Sunday 3 June 2018

Karanta Yanzu Kaji Dalili: Tabbas Allah ne ya hukunta Mohammad Salah saboda kin yin azumi - Inji Malamin Islama Mubarak Al-Bathali

Tura Wannan Zuwa Ga


Wani mai wa'azin addinin musulunci dan kasar Kuwaiti, Mubarak Al-Bathali ya bayyana cewa rashin yin azumi da dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Mohammed Salah ya yi a ranar 26 ga watan Mayu ne ya janyo masa fushin Allah a wasan karshe da suka buga a Kiev tsakanin Liverpool da Madrid.

Mohammed Salah dai ya yi gwagwarmayar neman kwallo ne da mai taimakawa wajen tsaron gida na kungiyar Madrid, Sergio Ramos wanda hakan ta haifar masa jin rauni a kafadarsa kuma daga baya ya fice daga wasar bayan mintuna 30 da farawa saboda radadin ciwo.

Da farko dai, an ruwaito cewa Mohammed Sallah zai yi azumi a ranar wasan karshe ta cin gasar kwararu na turai da za'ayi a birnin Kiev amma daga bisani sai likitan kungiyar Liverpool ya tabbatar da cewa ba zai yi azumi a ranar ba.

Mohammad Salah ya dai ajiye azuminsa a ranar 26 ga watan Mayun 2018 amma bai samu ikon kammala zango na farko a wasan ba kuma daga baya kungiyarsa ta Liverpool tayi rashin nasara inda kungiyar Real Madrid ta doke Liverpool din da 3-1.

Sai dai malamin kasar Kuwaiti, Sheik Mubarak al-Bathali ya ce Salah ya yi zunubi saboda ajiye azumi da ya yi a dalilin kwallon inda ya kara da cewa bashi da wani kwakkwaran dalili a addinance na ajiye azumin.

Malam yaci gaba da cewa "Kada kayi tunanin cewa dabara da kokari ne ke tafiyar da rayuwar musulmi, rayuwa na hannun Allah ne kuma shi ya ke juya ta yadda ya so."

"Wata kila ma raunin da ka samu alkhairi ne gare ka," kamar yadda mai wa'azin kasar ta Kuwaiti ya rubuta a shafinsa na Twitter.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin aiki Tukuru don jin dadin ku Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin website din akwai "Home" sai ku shiga,

mungode

Muryarhausa24.com Zata Kasance Babbar Kafar Yada Labarai aduk fadin Duniya domin Bunkasa Harshen Hausa, domin Zafafan Labarai ziyarci www.muryarhausa24.com

Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin Muryarhausa24.com aduk inda kuke a fadin Duniya farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24.com shine ta fito da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi
me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@
gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki daya Amin

Source by ©Hutu Dole
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user