Monday 2 September 2019

KARANTA SABON TSARIN DUNIYA KASHI NA BIYU (2) NEW WORLD ORDER

Tura Wannan Zuwa Ga
YAKIN KWAKWALWA TA HANYAR NA'URAR SADARWA (PHONE)

Daga cikin mafi munin dokar tsarin dake yaqar al'ummar mu a yau musamman shine,  yaqin qwalqwalwa ta dalilin Na'uwar Sadarwa (Phone). Kamar yanda kowa ya sani,  a irin Duniyar da muke ciki yau kusan kowani matashi musamman wadanda suke riqe da manyan wayoyi a hannayen su zasu fi fahimtar abunda nake cewa dangane da haka.

Sabon Tsarin Duniya

MarubuciKalimullah Ahmad Hinna

Akwai wasu Applications da aka qirqiro na tallata yada fina finai na batsa kyauta ba sai mutum ya biya kudi kafin ya shiga.

Daga cikin Apllication da ya qunshi irin wadannan abubuwa kuma sjine yafi cin kasuwa,  shine mai suna "VIDMATE" Yaqi ne yar sunquru wanda suka dasa shi,  ta yanda za'a halatta wa al'ummah ZINA,  LUWADI,  MADIGO,  da ISTIMA'I (Masturbations), ta kowani hali. Wanda daman Manzon Allah ya sanar damu faruwar haka. Yazo cikin Hadisin sa:

عن أبي هريرة رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: «سيكون في آخر الزمان دجالون كذابون يأتونكم من الأحاديث ما لم تسمعوا أنتم ولا آباؤكم، فإياكم وإياهم لا يضلونكم ولا يفتنونكم» (رواه مسلم).

"Daga Abu-Hurairah (Allah ya qara masa yarda),  yace: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata gare shi,  Yace:

A ƙarshen zamani zai kasance akwai Dajjalun (Dujal na mutane),  Maqaryata, zasu zo muku da sabn abubuwa,  wadanda baku ta6a ji ba,  ba ku ba balle iyayen ku. Don haka,  ku na hore ku dasu,  kada su 6atar daku,  kuma kada ku yarda su jefa ku cikin fitina"

Burin su shine,  za'a akai matsayin da za'a daina kunyar duk wata alfasha,  daga qarshe auratayyah ya zama don sha'awa akeyin su, zaka ga baya jimawa mutum ya saki matar shi,  domin dukkan su sun gina auratayyar ne bisa sha'awa. Kallon irin wadanna abubuwa suke sabbaba hirar batsa tsakanin Samari da Yan Mata ta hanyar yin waya da musanyar hotuna tsakanin junan su.

Zaka ga mace ta dauki hoton al'aurar ta tura wa saurayin ta ya gani,  shima ya dauka ya gura mata nashi ta hanyar
chatting tsakanin saurayi da budurwa ta da anfani da kalmomin motsa sha'awa wanda basu kamata ba. Wanda haka,  har wasu daga cikin magidan ta suna aikatawa Maza da mata don biya wa kansu buqata.

Duk sabbin al'amura ne da acan baya duk ba'a san dasu ba. Shiyasa a wancan lokacin aure yake daurewa a jima ana tare har mutuwa,  amma banda yanzu,  sakamakon faruwar wadannan abubuwa ta hanyar sadarwa. Duk shiri ne daga cikin shirin "SABON TSARIN DUNIYA" ƙarashin wannar maganar tasu:

Sabon Tsarin Duniya


"The New World Order will include changes in: the family: homosexual marriages will be legalized; parents will not be allowed to raise their children (the state will;) all women will be employed by the state and not allowed to be "homemakers"; divorce will become ex- ceedingly easy and monogynous marriage will be slowly phased out"

Don haka,  muyi qoqari mu kiyaye idan har muna son al'amuran mu su gyaru. Mu daure mu han kan mu,  domjn mutuwa na nan tafe,  bamu san ranar da zamu koma ga Allah ba. Muyi fatan komawa ga Allah cikin kyautata mu'amalar mu gare shi. Mu kawar da gannen mu daga dukkan abunda Allah ya haramta.

DUBA WADANNAN:

KARANTA SABON TSARIN DUNIYA KASHI NA FARKO (1) NEW WORLD ORDER


KARANTA MANYAN SIFFOFIN 'YAN LUWADI DA RAYUWAR SU CIKIN SIRRI KASHI NA FARKO (1)

Karanta Tarihin Sheikh Muhammad Auwal Albani Zaria

Allah ya kiya she mu sharrin "ILLUMINTATI" YAHUDAWA Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user