Thursday 22 August 2019

KARANTA ABUBUWAN DA SU KE HALATTA GA MAI YIN AZUMI

Tura Wannan Zuwa Ga
1. Hakika, Allah Madaukakin Sarki ya yi wa Musulmi sauki lokacin Azumi da daddare su sadu da iyalansu.

Lokacin shan Ruwa (Buɗa Baki)


قَالَ تَعَالَى: "أُحِلَّ لَكُمْ لَيْلَةَ الصِّيَامِ الرَّفَثُ إِلَى نَسَائِكُمْ." (سورة البقرة: 187 آية)

Ma'ana: Ubangiji Madaukakin Sarki ya ce: “An halasta gare ku a daren Azumi ku kusanci matanku.” (Suratul Bakara: aya ta 187).

An karbo daga Barra’u ya ce, yayin da Allah (S.W.T) ya wajabta Azumin Ramadan, sahabbai sun kasance ba sa saduwa da iyalansu da daddare, har sai da Allah ya saukar da wannan ayar.

2. Babu laifi mai Azumi ya wayi gari da janaba a cikin watan Ramadan.

عَنْ عَائِشَةَ وَأُمُّ سَلَمَة رَضِيَ اللهُ عَنْهُمَا: "أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يُدْرِكُهُ الْفَجَرَ وَهُوَ جُنُبٌ مِنْ أَهْلِهِ ثُمَّ يَغْتَسِلُ وَيَصُومُ." (رواه البخارى)

An karbo daga Aisha da Ummu-Salama (R.A) suka ce, Manzon Allah (S.A.W) ya kasance alfijir yana riskarsa yana mai janabar saduwa da iyalansa, sannan ya yi wanka kuma ya yi Azumi. (Bukhari ne ya rawaito).

Abu Dawud ya rawaito Hadisi daga Nana Aisha (R.A) ya ce, ta ce, Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana runguma ta lokacin da yake Azumi kuma ni ma ina Azumi. (Abu Dawud).

Idan mutum ya sumbaci matarsa ko ya rungume ta har ya fitar da maziyi to ba komai a gare shi.

Idan kuma mutum ya rungumi matarsa ko ya sumbace ta, lokacin duk suna Azumi har dayansu ya zubar da maniyi to Azumin wanda ya zubar da maniyyin ya baci kuma sai ya rama Azumi.

3. Yin Kaho: Idan mutum yana Azumi sai ya sa aka yi masa kaho, shi ma ba komai a gare shi.

عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ قَالَ: "احْتَجَمَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَهُوَ صَائِمٌ." (رواه البخارى)

An karbo daga dan Abbas (R.A) ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya yi kaho a lokacin da yake Azumi. (Bukhari ne ya rawaito).

DUBA WADANNAN:




4. Sa Kwalli: Anas dan Malik (R.A) ya kasance yana sa kwalli lokacin da yake Azumi.


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user