Sunday 5 August 2018

Karanta Kaji: Ubangiji ba zai yafe min ba idan na mara wa Atiku baya a zaɓen 2019 – Cewar Obasanjo

Tura Wannan Zuwa Ga
Tsohon shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa Allah ba zai yafe masa ba idan har ya mara wa tsohon mataimakin sa Atiku Abubakar baya a 2019.

Obasanjo da Atiku

Obasanjo ya ce bai rasa wanda zai mara wa baya ba da za ace wai shi ne da kan sa zai mara wa Atiku baya a 2019.

“Idan kaga nayi haka to bada sani na bane amma idan har ko da sani na ne bazan taba mara masa baya ba.

” Ni fa da kuke gani na dinnan bana gaba da kowa a kasar nan. Idan kaga na fara gaba da kai toh, ba ka kauna da kishin Najeriya ne. Ni kuwa duk wanda baya kauna da kishin Najeriya da talakawan Najeriya bana tare da shi. Amma idan kana kaunar wannan kasar to muna tare tamau.

” Na fa san Atiku kamar yunwan ciki na. Kuma matsayi na a kan sa bai canza ba.

Idan ya’ya na zasu yi aure yana aiko da wakilan sa haka nima idan nasa za su yi ina aikawa da nawa wakilan. Amma wannan dabam, ba siyasa ba ne.

” Idan da na mara masa baya a lokacin da ban san shi ba, yan zu ba zan yi haka ba domin na san shi kamar yunwan ciki na. Ba zan mara masa baya ba a siyasan ce ba.

Obasanjo da Atiku sun dade suna kai ruwa rana a fagen siyasar Najeriya. Duk da kuwa sun yi aiki ne tare a wancan lokaci, Obasanjo bai yarda da takun Atiku a siyasar Najeriya ba, yana mai cewa tun a wancan lokacin Atiku ba abin amincewa da bane.

Ko alokaci Obasanj yayi kokari canza shi amma bai yiwu ba, haka dai suka ganganda suka kari sa mulkin tare.

Obasanjo ya bayyana haka ne a filin jirgin saman Abuja, bayan dawowa da yayi daga kigal, kasar Kongo.

DUK MAI HANKALI IDAN YA KARANTA JAWABIN SHUGABAN KASA BUHARI SAI YA ZUBDA HAWAYE - KARANTA YANZU KAJI

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki Mungode

Source: Premium Times Hausa

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user