Friday 12 July 2019

KARANTA KA JI : MU KOYI RUBUTUN HAUSA DA KA'IDOJINSA KASHI NA GOMA SHA DAYA

Tura Wannan Zuwa Ga
Domin taimaka wa dalibai masu nazarin harshen Hausa, da kuma masu so rubutunsu ya yi ma'ana da saukin karatu, ba tare da mai karatu ya canja wa rubutun nasu ma'ana ba.

Koyan Ka'idojin Rubutu


Darasi Na 11


WASU KALMOMI MASU RIKITARWA

3. akan da a kan
Kalma ta farko (akan), lamirin lokaci ne ko zagin aikatau na lokacin sabawa da muka yi maganarsa a baya. Don haka a haɗe ake rubuta ta.

Misali:

sai an ajiye akan ɗauka
da ruwan ciki akan jawo na rijiya

Kalma ta biyu kuwa (a kan), bayanau ne na wuri da ke nufin a bisa, wanda kuma ke ƙunshe da kalmomi biyu: a da kan. Don haka a rabe ake rubuta su.

Misali:

ya zauna a kan tabarma

sun yi hatsari a kan hanya.

4. daka da da ka Kalma ta farko (daka), suna ne da ke nuna aikin yin daka. Kalma ɗaya ce ke nan, don haka a haɗe ake rubuta ta.

Misali:

Atine ce ke daka

Kowa ya daka rawar wani….

Kalma ta biyu kuwa (da ka), kalmomi biyu ne: da wadda ke matsayin aɗafi, wato mahaɗi, da kuma ka wadda ke nufin kai.

Kasancewarsu kalmomi biyu ya sa ba za a haɗe su ba, a rabe ake rubuta su. Misali:

ya yi karatun da ka

ta tuntsuro ƙasa da ka.

Za mu ci gaba  a sati mai zuwa Ranar Juma'a Insha Allah.

Wannan wani sabon darasi ne da
Waziri Aku tare da haɗin gwiwar Shafin Muryar Hausa24 su ka ɗauki nauyin kawowa 'yan uwa ɗalibai masu yin nazarin harshen Hausa da kuma masu son koyon ƙa'idojin rubutun harshenl Hausa domin rubutunsu ya yi ma'ana da sauƙin karatu, ba tare da mai karatu ya canja wa rubutun nasu ma'ana ba.

A lura da haƙƙin mallaka wajen kwafin ɗin rubutu, darasin zai rika zuwa muku duk ranar Juma'a, daidai wannan lokaci, tare da taimakon Malam Nasir G. Ahmad .


KARANTA WANNANMU KOYI RUBUTUN HAUSA DA KA'IDOJINSA KASHI NA GOMA


Za mu ci gaba  a sati mai zuwa Ranar Juma'a Insha Allah, Idan akwai mai tambaya a kan wannan darasi na yau sai a tura  tambaya zuwa
muryarhausa24@gmail.com

Mungode .


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user