Sunday 5 August 2018

Karanta Dalilin da Yasa Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Hafiz Bello ya Mika Takardar Ajiye Aiki

Tura Wannan Zuwa Ga
A yau Lahadi ne mataimakin gwamnan jihar Kano Hafiz Bello ya mika takardar ajiye aiki wato sauka daga kujerar mataimakin gwamnan jihar Kano.

Mataimakin gwamnan jihar Kano Hafiz Bello

Kakakin Hafiz, Abdulwahab Ahmad ne ya mika wa PREMIUM TIMES kwafin takardar.

A cikin takardar, Hafiz ya bayyana cewa sam baya jin dadin yadda suke aiki da gwamnan jihar Abdullahi Ganduje.

” Kwata-kwata gwamna Ganduje ba ya daraja kujera ta na mataimakin sa. Ko na bada shawara ba ya dauka da hakan yasa muka fada cikin kamayamayar da jam’iyyar ta shiga a yanzu a jihar.

Wasiƙar da mataimakin gwamnan jihar Kano Hafiz Bello ya aika

” Na yi ta fama da bakin ciki, zaman maraici da kakanikayi duk a dalilin rashin daraja ni da kujerar da nike zaune a kai. A haka ne na yi shawara sannnan na yanke hukuncin hakura da aikin kawai.

Shi dai Hafiz Abubakar makusancin sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da ake ganin nan ba da dadewa ba zai canza sheka ya koma PDP.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki Mungode

Source: Premium Times Hausa
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user