Friday 16 August 2019

MU SHA DARIYA: KARANTA LABARIN WANI RIKITACCEN TSOHO DA SAURAYI

Tura Wannan Zuwa
Wani saurayi yana tafiya a hanyarsa ta zuwa rumfar mai abici, sai ya hangi wani tsoho sai sharbar kukansa yake ba kakkautawa, sai tausayin wannan tsoho yakamashi.


'Yar Auta ta cikin shirin Kannywood


Sai ya nufi wurin tsohon baba lafiya kake irin wannan kuka haka? Sai wannan tsoho yece Yaro ina da mata yar kimanin shekara(22) a gida.


kullum da safe sai ta yimin tausa’ kuma ta soya min kosai ta yimin koko ta kuma dafamin shayi mai dadi.

Sai saurayin yace to me yasa kake kuka?

Tsohon yace: Da rana kuma tayimin miyar alayyahu da tuwon shikafa mai dadi ta kuma hada mini zobo mai sanyi, ta kuma tsaftace gidan. Bayan ta gama, sai tazauna kusa dani ta kunna mana talabijan muyi kallo cikin jin dadi har yamma. Sai saurayi yace baba har yanzu baka fadamin abinda yasa kake kuka ba!.

Sai tsoho yace: da daddare kuma tayimin alkubus da romon kaza, ta kuma matse lemo ta kawo min, naci na sha cikin annashuwa Sai wannan saurayi yace to duk da wannan abu da take maka me kuma yasaka kuka baba?
Sai tsoho yace: to ai hanyar gidan na manta.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode







TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user