Wednesday 12 June 2019

KARANTA KA SHA MAMAKI: HIKAYAR BUTULCI HIKIYA MAFI NISHADANTARWA

Tura Wannan Zuwa Ga
Wata rana wani dan sarki yana wasa a kofar fada sai wani bakin maciji ya lallabo ya cije shi, yaro ya yi kara ya fadi yana shure- shure kafin ka ce me har ya ce ga garinku.


Hikayar ButulciHankalin sarki da fadawa ya tashi,
sarki ya baza dogarai su nemo macijin
nan su kashe shi, maciji kuwa ya shige cikin gari yana ta gudu fadawa na binsa
har ya gaji sun kusa kama shi, sai ya zo ya tadda wani masaki yana saka ya ce
masa "ka ji kaina ka ceci rayuwata ka boye ni kar fadawan sarki su kashe ni".


Sai masaki ya ce "ni ba ni da wajen boye ka", sai maciji ya ce "ka bude bakin ka in
shiga idan sun wuce sai in fito na rantse maka ba
zan cutar da kai ba".


Sai masaki ya bude bakinsa maciji ya shige, bayan fadawa sun wuce sai masaki ya ce "to fito sun wuce", maciji ya ce "in fito? ina! ai ni na samu wajen zama, na huta da yawo
sai in yi ta cin hanjinka da hantarka su ne abincina".

Masaki yai juyin duniya
amma maciji ya ki fita, ya yi ta yawo ya na kuka, kwana da kwanaki duk ya rame ya kanjame.

Rannan ya na yawo sai ya gamu
da tsuntsu sai tsuntsu ya ce "kai
kuwa kukan me ka ke yi?" sai masaki ya kwashe labari kaf ya fada masa sai ya
ce "ba don halin 'yan Adam na butulci ba, da na taimake ka", sai masaki ya ce
haba! Ya za ka taimake ni, in yi maka butulci ai ba na yi haka ba" sai ya ce "to ka je ka kwanta a rana ka daga bakinka kamar ka mutu", sai masaki ya ce "to" ya je ya kwanta ya daga bakinsa.

Can Maciji ya ji zafi ya yi yawa sai ya fiddo kanshi ya sha iska sai tsuntsu ya yi farat ya jawo shi suka kashe shi.


Masaki ya ce "na gode" sai tsuntsu ya ce "to yanzu ka samu kaji biyu ka dafa ka ci shi ne maganin raunin da yai maka a ciki".


Ko da masaki yaji haka sai yayi
farat ya kama tsuntsu ya ce "dama ina kiwon kaza sai in gama da kai in yanka".


Tsuntsu ya yi ta kuka amma masaki ya tafi dashi gida ya kife da kwando ya na can ya na wasa wuka sai matarsa ta zo wurin tsuntsu ta ce "ya aka yi mijina ya kama ka?"


Tsuntsu ya kwashe labarin yadda suka
yi da masaki ya gaya mata sai ta ce "gaskiya ya yi maka butulci bai kyauta ba amma kar ka damu bari in bude ka ka tafi in yazo sai in ce bansan yadda aka yi ka gudu ba".


Sai tsunstu ya ce "da kin kyauta kuwa".


Sai ta buɗe kwando tsuntsu
kuwa kawai sai ya kwakwule idonta daya ya tashi abinsa ta yi ta ihu tana kuka.Wanne darasi ka ɗauka a cikin wannan taƙaitacciyar Hikayar?

Waye yafi Butulci a cikin su??


Allah yasa mu dace Amin.


KARANTA LABARIN HIKAYA MAFI TSAYI A DUNIYAShafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

MungodeTURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user