Saturday 28 July 2018

TAKAITACCEN TARIHIN KAFUWAR BIRNIN KANO A AREWACIN KASAR NIGERIA - KARANTA YANZU KAJI

Tura Wannan Zuwa
Shekaru sama da dubu biyu da suka gabata, sun tabbatar da cewa akwai mutane masu rayuwa a Afirka ta yamma. Wadannan mutane basu da wata sana'a sama da farauta.

Birnin Jihar Kano  a Nigeria

Marubuci: Sadiq Tukur Gwarzo
08060869978

A wancan lokacin sana'ar noma bata shahara ba a duniya, don haka mutane suke dogaro da farautar namun daji a matsayin aikin yi. Lokaci yana tafiya, har labarin wani babban dutse ya fara zama shahararre a kunnuwan mafarauta. Dalili shine, akwai namun daji masu yawa a yankin da dutsen yake. Sannan ana iya haqo Tama da Qarfe a wurin. Wadannan abubuwan sunfi komai daraja a wancan lokaci. Domin akasarin kayayyakin farautar waɗannan mutane da duwatsu aka sassaqa su, don haka suke da matuƙar buƙatar kayayyakin Ƙarfe saboda darajar su da sauƙin dasu ke dashi a wajen sarrafawa. Sunan wannan dutse DALA.

A bisa wata mahangar ta masana, wasu na ganin yankin dala a matsayin wuri ne wanda k'abilu daban-daban (kazo-na-zo) ke taruwa domin shiga dajin dake jikinsa yin farauta. Shine har wasu ke ganin babu takamai_man k'abilar data fara zama a yankin., amma dai ana ganin yarukan da Ƙabilun ke amfani dashi sun haɗar dana ZULU, FULA, da SHONA. (Idan hakane, hausa na iya fitowa daga haɗakar waɗannan yaruka kenan, amma dai zamu saurara daga masana a bisa haka)
Babu takamaiman wanda ya fara zuwa bakin wannan dutsen, wasu sunce wata k'abila mai suna Dala ce ta fara zama, daga nan aka sanyawa dutsen suna Dala, wasu kuma sunce sunan wanda ya fara gina gida akan dutsen tare da fara rayuwa akai shine Dala. Don haka ake yiwa dutsen kachokan lak'abi da sunan sa.

Daga bisani dai, sai mutane suka fara zama kadan-kadan a gefen dutsen domin neman arziki. Makera na zuwa don hak'o tama da k'arfe tare da sarrafawa, mafarauta kuna na zuwa don siyen k'arafa tare da shiga farauta a dajin dake bayan dutsen dala, kamar dai yadda yake a tarihi, za'a ga cewa mutanen da suka gabacemu sunfi rayuwa a wuri mafi daraja. Watau sa'ar da ruwa yake da tsada a wuri, sai kaga mutanen sun gina gari a wurin da ruwa yake, kamar yadda ya faru a garuruwan Makkah da sauransu.

Waɗanda suka ce Dala ne ya fara zama akan dutsen, sunce ya rayu tsawon shekaru masu yawa akan wannan dutse, tare dashi akwai matarsa da 'ya'yansu bakwai, huɗu maza uku mata. Wani mai suna Garegaji aka bayyana a matsayin babban d'ansa, shine kuma akace uban wani ƙaƙƙarfa mai suna Nuzamu, Nuzamu kuwa ance shine ya haifi Barbushe. Barbushe mutum ne ƙaƙƙarfan gaske, wanda akace yakan iya kashe giwa ya saɓota a kafaɗa duk girmanta.

LittafMtarihin Kano 'Kano chronicle' ya faro tarihin kano ne daga lokacin Barbushe. Shine ma har wata masaniyar tarihin Nigeria mai suna Elizabeth Isichei tayi hasashen cewa Barbushe ɗan ƙabilar Sao ne saboda yadda akace girmansa da ƙarfin sa yake yafi kamanceceniya da ƙabilar ta sao.

Ƙabilar sao kuwa itace tsohuwar ƙabilar da tarihi ya nuna cewa al'ummar kanembou (Kanem) sun samo tsatso daga garesu.
Tarihi dai ya nuna cewa a lokacin Barbushe shine sarkin mutanen dake zaune a zagayen dutsen dala. Kuma suna da al'adar bautawa wani gunki mai suna 'Tsumburbura' wanda yake can kan saman dutsen dala, akan wata bishiya wadda take zagaye da katangu mai suna Shamus. Ance babu mai shiga wurin dodon tsafi tsumburbura sai barbushe. Duk kuwa wanda ya shiga sai ya mutu. Barbushe kuwa ance a saman dutsen yake rayuwa abinsa. Yana saukowa ga mutanen sa sau biyu a shekara domin gudanar da bikin bauta na al'ada. A lokacin mutane ke taruwa sosai a bakin dutsen na dala suna jiran saukowar sarkinsu barbushe. Wanda yake saukowa gabanin faduwar rana. Yana mai buga ganguna. Sai yayi kirari da yabo ga tsumburbura, mutane suna tayashi.

Daga nan akace sai yahau sama mutanen na biye dashi a baya har izuwa saman dutsen na dala. Wanda akace daf da isarsu saman dutsen sai mutanen su yanka hadayar da suka kawowa tsumburar, abinda sukan yanka kuwa shine ; bakin kare, bak'ar kaza, ko bak'ar akuya. Idan suka isa bakin ɗakin bauta kuwa, sai kowa ya tsaya. Barbushe ne kaɗai ke shiga.
Kafin shigarsa ance sai yayi kirari da kuwwa. Yana cewa "Sai ni magajin dala. Mutane dole su bini, ko sunk'i ko sunso". Daga bisani idan ya fito, sai ya jagoranci bautar tsumburbura, wadda ake zagaya ɗakin bauta ana rawa da kiɗa tsirara.
Idan an kammala kuma sai aci asha a wurin. Sannan sai Barbushe ya fadi saƙon da tsumburbura ya bashi. Saƙon da mafi akasari akace labari ne na abubuwan da zasu faru a shekara mai zuwa.

Duk waɗannan abubuwa ana hasashen sun faru ne a wasu shekaru ƙasa da shekara ta 900AD (miladiyya) bayan wafatin Annabi Isa AS. Koda yake Marubucin littafin 'Kitab Al-buldan' mai suna Al'yaqubi bayan yawace-yawacen sa da yayi a kusa da yankin, ya ruwaito a shekarar 872-873 miladiyya cewa "akwai wata masarauta awani wuri dake tsakanin masarautar kanem da tafkin kwara (dai-dai da ko kuma kusa da inda kano take a yanzu), mai suna 'HBSH'. Sunan mai mulkinta 'MRH' sunan birnin ta 'ThBYR'.

Rashin wasulla a waɗannan kalmomi yasa shakku da jayayya a tsakankanin masana tarihi. Domin wasu na hasashen sunan masarautar shine Hausa, domin kuwa sunce HBshH na nufin Habasha ne, sunan da ake tsammanin daga cikinsa aka samo sunan Hausa. Ta yadda wasu sukace asalin Dala daga ƙasar Habasha ya taso tare da zuriyarsa, da abokansa Ranau da Gayya. Don haka daular daya kafa take amsa sunan ƙasar su Habsha kenan.

Wasu kuma na hasashen cewa ita waccan masarautar ta auku ne a kusa da kano, amma daga baya kafuwa da ƙarfin da kano tayi ya rusa ta, ya kuma yi sanadiyyar komawar mutanen ta zuwa kano. Sannan babu wata alaƙa tsakanin mutanen yankin Dala da Habashawa na waccan lokaci dube da irin al'adun da mutanen Dalan ke aikatawa yasha bambam da waɗanda Habashawa ke aikatawa a dai-dai wannan lokaci.

Koma ya abin yake, daga baya littattafan tarihi na kano misalin 'Kitab Tarih baladil Laziy Musamma Kano' (har yanzu ana taba-bar wanda ya rubuta shi), Raudat al-akbar na Abdulqadir bn mustafa Almagili da Tayqidil Akbar na Mallam Muhammad zangi sun ruwaito cewa wani mai suna Bagauda ne ya zama sarkin kano na farko a tarihi.

Shi kuwa bagauda wasu na cewa jikan Bayajidda ne, kuma daga Daura suka riski garin Gaya, sannan suka taso shi da al'ummar sa, har ma akace sunan su shine 'Abagayawa' (waɗanda suka zo daga Gaya) ko kuma ace musu Gaudawa, shiyasa kuma ake kiransa da 'Bagauda', ma'ana, mutumin Gaudawa, kamar yadda mallam bahaushe ke yiwa ɗaya daga cikin turawa laƙabi da Bature daga lafazin Baturke (watau Mutumin Turkiyya).

Wasu kuma suka ce sam, Bagauda ba jikan Bayajidda bane, Bamaguje ne maras addini wanda yazo yankin dala daga yammacin Kano, tare da wata runduna mai yawa kamar yadda Barbushe ya taɓa bada labarin zuwan su, kuma ainihin sunan sa shine kano, don haka daga nan kano ta samo sunan ta.

Amma dai, wasu sune shi Kano wani maƙeri ne wanda yazo gefen dutsen Dala daga Gaya, har kuma ɗaukakar sa a kafatanin yankin yasa daga baya ake yiwa ɗaukacin garin laƙabi da sunansa.

Shi kuwa Bagauda, tana iya yiwuwa kodai daga Barka ko Sheme ya taso shida ɗanuwansa Bugau, ya riski Baɗari da Goɗiya, har kuma ya shigo kano ya sauka a Maɗatai. Ko kuma ta yiwu daga Daura ya tashi ya zagaya garin Gaya, sannan ya shiga garin Kano.

A lissafi dai, dai-dai da yadda littafin Littafin tarihin Kano 'kano chronicle' ya zayyana (duk da cewa an samu saɓanin shekarun mulkin wasu sarakuna) ya nuna cewar Bagauda ya rayu a matsayin Sarkin kano a wani lokaci dake tsakanin shekara ta '950 ko 999 har zuwa 1031 ko ma sama da haka.

Daga nan kuma sai sarakunan jinsin sa suka cigaba da mulki a kano har na kusan tsawon shekaru 450, tunda ance Sarkin kano Muhammad Rumfa shine Sarki musulmi na farko da aka soma rubuta littafin addini a tarihin sarakunan kano, zamanin da wani shahararren Malami da ake kira al Maghili ya iso kano. Kuma ya amshi mulki ne a wajajen shekara ta 1490.

Ga kaɗan daga sarakunan farko na birnin Kano:-

Sarakunan Masarautar Kano Gyara

1. Bagauda ɗan Aunaka (Aunaka sunan mahaifiyarsa ne kamar yadda yazo a littafin Kano Cronicle) (Yayi mulki 999-1063)
2. Warisi dan Bagauda (Yayi mulki 1063-1095)
3. Gijimasu dan Warisi (Yayi mulki 1095-1134)
4. Nawata (Yayi mulki 1134-1136)
5. Yusa (Yayi mulki 1136-1194)
6. Naguji (Yayi mulki 1194-1247)
7. Guguwa (Yayi mulki 1247-1290)
8. Shekarau (Yayi mulki 1290-1307)
9. Tsamiya (Yayi mulki 1307-1343)
10. Usmanu Zamnagawa (Yayi mulki 1343-1349)

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Domin samun Labarai,Nishadi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, FADAKARWA,NISHADANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika sakon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com 

Za muyi farin ciki da samun sakon ka/ki Mungode

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user