Saturday 20 July 2019

KARANTA MU KOYI RUBUTUN HAUSA DA KA'IDOJIN SA KASHI NA GOMA SHA BIYU

Tura Wannan Zuwa
Domin taimaka wa dalibai masu nazarin harshen Hausa, da kuma masu so rubutunsu ya yi ma'ana da saukin karatu, ba tare da mai karatu ya canja wa rubutun nasu ma'ana ba.

Nazari aikin Mai Hankali da Tinani


Darasi Na 12

WASU KALMOMI MASU RIKITARWA

5. dashi da da shi

Kalmar farko (dashi), suna ne na wata itaciya, ko wani karo-karon kuɗi da akan yi ana karɓa-karɓar ɗauka. Don haka a haɗe ake rubuta ta. Misali:

ana yin magani da iccen dashi

jiya Kande ta ɗauki dashi

Kalma ta biyu kuwa (da shi), kalmar aɗafi ce da, da kuma wakilin suna shi, don haka a rabe ake rubuta su. Misali:

kowa ya ja da shi ya faɗi

darasin nan a kula da shi



6. gata da ga ta

Kalma ta farko (gata), suna ne da ke nufin samun kulawa ta musamman ga wani, ko sunan kwanaki uku masu zuwa. Don haka a haɗe ake rubuta ta. Misali:

yaron ya sami gata mayyawa

Gata za a yi taron Gizago

Kalma ta biyu kuwa (ga ta), ta ƙunshi kalmar nuni ga, da kuma sarrafaffen wakilin suna ta da ke nufin ita. Don haka a rabe ake rubuta su. Misali:

ga ta nan tafe

kowa ya zo ga ta

Za mu ci gaba  a sati mai zuwa Ranar Juma'a Insha Allah.

Wannan wani sabon darasi ne da
Waziri Aku tare da haɗin gwiwar Shafin Muryar Hausa24 su ka ɗauki nauyin kawowa 'yan uwa ɗalibai masu yin nazarin harshen Hausa da kuma masu son koyon ƙa'idojin rubutun harshen Hausa domin rubutunsu ya yi ma'ana da sauƙin karatu, ba tare da mai karatu ya canja wa rubutun nasu ma'ana ba.

A lura da haƙƙin mallaka wajen kwafin ɗin rubutu, darasin zai rika zuwa muku duk ranar Juma'a, daidai wannan lokaci, tare da taimakon Malam Nasir G. Ahmad .


KARANTA WANNANMU KOYI RUBUTUN HAUSA DA KA'IDOJINSA KASHI NA GOMA SHA DAYA


Za mu ci gaba  a sati mai zuwa Ranar Juma'a Insha Allah, Idan akwai mai tambaya a kan wannan darasi na yau sai a tura  tambaya zuwa
muryarhausa24@gmail.com

Mungode .


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode









TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user