Monday 1 October 2018

KARANTA KAJI: SHEKARU 58 DA SAMUN 'YANCIN KAN NAJERIYA CI GABA KO KOMA BAYA?

Tura Wannan Zuwa Ga
Tun a ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 1960 ne, Najeriya ta samu 'yancin kanta daga turawan mulkin mallaka na Ingila, wanda hakan ke nuni da cewa kasar ta cika shekaru 58 da samun wancan 'yanci.




Marubuci: Abba Ahmad Gwammaja

Kasar kuma ita ce kasa mafi yawan jama'a a yankin nahiyar Afrika, wadda ake kiyasin cewa tana da jama'ar da suka doshi miliyan 200 (shi yasa ma ake mata lakabi da "Giwar Afrika" ko kuma "Giant of Africa" a turance), kuma daya daga cikin kasashe masu arzikin man fetur a duniya baki daya.

Cikin wadannan shekaru, kasar tayi shugabanni daban-daban har guda 14.

Sai dai kuma a cikin wadannan shekaru babu yadda za'ayi ace kasar bata samu wani ci gaba ba ko k'ak'a yake, haka nan babu yadda za'ayi ace ba'a samu koma baya ba ko k'ak'a.

Amma ana yin hukunci ne da abinda yafi rinjaye.

Dukkanin wata kasa da ta samu ci gaba a duniya ya samu ne ta 6angaren gwamnati da kuma jama'ar gari.

Inda a 6angaren gwamnati ake duba wasu abubuwa kamar haka:

1. Harkar lafiya (Health): Farkon abinda kowanne dan kasa yake bukata shine a samar masa da ingantattun asibitoci, magunguna da kuma kwararrun likitoci, dan kuwa da zarar an haifi jariri a gida ko a asibiti, lafiyarsa da ta mahaifiyarsa ita ce abu na farko da za'a fara tambaya, bayan anyi masa wasu 'yan gwaje-gwaje don a tabbatar da cewar lafiya kalau aka haifeshi babu wata cuta a jikinsa ko kuma wani nak'asu.

Sai kuma rigakafin da za'a ringa kaishi asibiti ana yi masa duk bayan wani lokaci, har izuwa wani wa'adi.

2. Ilmi (Education): Da zarar yaro yakai shekaru 3-4 kuma, sai gwamnati tayi iyakacin iyawarta don ta fara shigar dashi a tsarinta na ilmi mai nagarta, kuma kyauta tun daga matakin Firamare har zuwa makarantar gaba da Sakandire, inda zai fara da ECCE, kamar yadda sashe na 18 na kundin tsarin mulkin kasa yayi umarni.
Inda zata samar masa da kyawawan tsaruka wanda suka hada da: Gine-ginen makarantu, kwararrun Malamai, da kuma isassun kayyakin koyo da koyarwa.

3. Aikin yi ko sana'a (Job or Occupation): Da zarar kowanne dan kasa ya samu isashshiyar lafiya da nagartaccen ilmi, to kuwa abu na gaba da yake bukata shine sana'a ko kuma aikin yi, wanda da safe idan ya tashi yasan inda zai nufa, yayinda da yammaci kuwa zai koma gida domin ya huta, kafin gobe da safe ya nufi gurin aikinsa.

Kuma hakan ce zata saka ya dogara da kansa, tare da wadatuwa da dan abinda zai kai bakin salati shi da iyalansa, kuma ya biya wasu bukatunsa na yau da kullum, har ma ya taimakawa wasu makusantansa.
Kaga kenan yayi bankwana da zaman banza, ballantana har takaishi ga aikata wasu muggan laifuka, tunda a kullum idan ya tashi da safe yasan inda zai dosa.

4. Tsaro (Secuirity): Da zarar kowanne dan kasa ya samu isashshiyar lafiya, nagartaccen ilmi da kuma aikin yi ko sana'a, to kudi kadan gwamnati zata kashe wajen samar masa da tsaro, dan kuwa a kullum zai kasance bashi da isashen lokaci nasa na kansa, ballantana har takai ga ya tada husuma ko kuma ya aikata wani mugun laifi.

Zaman banza da rashin aikin yi shine jagoran aikata dukkanin wasu manyan laifuka a duniya baki daya, kaga kenan da zarar al'umma ta wadatu da aikin yi, to kuwa za'a samu karancin aikata laifuka, tada zaune tsaye da kuma rashin zaman lafiya.

Kuma babu wata kasa a duniya da zata ci gaba matukar babu zaman lafiya a cikinta.

5. Kayayyakin more rayuwa (Basic Aminities/
Infrastructure): Da zarar 'yan kasa sun wadatu da wadancan abubuwa guda 4 na sama, sai kuma gwamnati ta mayar da hankali wajen sama musu kayayyakin more rayuwa, wadanda suka hada da:

a. Wutar lantarki (Electricity).

b. Ruwan sha (Water Supply).

c. Hanyoyin Sufurin kasa, na ruwa da na sama (Land Transpotation, Water Transpotation and Air Transportation).

d. Hanyoyin Sadarwa (Telecommunication).

e. Kafafen yada labarai (Media).

f. Kayayyakin kwasar shara (Refuse disposal).

g. Masana'antu (Industries).

h. Noma da albarkatun kasa (Farming activities and Mineral Resources).

Da makamantansu.....

Inda a 6angare guda kuma, jama'ar gari ana son su kasance 'yan kasa nagari masu bin doka da oda, marasa son fitina, masu hadin kai da son ci gaban kasar, tare da 6ullo da dukkanin wasu tsaruka da zasu taimakawa kasar taci gaba, kuma su gujewa dukkanin wadansu abubuwa da zasu jawo zubewar mutuncinsu da kuma kasarsu a ko ina suka samu kansu, haka nan su guji lalata kayayyakin gwamnati.

Don kuwa mutum daya yana iya jawowa kasarsu 6acin suna, haka kuma zai iya daga sunan kasarsu a idon duniya.

Sannan kuma shin sun wadatu da wadancan abubuwa da ake bukatar gwamnatocin su samar musu dashi ko kuma basu wadatu ba?

Wadannan abubuwan da makamantansu sune ma'aunin da ake amfani dashi wajen gane cewa kasa ta samu ci gaba ko kuma koma baya a tsahon wani lokaci.

Saboda haka sai mu auna mu gani, a tsahon wadannan shekaru 58 ci gaba muka samu ko kuma koma baya?

Ku ci gaba da Kasancewa da mu domin samun Cikakkun Bayanai masu gamsarwa.

Happy independenceday

Nigeria@58

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.MuryarHausa24.com.ng a duk inda ku Kasance a faɗin Duniya domin samun sahihan Tarihi Daban-Daban a faɗin Duniya.


KARANTA KAJI: TARIHIN ASALIN ZAMFARAWA

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: www.MuryarHausa24.com.ng

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user