Sunday 23 September 2018

Karanta Kaji: Shin Ko Kasan Matsayin da aka Ɗora Maryam Booth akai a Gidauniyar Atiku Abubakar?

Tura Wannan Zuwa Ga
Fitacciyar jaruma Maryam Booth ta samu babban matsayi a gidauniyar tsohon mataikin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar.


Maryam Booth ta shiga sahun sauran abokan aikin ta na masana'antar kannywood dake rike da matsayi karkashin wannan gaidauniyar.

Gidauniyar Atiku Care Foundation wacce take tallafa wa mara sa galihu ta daukaka mukamin ta daga jakadiya zuwa mukamin mataimakin shugaba na yankin arewa.

Gidauniyar ta sanar da hakan ne ta hanyar wani sako da ta wallafa a shafin ta na kafafen sadarwa inda ta bayyana cewa matsayin zai fara aiki daga ranar juma'a 21 ga watan Satumba.

Maryam Booth ta shiga sahun sauran abokan aikin ta na masana'antar kannywood dake karkashin wannan gaidauniyar.

Wasu daga cikin fitattun jarumai da suka samu matsayi a gidauniyar sun hada da Fati Muhammad, Rashida Adamu da Abdu Boda.

An kafa gidauniyar ne domin taimakawa mara hali tare da nuna aikin tallafawa da Atiku Abubakar keyi ga idon jama'ar Nijeriya har da na kasashen waje.

Har ila yau gidauniyar Atiku Care Foundation ta zama cibiya da tsohon mataimakin shugaban kasa ke samu yana mu'amala da yan kasa a ko wani lungu da sako ta hanyar kafafen sadarwa da gidauniyar ta kafa.

Karku Zargi Kowa Ku Zargi Producers Da Directors Akan Rashin Ganina A Fina-finai – Maryam Booth


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: Pulse Hausa NG
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user