar Katsina tare da Tarihin Sarakunan dasu Mulki Jihar Katsina A Takaice

Tura Wannan Zuwa Ga


Sarkin Katsina Sir. Usman Nagogo (1944-1981) Garba Jika, Wazirin Ayyuka na Sarkin Katsina Sir. Usman Nagogo
Daga Dungurun sai Lord Lugard, bayan duk an kulla wadannan yarjejeniyoyi sun kuma ba Sarki Abubakar ya rattaba hannu ya ki amincewa ya komo Katsina.

A nan kuma Katsina, bayan da turawa su ka lura kamar hankalin su ya fi karkata ga Dikko, ma’ana sun fi shakuwa da shi sai suka nada shi Sarki, cikin 1907. Shi kuma ya damu da cewa lallai sai sun dawo masa da dan uwan sa Sarki Abubakar murabus a Katsina kusa da shi. Su ka ce masa ai doka ba ta tanaji haka ban a idan an hutar da wani sarki ya kuma koma garin sa ya zauna, saidai ya zauna wani gari daban. Sarki Dikko ya dai yi tsaye lallai sai sun dawo masa da shi kusa da shi ko da Kano ne, inda za ya rika jin motsin sa. Su ka bi umurnin Sarki su ka maishe da Sarki Abubakar Kano, a wata unguwa da ake kira Ciranci. To anan ne wuci-wuci Sarki Dikko kan tafi ya gaishe da shi su yi hira irin ta ‘yan uwa .

Wajen karshen shekarar 1903 sai aka mayar da masarautar Katsina a karkashin mulkin lardin Kano, aka kuma nada mata Razdan mai Daraja ta uku R. E. Olibier, wanda ya zo ya zauna a Katsina, ya na kuma amsar umurnin Razdan mai daraja ta daya daga Kano. A ranar 9/11/1906 sai aka hutar da Sarki Yero daga rikon kasar Katsina, nan take kuma aka nada Durbi Muhammadu Dikko a matsayin wanda za ya rike birnin Katsina na wucin-gadi amma ba su yi masa alkawarin tabbatar da shi ne sarkin Katsina na gaba ba.

Sai kuma ranar 25/1/1907 mai rike da mukamin Kwamishina mai daraja ta daya na Arewa (watau Acting High Commisioner, Northern Protectorate) Mista Wallace ya nada Muhammadu Dikko Sarkin Katsina.
Wannan wata sakayya ce da su ka yi masa na na’am da goyon baya da ya nuna ma manufofin su.

An haifi Sarkin Katsina Muhammadu Dikko dan Durbin Katsina Muhammadu Gidado dan Tafarkin Katsina Malam Dahiru a cikin birnin Katsina a cikin shekara ta 1856. Ya yi karatun Alkur’ani mai tsarki har ya sauka ya kuma karanta littattafai na addinin Islama. Ya yi hidimar kasuwanci da cinikayya ba ma dai tsakanin kasashen da su ke a yankin sahara. Ya kuma halarci yakoki da dama.

Wannan basirori da ya hada su su ka sanya ya samu kwarewa da iya sanin yanda sha’anin sarauta da mu’amulla da mutane su ke. Muhammadu Dikko ya samu sarautar Karshin Katsina kuma Maigarin Muduru da kuma daga bisani ya zama Danbarhin na Katsina kuma maigarin Giremawa daga shekarar 1880 zuwa 1887. Lokacin rasuwar kawunsa Durbin Katsina kuma Hakimin Mani Muhammadu Sada sai aka nada shi ya maye gurbin sa, watau a cikin shekara ta 1896, kafin daga bisani ya zame Sarkin Katsina.

Sarki Dikko, shi ne Sarkin da a lokacin sa ya yi ayyukan da kusan babu sarki a arewacin kasar nan da ya yi. Shi ne ma Sarki na farko a Katsina da ya assasa samuwar baitulmali, ya kuma kirkiro biyan albashi ga ma’aikatan N. A. (Natibe Authority) cikin 1907. Ko bayan nada shi Sarkin Katsina, Muhammadu Dikko ya gaji hakimai guda 16: Mani, Rimi, Dutsi, Dutsin-Ma, Kaita, Malumfashi, Musawa, Kankara, Faskari, Maska, Ruma, Bindawa, Ingawa, Mashi, Dankama, sai Tsafe. Shi kuma ya kirkiro sabbi guda 7 kamar haka; Katsina cikin 1907, Jibiya cikin 1908, Safana cikin 1909, Bakori da Batagarawa cikin 1910, Tsagero cikin 1919, da kuma Kusada cikin 1920. Cikin kuma 1909 sai aka mayar da kasar Tsafe ga Sakkwato ita kuma Pauwa (Kankara) ta zauna a yankin kasar Katsina, lokacin da Turawan Birtaniya su ka aiwatar da gyaran iyaka.

Mun dan yi tsakaci akan Kauran Namoda a baya, to bari mu yi tsokaci akan kafuwar garin. Asalin kafa garin Kauran Namoda wani almajirin Shehu Usman Bin Fodiyo ne da ake kira Muhammadu Namoda. Ya na da wa mai suna Abu Amil wanda shi Shehu ya ba tuta ya zo ya kafa garin Zurmi, sannan kuma ya na da kanensa Umaru Mamuda. Su duka ukkun yaran Shehu ne. Da yakin Jihadin Shehu ya yi nisa sai aka nemi Namoda da ya yo kaura daga Zurmi ya yo yamma don ya sari gari. Inda ya sara din ne Kauran Namoda (ma’ana wurin da Namoda ya yo kaura daga Zurmi ya zo ya kafa) Amma a kewayen Kaura din akwai wasu mutane al’ummar Zamfarawa a wani wuri da ake kira Kiyawa.

A lokacin Kiyawa din suna da Sarkin su, ana kiransa Dagazau na Ma’inna. To shi ya kawo wa Namoda caffa ya kashe shi. Amma da kanensa mai suna Umaru Mamuda ya gaje shi mulki sai ya tafi shima ya dauki fansa ga wansa, ya kashe Dagazau, ya fasa jama’arsa wanda ya sa suka yi kaura zuwa Adafka, cikin yankin Bukkuyun.

Jin dadin haka sai Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya nada Umaru Mamuda din Sarkin Kiyawar Kauran Namoda, tunda ya ruguza ko hana bori da sauran kafircin da ake yi a Kiyawa. Mafari kenan a yau sarautar Kiyawa ta koma sarautar Magaji.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin aiki Tukuru don jin dadin ku Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Muryarhausa24.com Zata Kasance Babbar Kafar Yada Labarai aduk fadin Duniya domin Bunkasa Harshen Hausa, domin Zafafan Labarai ziyarci www.muryarhausa24.com
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin Muryarhausa24.com aduk inda kuke a fadin Duniya farin cikin ku shine Farin cikin Mu
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
Burin shafin Muryarhausa24.com shine ta fito da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi
me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@
gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki daya Amin
Source by ©Leadership A Yau
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user