Friday 5 April 2019

KARANTA KAJI: ME KE FARUWA A JIHAR ZAMFARA?

Tura Wannan Zuwa
Biyo bayan dogon nazari da binciken da nayi game da matsalar tsaro a jihar Zamfara, tabbas akwai wasu boyayyun ababen dake kara rura Wutar matsalar tsaro a jihar Zamfara.


Matsalar Tsaron Jihar Zamfara Matsala ta ce - Haji Shehu



Marubuci: Haji Shehu

Duba ga yadda gwamnatin jihar Zamfara, Sarakunan gargajiya, jam'iyun siyasa da sauran masu fada aji na jihar sukayi burus da hau hawan kisan gillar da akeyiwa Talakawan su, za mu iya cewar akwai lauje cikin nadi.

Tun lokacin da jihar Zamfara ta tsunduma cikin halin matsalar tsaro, har izuwa yau babu wani tanadi na musamman da gwamnatin jihar tayi domin shawo kan wanga matsala, wasu lokutan ma gwamnatin jihar bata kulawa da me ke faruwa face harkokin ta na takaddamar waye zai gaji kujerar mulkin jihar.

Idan muka duba bangaren Sarakunan gargajiya kuma, akwai Sarakunan gargajiya wadanda suke Shugabantar bangarori daban-daban a jihar, kuma Akasarin kashe-kashen jama'ar da yan ta'adda sukeyi jama'ar da suke mulka ake kashe wa a kowacce rana, har yau banga Sarakunan gargajiya na jihar Zamfara sun fito domin kai koken su zuwa fadar shugaban kasa ba, kamar yadda takwarorin su na jihar Borno sukayi.

Jam'iyun adawa a jihar Zamfara sun nade kafa sun rufe idanuwan su, sun kuma kauda fuska akan abubuwan dake faruwa akan Talakawan jihar su, har yau babu wata jam'iyar adawa da ta fito ta yaki gwamnatin jihar Zamfara akan matsalar tsaron jihar, kai kace babu wata jam'iyar adawa a jihar Zamfara.

Dattawa, masu fada aji na jihar Zamfara kowa ya kauda idon sa akan abunda ke faruwa a jihar, babu mutum daya da yake fitowa ya kalubalanci gwamnatin jiha ko ta tarayya akan matsalar tsaron jihar, a kowacce rana sai an kashe, sai anyi garkuwa, amma babu wani mutum guda da yake kalubalantar gwamnatotin jiha da ta tarayya akan wannan ta'asa.

Idan har babu lauje a cikin nadin, ya kamata ace Dattawa, masu fada aji, Sarakunan gargajiya, da jam'iyun adawa su izawa gwamnatin jiha da ta tarayya wuta akan wanga matsala dake lankome rayukan jama'ar su a kowacce rana.

Duk da cewar a dayan gafen nazari da binciken da nayi, akwai alamar tambayar dake kokarin tabbatar da cewar akwai yiwuwar samun wasu Manyan mutane dake amfana da matsalar tsaron jihar, a duk lokacin da jihar ta zauna lafiya, Kofar samun su zata rufe. Hakan ya tabbatar min da cewar shirun da manyan jihar Zamfara sukayi akan matsalar tsaron jihar yana da nasaba da wasu Manyan na amfanuwa da matsalar tsaron, wasu kuma na tsoron yin magana don gudun salwantar da rayuwar su.


Idan bamu manta ba, gwamnatin tarayya ta sha tura rundana ta musamman jihar Zamfara, a lokacin da rudanar ta fara aiki takan cimma nasarori kafun daga baya ka rasa inda rundunar ta bace.

Abun tambaya anan shine, shin ko masu amfana da matsalar tsaron sukan kulla harkalla ne da rundunonin da ake turawa?

A lokutan da matsalar tsaron jihar Zamfara ya fara, kafafen watsa labaru basu da labarin da ya wuce labarin jihar Zamfara, a wancan lokaci hankalin duniya ya koma kan jihar Zamfara, hakan yasa hankalin gwamnatin tarayya ya tashi, amma daga baya sai kafafen watsa labaru suka daina kawo rahoto akan jihar Zamfara.

Ko suma an saye sune domin su daina nunawa duniya irin ta'asar da ke faruwa a jihar Zamfara?

Muddin kowa zai nade hannu ya zurawa matsalar tsaron jihar Zamfara ido, to ko shakka babu watan wata rana zamu wayi gari cikin ganimar yaki.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode






TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user