Sunday 4 August 2019

KARANTA YADDA YA DACE KOWANNE MUSULMI YA FUSKANCI KWANAKI GOMA NA FARKON WATAN DHUL-HIJJAH TARE DA TARIN FALALAR DAKE CIKIN SA

Tura Wannan Zuwa
Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah. Tsira da aminci su kara tabbata ga Manzon Allah, Sallallahu 'alaihi wa sallama, Alayensa da Sahabbansa da dukkan wanda ya biyo bayan su da kyautatawa.

Yayin Buda Baki


Marubuci: Sheikh Umar Shehu Zaria {Hafizahullah}

Daga: MASJID DARUL QUR'AN 07066002455

Bayan haka, duba da yanda kwanaki goma na farkon watan Dhul-Hijja suke da matukar muhimmanci, amma mafi yawa daga cikin mutane sun rafkana ga barin cin gajiyan su, ya sanya na ga dacewar in yi tsokaci a takaice dangane da wadannan kwanaki.

Dukkan abun da aka samu na daidai a cikin wannan Rubutu nawa daga Allah ne, abun da kuma aka samu na kuskure daga gare ni ne da Shaidan, Allah Ta'ala da ManzonSa sun barranta daga gare shi.

Da me ya kamata Musulmi ya fuskanci wannan wata da shi?

1. TUBA ZUWA GA ALLAH saboda zunubi shi ne kofa mafi girma da yake sanya Allah Ta'ala Ya azabtar da bawa.

Allah Ta'ala yana cewa: "Kuma wata musiba da take samun ku face sai sakamakon abun da hannuwanku suka sana'anta". Suratu al-Shuura aya ta 30.

Babban dalilin da zai sa mu fara wannan wata da tuba shi ne, barna da tasirin da zunubai suke yi a rayuwar mutum.

Daga ciki:

Na farko: Zunubai suna haramta ma mutum samun ilimi mai amfani. Domin shi ilimi haske ne da Allah Ta'ala Yake sanyawa a zuciyar mai shi, kuma zunubai suna kawar da wannan hasken.

Na biyu: Zunubai suna sanya talauci su hana bawa samun arziki.

Manzon Allah, Sallallahu 'alaihi wa sallama, ya ce: Lallai ana haramta bawa arziki saboda wani zunubi da ya aikata. Imamu Ahmad ya riwaito a cikin al-Musnad 5/282.

Na uku: Duhu da da mutum zai rinka ji a zucirya shi.

Abdullahi Bn Abbas, Radhiyallahu Anhu, ya ce:  "Lallai kyawawan ayyuka suna sanya ma mutum hasken fuska da hasken zuci da yalwan arziki da karfin jiki da soyayya daga bayin Allah, kamar yadda sabon Allah yake fuska zuciya ya yi duhu da duhun zuciya da raunin jiki da tawayan arziki da kiyayya daga mutane".

Na hudu: Zunubai suna sanya daraja da mutuncin mutum ya zube a wurin Allah.

Allah Ta'ala Ya na cewa: "Dukkan wanda Allah Ya wulakantar, to ba shi da wani mai girmamawa. Suratul Hajji aya ta 18

Na biyar: Idan mutum yana aikata zunubai zai wayi gari baya ganin girman zunuban, wannan kuma alama ce ta tabewa da halaka.

Na shida: Idan mutum yana aikata zunubai za a wayi gari sun lullube zuciyar shi har ta yi tsatsa ta koma bata iya daukan wa'azi da shiriya.

2. NEMAN TAIMAKON ALLAH A WADANNAN KWANAKI: Wadannan kwanaki ya dace dukkan musulmi ya dage wurin neman taimakon Allah domin ganin ya ribace su yanda ya kamata.

Allah Ta'ala Ya na cewa: "Kuma wadanda suka yi kokari ga neman yardan Mu, lallai Muna shiryar da su ga hanyoyinMu, kuma lallai Allah Tabbas Yana tare da masu kyautatawa".  Suratul 'Ankabut aya ta 69.

ME YA SA AKA FIFITA YINNAI GOMA NA FARKON WATAN DHUL-HIJJAH AKAN WASUN SU?

Mu hadu a fitowa ta 2 in sha Allahu Ta'ala

MUKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA SUNNONIN AZUMI DA LADUBBAN SA

KARANTA MANYAN FARILLAN SALLAH GUDA 14

KARANTA HANYOYI GUDA 10 DOMIN MAGANCE MATSALAR YAWAN FISHI

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode







TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user