Sunday 21 October 2018

KARANTA KAJI: TAKAITACCEN TARIHIN DAURA A AREWACIN NIGERIA

Tura Wannan Zuwa
Tsohon Littafin tarihi na masarautar Daura da ake masa laƙabi da suna Girgam kamar dai sauran littattafan tarihin yawa-yawan masarautu, ya ruwaito cewar tun a wajajen shekaru dubu biyu kafin haihuwar Annabi Isah A.S wasu mutane ƙarƙashin jagorancin shugabansu mai suna Najib (Wasu sunce Nimroid ko Namarudu sunansa) suka yo hijira daga ƙasar su ta haihuwa Kan'ana tare da riskar inda ƙasar Daura take a yanzu.



Marubuci: Sadiq Tukur Gwarzo

Babu takamaen dalilin tasowar su, amma dai ance akan hanyar su ta tafiya, sun yada zango a tsohuwar Misira tsawon wani lokaci har kuma daga bisani wasu Misirawan na dauri suka shigo cikinsu akayi hijirar tare dasu.

Ance kuma da suka baro Misira sai suka shigo cikin ƙasar Libya, inda suka sauka a birnin Tarabulus, a zamanin da wani Sarki mai suna Abdurdaar ke mulkinta har ya so ya mallake wannan runduna amma bai samu nasara ba, daga ƙarshe shi Najib ya cigaba da tafiya da mutanensa har suka riski wani wuri da ake kira Tsohon birni, inda suka fara kafin birnin Daura kafin su koma sabuwar Daura.

Akwai ƙarancin sani matuƙa game da kafuwar daura ko kuma tsawon lokacin da tayi tana sharafi.

Marubuci Zakariyya Kabo ya kawo hujjojin cewa Daurawa misirawa ne da suka zo daga ƙasar su ta misira a littafinsa mai Suna 'Gamsasshen Tarihin Hausawa'.

Ga kaɗan daga hujjojinsa akan haka:-

1. Da akwai wani takobi mai rubutu ajikinsa irin na mazauna kasar misira ada can wanda koda turawa suka zo sai da suka ce wannan takobin babu masu irinsa sai misirawa. Kuma ko yanzu kaje Daura ana iya ɗauko maka shi ka gani.

2. Yanayin tsarin gine-ginen fadar Daura ɗaya ne dana misirawan-da. Zakaga anyi soro, sannan katangun gida masu kaurin Gaske. Akan kuma yi manyan turaku da babban fili a matsayin tsakar gida da manyan zaurukan hutawar sarki.

3. Tamburan da ake zanawa a bangwayen gidan sarauta na Daura.

Haka shima Marubuci Maje Ahmad Gwangwazo ya tafi akan cewa tsoffin mazauna Daura Mangawa ne waɗanda basa jin Hausa, don haka koda Bagauda ya riski Kano sai daya shafe aƙalla shekaru biyu yana Koyon harshen Hausa na mazauna Kano.

Akwai kuma masu ganin cewa hijira biyu ko uku akayi daga can kan'ana zuwa Daura. Inda suka ce a hijira ta farko, Najib ne ya jagorance ta. Amma a hijira ta biyu, wata jaruma da ake kira Daurama ce ta jagorance ta. Kuma daga sunan tane aka laƙabawa birnin suna Daura, har kuma aka samu cewa an shafe tsawon lokaci mata ne ke jagorantarsa.

Ga sunayen Sarakunan farko da aka samu sun mulki Daura tun tsawon lokaci da ya gabata:-

1. Kufuru
2. Ginu
3. Yakumo
4. Yakunya
5. Wanzamu
6. Yanbamu
7. Gizir-gizir
8. Inna Gari
9. Daurama
10. Ga-wata
11. Shatu
12. Fatatuma
13. Sai Da mata
14. Ja Mata
15. Ha-Ma
16. Sha-wata
17. Daurama II (wadda alokacinta ake tsammanin Bayajidda yazo Daura).

An samu cewa kusan dukkan waɗannan sarakuna mataye ne, ana kiransu da suna 'Kabaras ' fassararsa shine Magajiya da hausa. Watau wadda tayi gadon mulki kenan.

Haka kuma, akwai maganganu na tarihi dake nuna cewar an samu ɓullar Shugabanni mataye masu laƙabin 'Kabara' a wasu masarautu na ƙasar Mali, da Isra'ila.

Amma dai babu wanda ya tabbatar da wata alaƙa data kasance tsakaninsu da waɗannan Kabarori na Daura duk da cewar akwai hasashen yanayin bautar da akace Kabarorin sunyi yafi kamanceceniya shigen wadda aka taɓa samu anyi a Isra'ila.

Zuwan Bayajidda akafi labartawa a matsayin tarihin Hausa da Hausawa, amma a zahiri, labarai sun nuna cewar Bayajidda ya riski Daura ne a zamanin da Sarauniya Daurama Shawarata ke mulki, ita kuwa ana ganin itace sarauniya ta goma sha bakwai a tarihin mulkin Daura.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: www.MuryarHausa24.com.ng

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user