Thursday 16 August 2018

Shin ko kasan Baiwa 11 Da Allah Ya Yi Wa Sheikh Ja'afar Yayin Rasuwarsa?

Tura Wannan Zuwa Ga
1. SHAHADA: Ya yi Shahada iri daya da ta Sayyidina Umar (R.A).


Sheikh Ja'afar

Marubuci: Rabi'u Maiwaya Limawa

2. Ya rasu ranar Juma'a: Rasuwar Ranar Juma'a alama ce da ake kyautata wa Mutum zato ya samu dacewa.

3. Mahaddacin Alkur'ani ne: Ana kyautata zaton duk wanda ya haddace Alkur'ani Mai Girma ya kuma kiyaye shi ya yada shi. Zai samu rabauta ranar Lahira.

4. Kisan Gilla: Duk Muminin da aka yi wa kisan gilla ana sa ran laifukan sa sun rataya a wuyan wanda ya kashe shi.

5. Ya cika da kalmar SHAHADA: Kafin rasuwar sa an ji shi ya na maimaita kalmar La ila ha illallah Muhammadur Rasulullah

6. Dandazon Mutanen da suka halarci jana'izarsa: Ana kyautata zaton duk mamacin da mutane 40 suka halarci jana'izarsa wadanda ba sa shirka zai samu dacewa.

7. Ya rasu ya na Sallar Asuba. Sallar Asuba na daya daga cikin Sallah mai madaukakiyar daraja.

8. Limami ne shi: Jagorancin Sallah wata babbar baiwa ce da ke kusanta Bawa zuwa ga Allah.

9. Ya Karanta Suratul MA'ARIJ: Kafin a kai ga kashe shi ya karanta sura daga cikin Alkur'ani Mai Girma.

10. Ya Dago Daga SUJADA: Sai bayan da ya dago daga sujada sannan makisan sa suka fara harbin sa.

11.Ya Nemi Gafarar Mutane Kafin Rayuwar sa. (Duk wanda na yi wa ba daidai ba don Allah ya yafe min).

Ya Allah Ka amshi shahadar Malam Mu kuma Allah Ya azurta mu da yin shahada

Amin

Takaitaccen Tarihin Mal. Aminu Ibrahim Daurawa: Abubuwan da Yakamata Ku sani dangane da Rayuwar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa - Hotuna da Cikakken Tarihi

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: www.muryarhausa24.com.ng
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user