Sunday 9 June 2019

KARANTA KAJI: A DALILIN AURE TA ZAMA KIRISTA YANZU A DALILIN AURE TA SAKE ZAMA MUSULMA

Tura Wannan Zuwa Ga
Wannan dai auren ya zo da sabon salo ta yadda shafukan sada zumunta suke yin Sharhi sosai akan daurin auren nasu .


Amarya da AngoGa dai sharhin mutanen da yafi daukar hankulan kafafen sadarwa..


Jama'a, ko za mu iya tuna tsohon Gwamnan Jihar Taraba, Danbaba Suntai? Shi ne a lokacin da yake Gwamna, ya sayi jirgin sama, yana kan tukawa da kansa, Allah Ya kaddara masa hadari.


Amarya da Ango


A sanadiyyar hadarin nan ya mutu bayan ya sha jinya a asibitocin gida da waje.


Sharhin Bashir Yahuza Malumfashi


Marigayin ya mutu ya bar matarsa daya, wacce kuma ita da 'ya'yanta suka gaji dukiyarsa da ya bari.

A yanzu, kamar yadda labari ya ishe ni, wannan mata ta marigayi ta samu sabon bazawari, sun shirya aure na kasaita, har da daukar hotunan da a zamance ake kira "Hotunan Kafin Aure" (Pre-Wedding Pictures).


Ni a wurina, ba laifi ne matar ta yi ba, don ta sake aure bayan mutuwar mijinta. Ni a ganina, wannan darasi ne ga al'umma.


Wane darasi ne nake son jawo hankali gare shi? DUK ABIN DA KAKE YI, KA TUNA AKWAI MUTUWA. DUKIYAR DUK DA KA TARA, KANA TAFIYA, MATARKA DA ITA ZA TA SAKE DORA SABUWAR RAYUWA.


A GIDANKA ZA TA TARE DA SABON MIJINTA, LOKACIN KAI KUMA KANA CAN LAHIRA KANA AMSA TAMBAYOYIN  YADDA KA TARA DUKIYAR?


YA ALLAH KA SA MU GAMA DA DUNIYA LAFIYA.


Shima dai Rabi'u Biyora daya ne daga cikin fitattun marubuta a arewacin Nigeria a kafafen sada zumunta  (Social Network) .


Mrs. Hauwa matar tsohon gwamna Danbaba Suntai wacce yar asalin jihar Borno ce, ta koma addinin kirista sakamakon zaman auren daya hadata da Suntai a wancan lokacin.


Amarya da Ango
Sharhin Rabi'u Biyora


Bayan rasuwar mujinta tsohon Gwamna Suntai sai soyayya ta hada ta da Alhaji Sa'ad Malami wanda yake dan'uwa ne ga matar tsohon shugaba Yar'adua, wannan soyayya tasu ta kai Hauwa ga shiga addinin musulunci, a babban Masallacin Abuja ranar asabar ta karbi musulunci sannan suke shirye shiryen Daura aure da mujinta wanda ta girmeshi....


Alhaji Sa'ad yayi nasarar dawo da Hauwa zuwa Addinin musulunci, wannan babbar karuwa ce muka samu, Allah ya albarkaci auren nasu Ameen.Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user