Wednesday 30 May 2018

Karanta Yanzu Kaji: Abubuwa 5 da Yakamata Ku sani dangane da Jawabin Shugaba Buhari akan Ranar Tunawa Da Zagayowar Mulkin Dimokradiya A Najeriya

Tura Wannan Zuwa


Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi jawabi ga ‘yan Najeriya a ranar demokaradiyya, inda ya tunawa ‘yan Najeriya cika shekaru 19 da Najeriya ta dawo turbar yanci.

Wannan rana ta kuma yi daidai da cikar shugaban kasar shekaru 3 akan karagar mulki.
A cikin jawabin nasa, Shuaban kasa Muhammadu Buhari ya tabo wasu muhimman babtutuwa da suka shafi cigaban da kasar ta samu.

1. Buhari ya yi jawabi kan cewa lallai anci nasarar karya lagon kungiyar Boko Haram a hare haren da take kaiwa a yankinArewa maso gabashin Najeriya. Duk kuwa da cewar Shugaban ya kaucewa bayyana cewar an gama da Boko Haram.
2. Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa tayi nasarar kwato ‘yan matan Chibok 106 da Boko Haram suka sace su, da kuma ‘yan mata 104 da aka ci nasarar kwato su da Boko Haram din suka sace a makarantar ‘yan mata ta Dapchi dake jihar Yobe, da kuma wasu karin mutane 16,000 da aka kwato daga hannun ‘yan Boko Haram
3. Ya kuma yi Magana kan batun da ya masu yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, da kuma batun rikicin da yaki ci yaki cinyewa na tsakanin Manoma da kuma Makiyaya, wanda ya janyo hasarar rayuka masu dumbin yawa musamman a yankin Binuwai da Taraba da Adamawa.
4. Shugaban yayi bayanin yadda aka samu zaman lafiya a yankin Neja Dalta mai arzikin man fetur, inda yace ana samun cigaba wajen samar da zaman afiya a yankin, domin samun adadin man da ake bukata a kullum domin samarwa da Gwamnatin Najeriya kudaden shiga.
5. Shugaban yayi bayanin irin dumbin kudaden da Gwamnati ta tara a tsarin asusun nan na bai daya wato TSA, inda yace anci nasarar tara sama da Naira biliyan 200 wajen kudaden da ake baiwa ma’aikatan bogi, da kuma dawo da zunzurutun kudi Naira biliyan 500 daga hannun masu handama da babakere.
Wadannan sune wasu daga cikin jawaban da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ga talakawansa a yau, Talata, 29 ga watan Mayu.
A baya NAIJ.com ta rahoto cewa, Gwamnan jihar Niger Abubakar Bello, a ranar Litinin, ya bayyana dalilai da dama wadanda suka nuna cewa ya kamata ‘yan Najeriya su sake jefawa Buhari kuri’a a zaben 2019.
Bello, ya bayyana cewa sake tsayawar Muhammadu Buhari takarar shugaban kasa a 2019, shine domin shimfida kwakwaran tubalin ginin cigaban damokradiyyar Najeriya.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin aiki Tukuru don jin dadin ku Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin website din akwai "Home" sai ku shiga,

mungode

Muryarhausa24.com Zata Kasance Babbar Kafar Yada Labarai aduk fadin Duniya domin Bunkasa Harshen Hausa, domin Zafafan Labarai ziyarci www.muryarhausa24.com

Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin Muryarhausa24.com aduk inda kuke a fadin Duniya farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24.com shine ta fito da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi
me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@
gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki daya Amin

Source by ©Hausa Naij
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user