Friday 9 August 2019

KARANTA FALALAR KWANAKI GOMA NA FARKON WATAN ZULHAJJI

Tura Wannan Zuwa Ga
An karbo Hadisi Daga ibn Abbas (R.A) ya ce Annabi (SAW) ya ce: Ranar daya ga watan zulhijja ita ce ranar da Allah (swt) Ya gafarta wa Annabi Adam (A.S).

Dakin Ka'aba


1. Duk wanda ya azimci wannan rana Allah(SWT) Zai gafarta masa kowane irin zunubi tsakaninsa da Shi.

2. Ranar biyu ga Zulhijja ita ce ranar da Allah (SWT) Ya karbi Addu’ar Annabi Yunus (A.S) Ya fitar da shi daga cikin kifin da ya hadiye shi. Wanda ya azimci wannan rana yana da lada kwatankwacin wanda ya raya shekara da ibada

3. Ranar uku ga Zulhijja ita ce ranar da Allah (SWT) Ya karbi addu’ar Annabi Zakariyya (A.S) Ya ba shi haihuwa. Duk wanda ya azimci wannan rana Allah (SWT) Zai karbi adduo’in sa.

4. Ranar hudu ga Zulhijja ita ce ranar da aka haifi Annabi Isah (A.S). Duk wanda ya azimci wannan rana Allah Zai kare shi daga talauci da musibu.

5. Ranar biyar ga Zulhijja ita ce ranar da aka haifi Annabi Musa (A.S). Duk Wanda ya azimci wannan rana Allah (SWT) Zai kare shi daga munafunci ko azabar kabari.

6. Ranar shida ga Zulhijja ita ce ranar da Allah (SWT) Ya Yi budin alkhairi ga Annabi (SAW). Duk wanda ya azimci wannan rana Allah Zai dube shi da rahama, kuma ba Zai azabtar da shi ba.

7. Ranar bakwai ga Zulhijja ita ce ranar da Allah (SWT) Zai sa a rufe kofofin wuta, ba za a bude su ba har sai wadannan kwanaki goma sun wuce. Duk wanda ya azimci wannan rana Allah Zai rufe masa kofofi talatin na tsanani a rayuwar sa, a bude masa kofofi talatin na sauki.

8. Ranar takwas ga Zulhijja ita ce ranar da ake cewa, ranar tarwiyya. Duk wanda ya azimci wannan ranar, babu wanda ya san adadin sa sai Allah.

9. Ranar tara ga watan Zulhijja ita ce ranar hawan Arfa. Allah Yana gafartawa duk Alhazan da ke wurin Arfa. Wanda kuma ba ya wurin aikin Hajji, idan ya azimci wannan ranar, Allah Yana gafarta masa zunubansa na shekarar da ta gabata, da kuma shekarar da ke tafe.

10. Ranar goma ga Zulhijja ita ce ranar layya. Duk wanda Allah Ya horewa abin da zai yi layya, idan ya yanka dabbarsa, digon jini na farko da zai fara diga a kasa zai zama gafara gare shi da
iyalin sa.

An so wanda zai yi layya da wanda ba zai yi ba ya kame bakinsa sai bayan an dawo daga sallar idi, ya ci abinci ko wani abu daga cikin layyarsa. Allah Zai ba shi lada wacce ta fi Dutsen Uhud girma da nauyi.

Kuma ana so ya raba naman sa kashi uku. Kashi na farko sadaka, kashi na biyu kyauta, kashi na uku kuma domin iyali.

MUKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA YADDA YA DACE KOWANNE MUSULMI YA FUSKANCI KWANAKI GOMA NA FARKON WATAN DHUL-HIJJAH 

KARANTA FALALAR AZUMIN RAMADAN

KARANTA MA'ANAR AZUMI A CIKIN ADDININ MUSULINCI

Allah Ya Bamu Ikon Azumtar Dukkan Wadannan Ranakun, kuma Ya sada mu da falalar da Ya tanadar ga masu Ibada a wadannan ranaku Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

MungodeTURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user