Sunday 11 August 2019

KARANTA HUKUNCE-HUKUNCE AZUMIN RANAR ARFA

Tura Wannan Zuwa
1-ME NE NE AZUMIN ARFA?

Azumin Arfa shine yin Azumi a ranar Tara ga Watan Zil-Hijjah ga wanda bai sami ikon zuwa aikin hajji ba,sai ya azuminci wannan yinin da neman kusanci zuwa ga Allah da raya sunnar Manzon Allah SAW.

Allah ya Amshi Ibadun Mu


Marubuci: Aminu Rabe Dauta

2- ME NE NE FALALAR AZUMIN RANAR ARFA?

Azumin ranar Arfa yana da falala mai yawa ga kadan daga ciki;

i-Manzon Allah s.a.w yana cewa;

(Yin Azumin ranar Arfa yana kankare zunuban shekarar da ta gabata da shekara mai zuwa)

ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺑﺮﻗﻢ 3805

ii-Manzon Allah s.a.w yana cewa;

(Duk wanda yayi Azumin ranar Arfa Allah ya gafarta masa zunubansa na shekara guda biyu,shekarar da ta gabata da wadda ta biyo bayanta)

ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺑﺮﻗﻢ 6335.

iii-Manzon Allah s.a.w yana cewa;

(Yin azumin ranar Arfa,ni ina fatan Allah zai kankare zunuban shekarar da ta gabata da shekarar da ta biyo bayanta...........)

ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺑ3853.

3- ME YASA AZUMIN RANAR ARFA YAKE KANKARE ZUNUBAN SHEKARA 2 AMMA AZUMIN ASHURA'A YAKE KANKARE SHEKARA DAYA?

ابن القيم رحمه الله؛

Yana cewa:

"Na farko: Saboda ranar Arfa tana cikin watan mai alfarma kafinta akwai wata mai alfarma kuma a gabanta akwai wata mai alfarma,sabanin ranar Ashura'ah".
"

"Na biyu: Azumin ranar Arfa ya shafi shari'ar wannan al'ummace kadai sabanin Azumin Ashura'ah wanda shi ya shafa wata al'umma wadda bamu ba,dan Allah sai Allah ya rubanya gafararsa akan ashura'ah".

بدائع الفوائد(4-211)

4- ME  YASA AKA KIRA RANAR ARFA DA WANNAN SUNA NA ARFA??

ابن الجوزي رحمه الله:

Yana cewa;

"Saboda Mala'ika Jibrilu ya kasance yana nunawa Annabi A.S guraran aiyukan hajji,sai yana fada masa عرفت ".

"Na biyu saboda Lokacin da Allah ya sauko da Annabi Adamu da Hawaa'ah sun gane junan sune a daidai wajan da ake tsayuwar arfa".

كشف المشكل (2-156).

Allah ne mafi sani

MUKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA FALALAR KWANAKI GOMA NA FARKON WATAN ZULHAJJI

KARANTA WARAKAR ZUKATA CIKIN BAYANIN AZUMIN ARFAH

KARANTA YADDA YA DACE KOWANNE MUSULMI YA FUSKANCI KWANAKI GOMA NA FARKON WATAN DHUL-HIJJAH 

Mu hadu a Darasi na gaba insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user