Saturday 10 August 2019

Karanta Addu'ar Bude Sallah Bayan An yi Kabbarar Harama

Tura Wannan Zuwa
Bayan An yi Kabbarar Harama.

اَللَّهُـمَّ باعِـدْ بَيـنِي وَبَيْنَ خَطـايايَ كَما باعَدْتَ بَيْنَ المَشْرِقِ وَالمَغْرِبْ ، اَللَّهُـمَّ نَقِّنِـي مِنْ خَطايايَ كَمـا يُـنَقَّى الثَّـوْبُ الأَبْيَضُ مِنَ الدَّنَسْ ، اَللَّهُـمَّ اغْسِلْنِـي مِنْ خَطَايَـايَ بِالثَّلـجِ وَالمـاءِ وَالْبَرَدْ .

 Allahumma ba'id baynee wabayna khatayaya kama ba'adta baynal-mashriki walmaghrib, allahumma nakkinee min khatayaya kama yunakkath-thawbul-abyadu minad-danas, allahummagh-silnee min khatayaya biththalji walma'i walbarad.

Addu'ar Bude Sallah


Ya Allah! Ka nisanta tsakanina da laifuffukana kamar yadda Ka nisanta tsakanin gabas da yamma; Ya Allah! Ka tsarkake ni daga laifuffukana kamar yadda ake tsarkake farar tufa daga dauda, Ya Allah! Ka wanke ni daga laifuffukana da kankara da ruwa da raba.


سُبْـحانَكَ اللّهُـمَّ وَبِحَمْـدِكَ وَتَبارَكَ اسْمُـكَ وَتَعَـالَى جَـدُّكَ وَلا إِلهَ غَيْرُكَ.
Subhanakal-lahumma wabihamdika watabarakas-muka wata'ala jadduka wala ilaha ghayruk.

Tsarki ya tabbata gareKa, Ya Allah, tare da yabo gareka; Albarkatun sunanka sun yawaita; mulkinka da girmanka sun daukaka; babu abin bautawa da gaskiya ba Kai ba.

وَجَّهـْتُ وَجْهِـيَ لِلَّذِي فَطَرَ السَّمـَوَاتِ وَالأَرْضَ حَنِـيفَاً وَمَـا أَنَا مِنَ المشْرِكِينَ، إِنَّ صَلاَتِـي، وَنُسُكِي، وَمَحْـيَايَ ، وَمَمَاتِـي ِللهِ رَبِّ العالَمِينَ، لاَ شَرِيـكَ لَهُ وَبِذَلِكَ أُمِرْتُ وَأَنَا مِنَ الْمُسْلِـمِينَ. اَللَّهُـمَّ أَنْتَ المَلِكُ لاَ إِلهَ إِلاَّ أَنْتَ ،أَنْتَ رَبِّـي وَأَنَـا عَبْـدُكَ ، ظَلَمْـتُ نَفْسِـي وَاعْـتَرَفْتُ بِذَنْبِـي فَاغْفِرْ لِي ذُنُوبِي جَمِيعاً إِنَّـهُ لاَ يَغْـفِرُ الذُّنـُوبَ إلاّ أَنْتَ .وَاهْدِنـِي لأَحْسَنِ الأَخْلاقِ لاَ يَهْـدِي لأَحْسَـنِهَا إِلاَّ أَنْـتَ، وَاصْـرِفْ عَـنِّي سَيِّئَهَـا، لاَ يَصْرِفُ عَـنِْي سَيِّئَهَـا إِلاَّ أَنْـتَ، لَبَّـيْكَ وَسَعْـدَيْكَ، وَالْخَـيْرُ كُلُّـهُ بِيَـدَيْـكَ، وَالشَّرُّ لَيْـسَ إِلَـيْكَ، أَنَا بِكَ وَإِلَيْـكَ، تَبَـارَكْتَ وَتَعَـالَيتَ أَسْتَغْـفِرُكَ وَأَتُوبُ إِلَـيْكَ.

Wajjahtu wajhiya lillazee fataras-samawati wal-arda haneefan wama ana minal-mushrikeen, inna salatee wanusukee wamahyaya wamamatee lillahi rabbil-'alameen, la shareeka lahu wabithalika umirtu wa-ana minal-muslimeen. Allahumma antal-maliku la ilaha illa ant. anta rabbee wa-ana 'abduk, zalamtu nafsee wa'taraftu bizanbee faghfir lee thunoobee jamee'an innahu la yaghfiruz-zunooba illa ant.wahdinee li-ahsanil-akhlaki la yahdee li-ahsaniha illa ant, wasrif 'annee sayyi-aha la yasrifu 'annee sayyi-aha illa ant, labbayka wasa'dayk,walkhayru kulluhu biyadayk, washsharru laysa ilayk, ana bika wa-ilayk, tabarakta wata'alayt, astaghfiruka wa-atoobu ilayka.

Na juya fuskata ga wanda ya kagi halittar sammai da kassai, ina mai karkata ga addini na gaskiya, kuma ni ba na cikin mushrikai. Lallai sallata da ayyukan ibadata da rayuwata da mutuwata na Allah ne, Ubangijin talikai; babu abokin tarayya a gare Shi, kuma da wannan aka umarce ni, kuma ni ina daga Cikin Musulmi. Ya Allah! Kai ne Sarki, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai; kai ne Ubangijina, kuma ni bawanka ne, na zalunci kaina, kuma na tabbata da zunubina; Ka gafarta mini zunubaina dukkanninsu, ba wanda yake gafarta zunubai sai Kai; Ka gusar da miyagunsu daga gare ni, babu wanda zai gusar da miyagunsu daga gareni sai Kai. Amsa maka, da biyayya gare ka bayan biyayya; kuma arziki naka ne, kuma alherin dukkaninsa yana hannunka, sharri kuma ba a danganta shi gare Ka. Ni kuma dacewata tana gare Ka, kuma gare Ka nake fakewa. Alherinka ya yawaita, kuma Ka daukaka. Ina neman gafarrka, kuma ina tuba gare Ka.

اللّهُـمَّ رَبَّ جِـبْرَائِيلَ، وَمِيكَـائِيلَ، وَإِسْـرَافِيلَ، فَاطِرَ السَّمَوَاتِ وَالأَرْضِ، عَالِمَ الغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ أَنْتَ تَحْكُمُ بَيْـنَ عِبَادِكَ فِيمَا كَانُوا فيهِ يَخْتَلِفُونَ. اهْدِنِي لِمَا اخْتُلِفَ فِيهِ مِنَ الْحَقِّ  بِإِذْنِكَ، إِنَّـكَ تَهْـدِي مَنْ تَشَـاءُ إِلَى صِرَاطٍ مُسْتَقَيمٍ.

Allahumma rabba jibra-eel, wameeka-eel, wa-israfeel fatiras-samawati walard, 'alimal-ghaybi washshahadah, anta tahkumu bayna 'ibadika feema kanoo feehi yakhtalifoon. ihdinee limakh-tulifa feehi minal-haqqi bi-ithnik, innaka tahdee man tasha-u ila siratin mustaqeem.

Ya Allah! Ya Ubangijin Jibrilu da Mika'ilu da Israfilu! Mai kagen halittar sammai da kassai, masanin fake da sarari! Kai ne Kake hukunci tsakanin bayinka Cikin abin da suka kasance suna sassabawa a cikinsa (na gaskiya). Ka shirye ni zuwa ga abin da aka sassaba a cikinsa na gaskiya da Nufinka; hakika Kai ne mai shiryar da wanda Ka so (shiriyarsa) zuwa ga tafarki madaidaici.

اللهُ أَكْبَرُ كَبِيرًا، اَللهُ أَكْبَـرُ كَبِيرًا، اللهُ أَكْبَـرُ كَبِيرًا، وَالْحَمْدُ للهِ كَثيرًا، وَالْحَمْدُ للهِ كَثِيرًا، وَالْحَمْدُ للهِ كَثِيرًا، وَسُبْـحانَ اللهِ بكْـرَةً وَأَصِيلاً. (ثَلاَثاً)
أَعُـوذُ بِاللهِ مِنَ الشَّـيْطَانِ مِنْ نَفْخِـهِ وَنَفْـثِهِ وَهَمْزِه .

Allahu akbaru kabeera, Allahu akbaru kabeera, Allahu akbaru kabeera, walhamdu lillahi katheera, walhamdu lillahi katheera, walhamdu lillahi katheera, wasubhanal-lahi bukratan wa-aseela. (3)

A'uthu billahi minash-shaytani min nafkhihi wanafthihi wahamzih.

Ina girmama Allah girmamawa, ina girmama Allah girmamawa, ina girmama Allah girmammawa. Kuma yabo ya tabbata ga Allah, a safiya da yammaci (sau uku). Ina neman tsari da Allah daga shaidan, daga hurawarsa, da tofinsa da kuma zungure-zungurensa.

Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance idan ya tashi Cikin dare zai yi sallar dare (tahajjudi) yana cewa;

َاللّهُمَّ لَكَ الْحَمْدُ أَنْتَ  نُورُ السَّمَـوَاتِ وَالأَرْضِ وَمَنْ فِيـهِنَّ، وَلَكَ الْحَمْدُ أَنْتَ قَـيِّمُ السَّـمَوَاتِ وَالأَرْضِ  وَمَنْ فيـهِن، [وَلَكَ الْحَمْدُ أَنْتَ رَبُّ السَّـمَوَاتِ وَالأَرْضِ  وَمَنْ فِيـهِنَّ] [وَلَكَ الْحَمْدُ لَكَ مُلْـكُ السَّـمَوَاتِ وَالأَرْضِ  وَمَنْ فِيـهِنَّ]   [وَلَكَ الْحَمْدُ أَنْتَ مَلِـكُ السَّـمَوَاتِ وَالأَرْضِ] [وَلَكَ الْحَمْدُ] [أَنْتَ الْحَقُّ وَوَعْـدُكَ الْحَـقُّ، وَقَوْلُـكَ الْحَـقُّ، وَلِقَاؤُكَ الْحَـقُّ، وَالْجَـنَّةُحَـقٌّ، وَالنّـارُ حَـقٌّ، وَالنَّبِـيُّونَ حَـقٌّ، وَمُـحَمَّدٌ  حَـقٌّ، وَالسّـاعَةُحَـقٌّ]  [اللّهُـمَّ لَكَ أَسْلَمْتُ، وَعَلَـيْكَ تَوَكَّلْـتُ، وَبِكَ آمَنْـتُ، وَإِلَـيْكَ أَنَبْـتُ ، وَبِـكَ خَاصَمْتُ، وَإِلَـيْكَ حاكَمْـتُ. فَاغْفِـرْ لِي مَـا قَدَّمْتُ ، وَمَا أَخَّـرْتُ، وَما أَسْـرَرْتُ، وَمَا أَعْلَنْتُ]  [أَنْتَ الْمُقَـدِّمُ وَأَنْتَ المُـؤَخِّرُ، لاَ إِاَـهَ إِلاَّ أَنْـتَ]  [أَنْـتَ إِلَهِي لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ.

Allahumma lakal-hamd anta noorus-samawati wal-ardi waman feehin, walakal-hamd, anta kayyimus-samawati walardi waman feehin, [walakal-hamd, anta rabbus-samawati walardi waman feehin], [walakal-hamd, laka mulkus-samawati walardi waman feehin] [walakal-hamd, anta malikus-samawati walard] [walakal-hamd] [antal-haq, wawaAAdukal-haq, wakawlukal-haq, walika-okal-haq, waljannatu haq wannaru haq, wannabiyyoona haq, wa Muhammadun  haq, wassaAAatu haq] [allahumma laka aslamt, waAAalayka tawakkalt, wabika amant, wa-ilayka anabt, wabika khasamt, wa-ilayka hakamt, faghfir lee ma kaddamt, wama akhkhart, wama asrart, wama a'lant] [antal-mukaddim, wa-antal-mu-akhkhir, la ilaha illa ant] [anta ilahee la ilaha illa anat .

ADDU'O"I MASU ALAKA:

Karanta Addu'ar tafiya Zuwa Masallaci

Karanta Addu'ar Shiga Masallaci

Karanta Addu'ar tafiya Zuwa Masallaci

Ya Allah! Dukkan yabo ya tabbata gare Ka, Kai ne hasken sammai da kassai da wanda ke cikinsu; kuma dukkan yabo ya tabbata gare Ka, Kai ne mai tsayar da sammai da kassai da wanda ke cikinsu da karfin ikonka; kuma dukkan yabo ya tabbata gare Ka, Kai ne Ubangijin sammai da kassai da wanda ke cikinsu; kuma dukkan yabo ya tabbata gare Ka, Kai ne gaskiya, kuma alkawarinka shi ne gaskiya, kuma maganarka ita ce gaskiya, kuma saduwa da Kai ita ce gaskiya, kuma aljanna gaskiya ce, wuta ma gaskiya ce, Annabawa ma gaskiya ne, (Annabi) Muhammadu ma, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, gaskiya ne, sa'ar kiyama ma gaskiya ce. Ya Allah! Gare Ka kadai na mika wuya, kuma da Kai kadai na dogara, kuma da Kai kadai na yi imani, kuma zuwa gare Ka kadai nake komawa, kuma saboda Kai ne kadai na yi jayayya, kuma gare Ka kadai na kai hukunci. Don haka Ka gafarta mini abin day a wuce da abin da zai zo da abin da na boye da abin da na bayyana, Kai ne mai gabatarwa, kuma Kai ne mai jinkirtawa, babu abin bautawa da gaskiya sai Kai. Kai ne wanda nake bautawa; babu abin bautawa da gaskiya sai Kai.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user