Sunday 10 June 2018

Hotuna da Cikakken Tarihin Fati Washa: Abubuwan da Yakamata Kusani dangane da Rayuwar Fati Washa

Tura Wannan Zuwa


Fatima Abdullahi Washa kamar yadda asalin sunan ta yake ba bakuwa bace a harkar fim din Hausa don kuwa ta fito a fina-finai da dama inda tayi fice Duniya ta san ta jama’a sun fi sanin ta da Washa ko Fati Washa watau sunan Mahaifin ta ya bace.

Jarumar tana lokaci, tana samun aiki fiye da duk wata jaruma domin acikin fim biyar sai ka samu ta fito a uku ko hudu, daga cikin tsoffin finafinanta akwai Sarki, Kadan daga cikin fina-finan wannan Jaruma akwai Ya Allah daga Allah, da tayi a 2014, 'Yar Tasha a 2015 Washa ta fito a Ana Wata ga Wata a shekarar 2015. Sannan ta fito a Mijin Biza, Hindu, Dangin miji, Matar Wani da sauransu.
Akwai jita-jita da take yawo akan Jarumar tana soyayya da Jarumi Adam A Zango, duk dai basu fito fili sun tabbatar ko karyata hakan ba, Amma kowa ya yadda fati washa tafi kowace jaruma kusa da Adam A Zango domin tun daga fim din Sarki har yanzu suna tare.

Fatima ba ruwanta da fada da kowa domin tunda take ba'a taba jinta da wani ko wata ba suna rigima ko kuma jan fada.
Films dinta da  ta fito da Wanda zasu fito suna da yawa Irinsu Gamdakatar, Gwaska Returns, Gobarar titi, Rariya, Boyayyen Al'amari da sauransu.

Fati Washa kamar su Rahma Sadau, Hadiza Gabon, da 'Dan wasa Ali Nuhu, dsr tana kan shafin Tuwita na yanar gizo inda ta ke aikawa dinbin masoya da mabiyan ta sako da game da halin rayuwa.

A halin yanzu jarumar tana daya daga cikin fitattun jarumai mata da tauraruwar su ke haskawa a masana'antar kannywood.

 Hotuna daga shafin Muryarhausa24.com.ng

Takaitaccen Tarihin Hadiza Gabon da Hotunan ta: Abubuwan da Yakamata Kusani dangane da Rayuwar Jaruma Hadiza Gabon - Karanta Yanzu Kaji


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Domin samun Labarai,Nishadi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, FADAKARWA,NISHADANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika sakon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun sakon ka/ki Mungode

Source: www.muryarhausa24.com.ng

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user