Monday 22 October 2018

Karanta Kaji: Manyan Aiyuka 3 da Buhari ya yi a Nigeria Waɗanda ba Kowa Bane Ya Sansu

Tura Wannan Zuwa
Ba nufina ince ba'a samu gazawa a wasu bangarorin ba a zamanin mulkin Baba, tabbas nasan akwai al'amuran da wasu ke kalla a matsayin gazawa, amma dai yanzu ina son ne inyi magana akan wadannan abubuwan da aka samu nasara akansu.....



Marubuci: Rabiu Biyora

GASU.....

1.. Social Investment Programmes for Nigerian.

A kafin zuwan Gwamnatin Shugaba Buhari babu wannan tsarin gaba daya, amma yanzu an samu ikon tallafawa mutane sama da miliyan Goma kai tsaye ta cikin Tsarin, ga wasu dubunnan matasan da aka samawa aikin wucin gadi a N-Power ana basu N 30,000 duk karshen wata, ana bawa yara abunci a makaranta duk a cikin tsarin, Rance mara ruwa na N10,000 ga dubunnan mutanen Nigeria tare da sauran wasu ayyukan duk da akeyi a karkashin tsarin Social Investment wanda Shugaba Buhari ya samar....

2.. Rail Project......

Tun shekarar 1999 har zuwa 2015 babu Gwamnatin data iya kammala aikin shimfida titin jirgin kasa a Nigeria, amma cikin kasa da shekara Hudu na mulkin Shugaba Buhari yayi kokarin samar da manya manyan layukan jirgin kasa har guda uku tare da sabbin tashoshin jiragen kasa hadi da sabbin jiragen kasa, kunga ai yayi kokari ko.....

3... Rice Importation .....

A baya kasarmu ta kusan dogara ne gaba daya da shinkafar da ake shigowa da ita daga wasu kasashen Duniya, inda mu bama iya noma wacce zata iya ciyar damu, masana lissafi sun bayyana cewa ana shigo sa shinkafa sama da Ton Dubu dari shida a kowacce shekara, amma yanzu daga 2015 zuwa yau shinkafar da ake shigowa sa ita bata kai Ton Dubu Ishirin ba, wanda hakan ke nuna yanzu muna iya samar da shinkafar da muke bukata a kasarmu ba tare dasai mun dogara da kowacce kasa wajen cin abunci ba.....

Wadannan dana lissafa kadan ne daga cikin irin nasarorin da aka samu a zamanin mulkin Muhammadu Buhari, idan kenan muka kara zabarsa zuwa kankanin lokaci nasarar da kasarmu zata samu zasu kasance masu yawa, arziki zai kara yalwata a tsakaninmu.....

Kada kayi adawa cikin rashin gaskiya, idan har kaga kuskure ko karya a cikin abun dana rubuta zanso kayi bayanin dazai fito da gaskiyar karyar danayi maimakon ka karyatani kai tsaye, ka turan a Muryarhausa24@gmail.com .....

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: www.MuryarHausa24.com.ng
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user