Friday 5 April 2019

KARANTA KAJI: HANYOYIN MAGANCE MATSALAR TSARO A JIHAR ZAMFARA

Tura Wannan Zuwa Ga
Tun bayan da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dare karagar mulki a cikin watan Mayu na shekara ta 2015, yan Najeriya da dama ke fatan ganin sauye-sauye a lamura masu yawa da suka ji6inci talakawa, ciki kuwa har da lamarin da ya shafi tsaro da kiyaye lafiya da dukiyar 'yan kasa, wanda yana daya daga cikin manyan abubuwan da Shugaba Buharin yayi alkawarin samarwa saboda gazawar waccan gwamnatin ta Shugaba Goodluck, kuma kasancewarsa tsohon soja wanda yasan hanyoyi maganceshi.





Marubuci: Abba Ahmad Gwammaja


A wancan lokaci, jahohin arewa maso gabas sune ta6ar6arewar tsaro da rashin zaman lafiya yafi tsamari, amma bayan zuwan Shugaba Buharin ya taka rawar gani wajen karya lagonsu.

Sai dai za'a iya cewa: "ana magani kaba, amma kai yana dada kumbura", domin kuwa lamarin kullum dada samun nakasu yake a wasu sassa na kasar. Dan kuwa yanzu haka kullum abin dada lalacewa yake a jihar Zamfara, inda 'yan bindiga dadi da masu garkuwa da mutane suke cin karensu babu babbaka, tare da kashe mutane ko kuma kar6ar kudin fansa babu gaira, babu dalili.

Duk da cewa a kwanakin baya, gwamnatin tarayya ta ayyana cewa: "ta aika da jiragen yaki masu saukar ungulu, tare da kaddamar da wata rundunar sojoji wadda aka yiwa lakabi da 'operation sharar daji', inda aka umarcesu da kada su saurarawa kowane mai laifi, har sai sunga bayansa".
Amma sai gashi a 'yan kwanakin nan lamarin na neman komawa gidan jiya, wanda hakan har ya jawo jama'ar wasu garuruwan na gujewa gidajensu.

A zahirin gaskiya, hakki ne akan gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar ta Zamfara, kan suyi duk mai yiwuwa wajen ganin cewa an samu dawwamammen zaman lafiya a jihar, kamar yadda a kwanakin baya gwamnan jihar Kaduna ya taka rawar gani wajen samar da zaman lafiya a jiharsa.

In har a baya zamu zargi gwamnatin Shugaba Goodluck wajen gazawa akan samar da zaman lafiya a shiyar Arewa maso gabas, to a yanzu ma zamu iya zargin gwamnatin Shugaba Buhari wajen gazawa, dan kuwa duk shugaba sunansa shugaba.

Idan har akwai sojojin da zasu ragargaji 'yan shi'a don sun tare hanya, sannan su samar da zaman lafiya a yankin Kudu lokacin rikicin Biafara, ko kuma su harbe 6arawon akwatin za6e, to banga dalilin yin lakwa-lakwa da rayuwar wadancan al'umma ba. Kamata yayi gwamnati tayi duk mai yiwuwa wajen ganin cewa ta binciko wadanda suke da hannu wajen wannan balahira, domin a hukunta mutum kowaye shi, dan kuwa ko a kwanakin baya an rawaito cewa akwai sa hannun wani mai sarautar gargajiya, amma shiru kake ji babu abinda ya biyo baya.

Babu wani uzuri ga hukuma akan tabbatar da tsaro ga dukiya da lafiyar 'yan kasa, dan kuwa dalilin da yasa talaka ya hau layin za6e yasha rana ya za6esu kenan, wajibi ne a dauki mataki, idan ba haka ba kuwa kamar yadda waccan gwamnatin aka nemi yi mata tawaye da zanga-zanga, ita ma wannan haka za'a yi mata, domin talaka yafi kaunar zaman lafiya fiye da komai.

Na tabbatar da cewar da ace lamarin ya shafi wani yanki na matsugunin gwamnati, ko kuma daga ko ina zai iya sahafar masu mulkin kai tsaye, to da tuni an dauki matakin da ya kamata, kamar yadda akayi lokacin da "Ebola" ta shigo Najeriya, inda har hutun makarantu aka bayar dan a shawo kan lamarin, saboda babu ruwanta da talaka ko mai mulki, kuma cikin kankanin lokaci aka ga bayanta.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode





TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user