Thursday 6 September 2018

Karanta Yanzu Kaji: Shin dagaske ne Ibrahim Shekarau ya Sauya Sheƙa Daga Jam'iyyar PDP zuwa Jam'iyyar APC?

Tura Wannan Zuwa
Tsohon gwamnan jihar Kano ta Najeriya, Malam Ibrahim Shekarau ya fitar da wani sakon murya da ke bayyana cewa, zai sanar da matsayinsa bayan ganawa da jam'iyyar PDP.

Ibrahim Shekarau

Wannan na zuwa ne a yayin da ake yada rahotannin da ke cewa tuni tsohon gwamnan ya koma jam'iyyar APC.

Shekarau ya bayyana rashin jin dadinsa kan matakin da uwar jam'iyyar PDP ta dauka na rusa shugabancin jam'iyyar a jihar Kano, matakin da ya ce, ya saba ka'ida.

Tsohon gwamnan ya ce, zai fito da kansa don sanar da jama'a game da duk irin matakin da ya dauka nan kusa.

Wannan na zuwa ne bayan kafafen yada labarai sun rawito mataimakinsa na musamman kan kafafen yada labarai, Sule Ya’u Sule na cewa, tuni Shekarau din ya koma APC daga PDP.

A cewar Sule, “ Ina son tabbatar muku cewa, Shekarau ya yanke shawarar ficewa daga PDP zuwa APC sakamakon rashin adalcin da PDP ke nuna masa da magoya bayansa”

Mataimakin nasa ya ce, babu yadda za su ci gaba da zura wa uwar jam’iyyar PDP ido gain yadda take biye wa Rabiu Musa Kwankwaso daga ya koma PDP a ‘yan kwanakin da suka gabata daga APC.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: RFI HAUSA

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user