Friday 2 August 2019

KARANTA MANYAN FARILLAN SALLAH GUDA 14

Tura Wannan Zuwa
Su farillan sallah guda goma sha huɗu ne:

1- Kabbarar harama ga dukkan mai sallah wani ba ya daukewa wani, lafazinta shi ne ALLAHU AKBAR ka da a ce ALLAHU AKABAR, yin haka kuskure ne.

Yayin Tahiyar Sallah


Mutum ya fadi watanta ba zai isar masaba in dai zai iya da Larabci, amma idan ba zai iya ba, (kamar sabon tuba) to sai ya shiga sallar da niyyarsa kawai, a wata maganar kuwa cewa akai ya shiga sallar da hausarsa.

Kamar ya ce (Allah mai girma), amma sai ya gaggauta neman sanin ilimin da zai yi sallah da shi.

2- Yin niyya ita ana yinta ne a zuciya shine mutum ya ayyana sallar da zai yi, sannan kuma yana gwamata da kabbarar harama. Kuma ba dole bane sai ya ayyana adadin raka’o’in da zai yi.

3- Yin karatun fatiha, dole ne liman ya yi mai yin sallah shi kadai ma dole ne ya yi ta.

4- Tsayawa don yin kabbarar harama da yin karatun fatiha.

5- Yin ruku’i:  Shi mafi cikarsa shine mutum ya sunkuya ta inda bayansa da wuyansa za su dai-daita, kuma ya kama guiwoyinsa da tafukan hannunsa, ana neman namiji da ya nisanta guiwoyin hannuwansa daga jikin hakarkarinsa, sannan ba a so ya sunkuyar da kansa kasa, abin nema kawai shine ya dai-daita bayansa.

6- Yin sujjada: Sifarta shine mutum ya tabbatar da goshinsa da hancinsa a kasa da guiwoyinsa da ‘yan yatsun kafafuwansa suna a kasa.

7-8- sune dagowa daga ruku’u da sujjada idan ya bar daya daga cikinsu to ya sake sallah har abada.

9- Zaman sallama gwargwadon yadda za’a sami nutsuwa, sannan a yi sallamar.

10- Yin sallamar wadda take halatta yin ayyuka ba na sallah ba ita ce mutum ya ce ASSALAMU ALAIKUM. Wanin wannan lafazi ba zai isarwa mai sallah ba. To amma shi mamu (mai bin liman) yana yin sallama a bisa damansa sannan ya yi a gabansa yana nufi da ita amsawa ga liman sannan ya yita a hagunsa idan akwai a hagun nasa don amsawa gareshi, kuma abinda yake mafi kyau a mayar da amsar sallamar sallah ita ce ASSALAMU ALAIKUM kamar yadda liman ya yi.

Haka kuma ba sharadi ba ne a ce mutum sai ya kudurce niyyar fita daga sallah da sallamarsa ba, wannan haka aka samu a bisa dayan zantattuka guda biyu, to amma shi liman akasin wannan ne, domin kuwa shi yana yin niyyar fita daga sallah da sallamarsa, sannan kuma yin da yake yi yana yinta ne a bisa mala’iku da kuma masu koyi da shi. Shi kuwa mai yin sallah shi kadai yana yinta ne a bisa mala’iku.

11- Daidaita gabbai tsakanin rukunan sallah.

12- Nutsuwa a cikin rukunan sallah, baki dayansu, a tsayuwa da ruku’u da sujjada da kuma dagowa daga garesu. Don haka bambancin dake tsakanin daidaito da kuma nutsuwa shine: shi daidaito yakan kasance ne a cikin tsayuwa, ga misali shine:

Mikuwa kyam cikin tsayuwa ita kuwa nutsuwa ita ce tabbatar da gabbai ko kafa su lokacin aiwatar da rukunai.

13- Jeranta ayyukan sallar ta hada da kabbarar harama take zuwa kafin karatun sallah shi kuma karatu kafin ruku’u, shi kuma ruku’u kafin sujjada ita kuma sujjada kafin yin sallama.

14- Shi ne bibiyar ayyukan sallah ta hanyar aiwatar da shashi akan sashi ba, tare da wara tsakaninsu ba.

MUKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA SHARUDDAN YIN SALLAH

KARANTA  ME CE CE ALWALA?

KARANTA YADDA AKE YIN SALLAH


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user