Monday 25 June 2018

NEMAN TAIMAKO KO SHAWARA DAGA KHADIJA ABDULLAHI

Tura Wannan Zuwa Ga
Khadija Abdullahi Yarinya ce 'yar Shekara 13 wacce ake zargin Wani mutum ya yiwa fyade ya kuma saka mata cutar HIV a unguwar Kachi dake Qaramar Hukumar Dutse, Jihar Jigawa.


Rubutawa: Sani Hamza Funtua

Mahaifinta Mal. Abdullahi Ahmed yace sun kai rahoto wajen 'yan sanda inda suka yi bincike suka kuma shigar da qara kotu, sai dai ba a zauna Shari'ar ba kawai suka ga an saki wanda ake zargi yana yawo a gari. Sun yi qoqarin tuntu6ar jami'in hulda da jama'a na kotun amma suka kasa samunsa.

Hakan Ya sa suka Je Freedom Radiyo Dutse inda aka sa rahoton a wani shirin su, Bayan an saka rahoton ne Jami'in Hulda da jama'ar Yaje gidan Radiyon Ya yi bayanin cewa an saki wanda ake zargin ne a kan beli.

Amma abin tambayar shine dama ana bayar da beli kafin zaman Kotu?
Iyayen Khadija dai suna zargin ana qoqarin Kashe maganar ne saboda wanda ake zargin Abokin wani mai sarauta ne a garin, Saboda haka suke neman Taimako ko Shawara akan hanyar da zasu bi domin nemarwa Yarinya haqqinta.

Sun nemi kar a saka hotonta a wannan Kafa domin gudun tsangwama wanda yanzu haka take fuskanta a garinsu.

Za'a Iya Tuntu6ar Mahaifinta Mal. Abdullahi Ahmed a lambar waya 07066216969 ko 08184306161.

Domin samun Labarai,Nishadi,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna, Hausa Videos,Wakoki Hausa, Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari  ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika sakon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com za muyi farin ciki da samun sakon ka/ki Mungode

Source: www.muryarhausa24.com.ng

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user