Friday 27 July 2018

Za A Yi Kusufin Wata Mafi Tsawo A Tarihin Duniya - Karanta Yanzu Kaji

Tura Wannan Zuwa
Zai kasance kusufin wata mafi tsayi da aka taba yi a karni na 21, a cewar Hukumar Kula da Sararin Samaniya.

A ranar Juma'a 27 ga watan Yuli za a yi kusufin wata da ba a taba yin irinsa ba a duniya.

Kuma idan har kun yi sa'a, za ku iya ganin kusufin na tsawon sa'a daya da minti 43.
Mene ne kusufin wata dundum?

Kusufin wata kan faru ne a yayin da Rana da Dunyiar Earth da kuma Wata suka jeru da juna, hakan na nufin Duniyar Earth na daf a tsakanin Rana da Wata, inda ta tare hasken rana.

Kusufin kan faru ne a yayin da Wata ya shiga karkashin inuwar da Duniyar Earth ta samar.

Me ya sa ake kiransa "bakin wata"?

Daren da kusufin zai faru zai hadu da lamarin da aka fi sani da "Blood moon" ko "bakin wata" saboda yadda yake zama ja-jahur.

A yayin da kusufin na ranar ga watan Yuli watan zai tsaya a wani waje, inda shi mafi nisa tsakaninsa da duniya.

Yaushe kuma a ina za a ga kusufin?

Za a ga kusufin da za a yi ranar 27 ga watan Yulin a mafi yawancin sassan Turai da Afirka da Gabas Ta Tsakiya da Tsakiyar Asiya da Asutraliya - kusan dai a ko ina ban da Kudancin Amurka.

Ba kwa bukatar wata babbar na'ura don kallon kusufin, abin hangen nesa ma kawai ya isa a duba da shi.

Idan har kun kasance a wajen da za ku iya kallo, to za ku ga kusufin ta yankin da wata ya yi kasa-kasa, inda zai fi bayyana sosai da misalin karfe 8.21 agogon GMT.

A ina za a fi ganinsa da kyau?

Wajen da za a fi ganin wannan kusufi da kyau shi ne rabin gabashin Afirka, da Gabas Ta tsakiya da Tsakiyar Asiya.

Ba za a ga kusufin a yankuna irin Tsakiya da Arewacin Amurka ba.

A kudancin Amurka kuwa, za a gan wani bangare nasa ne kawai a yankunan gabashi, kamar a biranen Buenos Aires da Montevideo da Sao Paulo da kuma Rio de Janeiro.

A wadancan biranen da wadanda ke kusa da su, za a ga kusufin ne a yayin da watan ke bacewa daga sararin samaniya.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Domin samun Labarai,Nishadi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, FADAKARWA,NISHADANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika sakon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun sakon ka/ki Mungode

Source: BBC HAUSA
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user